← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 118

Sashe 32

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Rainatu da take la'be bayan window kaf komai agabanta ya faru, tin bayan shigarsu Jaddatu falon ta tintsire da dariya, tana fa'din.
“Kowa yaci tuwo dani miya yasha, wlh duk sai na tarwatsa rayuwarku na mallake Abdul Majeed ni 'daya.â€
Ta 'karashe mgnar tana dialing 'din number Abie.
Tana ta ringing bai 'daga ba, har kusan sau biyar kafin ya 'daga, bai ce mata komai ba.
Kukan kissa ta saki tana fa'din.
“Abien umminmu don girman Allah ka gaggauta aurama Ummi yaron nan sbd zasu iya rasa rayuwarsu su na son junansu sosai, ga Ummi babba tasaka su agaba, harda dukan Rahma ga ta can ya 'dauke a mota sun nufi hospital dan Allah ka ban izinin bin bayansu.â€
Ta 'karashe cikin wani irin kuka.
Abie ya miqe tsaye hankalinsa atashe ya ce “What? Wane asibitin?â€
Dai dai lokacin yaga Ja'afar da nurses an wuce da Rahma saman gadon 'daukar marasa lfy, an nufi wata 'kofa da ita.
Da'bas ya zauna ya 'kurama Ja'afar manyan fararen idanunsa masu matuqar haske da lumshewa amman lokaci 'daya sun riki'de sunyi jajir, bai iya furta komai ba banda bakinsa da yake motsawa alamar sunan Allah yake Kira.
Abie2 ne ya miqe da sauri ya kalli Ja'afar hankalinsa a tashe ya ce“Me ya sameta Ja'afar yaushe kaje gida muna nan?â€
Ja'afar ya kalli Abie 2 ba kowani 'dar ya zayyane masa abinda ya faru.
Baba Tsalha ya kalli Ja'afar takaici ya cikasa ganin irin cin amanar da yay Wa Ibtisam.
Harisu da Yahuza ma kasa masa mgna sukayi bare Abie 1.
Ja'afar ya matso kusan Baba Tsalha ya ce“Baba dan Allah ina Ibtisam take? Fatan bataji ciwo dayawa ba?â€
Ba wanda ya tankasa ko kallon arzi'ki bai ishasu ba.
Abie 1 ne ya ha'diye wani yawu me masifar 'daci bayan ya jajirce wajan tattaro dukkan nutsuwarsa,ya Kira shi.
“Ja'afar! zo zauna.â€
Zauwa ya yi ya zauna kusan Abie hankalinsa duk atashe, kallo 'daya zaka masa kasan baida wani sukuni acikin rayuwarsa.
Hannunsa ya kama ya riqe ya kafeshi da ido ya kasa mgna.
Abie 2 ya dafe kan Ja'afar ya 'kura masa idanu yana qara nazarta wasu a'amura masu girman gaske.
Kallon Baba Tsalha yay ya ce“Wannan fa ayanzu bazaku ta'ba iya fahimtarsa ba, abu 'dayane addu'a itace zamu musu ahannu suke Wallahi duk abinda yake baisan me yake ba.â€
Baba Tsalha ya ce“
Ban gane me kake nufi ba?â€
Zayyane musu komai yay. Ja'afar ya mi'ke ya isa 'kofar room 'din da aka shiga da Rahma ya tsaya ransa a'bace jin ana cewa jinnu garesu kawai dan kar a aura musu juna.

Raiyana jin Abie ya 'kyale baice komai ba, ya saka tai shiru, ta katse kiran cike da farin ciki ta nufi 'bangaransu.
Jaddatu ta share hawayen fuskarta ta ce“Hanan ta shi muje asibitin nasan wane hali Rahma take ciki.
Ya Allah ka kawo mana 'dauki cikin gaggawa.â€
Hanan ta Kira Abie taji ko Rahma nan hospital 'din da suke.
“Ehâ€
Ka 'dai ya iya cewa.
kama hannun Iman ta ce“Muje wannan masifar Allah ka kawo mana 'karshenta idan da saka hannun wasu magautan ne ya Allah ka toni asirinsu ka Hana kowaye kwanciyar hankali.â€
Ummu Adnan da Latifa suka amsa da “Ameee.â€
Rayyana aranta ta ce.
“Ba Amin ba.
Azahiri ta amsa da “Ameen muje hospital mugani wannan yaron kawai a aura masa Ummi ko ma samu kwanciyar hankali.â€
Wani mugun kallo Jaddatu ta mata ta ce.
“insha Allahu bazata auresa ba Rahma nada mijinta wlh lokaci ya yi yanzu ko Rahma na aman jini bazamu aura mata jansin da ba namuba, bayan hakan zuciyarta da wanda take so yake sonta bazamu aura masa ita ba.â€
Rayyana jin abinda Jaddatu ta ce, ta zazzaro idanunta gabanta na fa'duwa ta ce“Ayyah! Ummi bansan tanada wanda take so ba amman yana wace 'kasa?â€
Kai tsaye Jaddatu ta ce“ Morocco. â€
Wani yawu Rayyana ta ha'de tana wani irin nazari me yasa tin farko bata tsaya taji kan abu ba taje ta ha'da wannan qazamar soyayya wacce take ganin gaba 'daya lamarin kamar sam baiyi ba.
Murmushin 'boye tai tana canza shawara akan zataje wajan malam ta ce awarware lamarin sai a ha'data da wancan ya 'dauketa subar qasar ma zatafi nutsuwa Inda bata ganinta.
Su uku suka nufi asibitin.
Chapter 32 · 0% Book details