← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 118

Sashe 116

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ja'afar har iyayansa ya Kira ya gayamusu suka Kira Abie sukayi masa barka harda Tanko hakan ba qaramin kima ya qarama Ja'afar wajan Abie b dan aduniya Wanda zai nun k'aunarsa da yaransa ko Rahma da Jaddatu toh ba qaramin masoyinsa yake kallonsa ba.

Kusan kullun asibitin cike take ga abokan arziqi mazu zuwa ganin Rahma da yaranta Wanda aqalla yanzu kusan kwana goma kenan, yaran suna samun kulawa sosai Rahma Allah ya jarabceta da son yaranta matuqa ba kamar macan da tai irin idanun mahaifiyarta.

*Niger*
Misalin k'arfe d'aya na rana Ibtisam zaune ta bararaje, tana cin wake da shinkafar da akayi, tana ci tana turo baki.
Laraba ta ce.
“Wai baqin ran me kikeyi yau Ibtisam? Me aka miki? Ji yadda kike cin abincin kamar dole kodai bakya so ne?â€
Ibtisam ta qaqalo murmushin k'arfi tai ta ce.
“Kai Anna wlh ni bawani baqin rai da nakeyi kawai banajin dad'in yanayin ne.â€
Anna tai shiru kamar batasan naquda ta fara.
“Taslim ku qare cin abincin kije ki kirawo mun Dadda.â€
Taslim ta amsa da.
“Toh Anna.â€

Ibtisam ta yamutsa fuska tana ciza lips ta ce.
“Me zata miki Anna? Ni kamar ma natafi can.â€
Laraba ta ce“A'a ki zauna ai zatazo.â€
Ibtisam batace komai ba tana tura Wake da shinkafar kamar dole.
Suna gamawa Taslim ta tafi gidan Dadda kiranta.
Kamar wasa Taslim na fita naquda ta tasoma Ibtisam gadan-gadan, ai kafin su Dadda suzo Laraba ta Kira Tanko a waya yazo da mai taxi suka nufi asibiti.

Cikin hukuncin Allah suna zuwa Ibtisam bata huce 30 minutes ba Allah ya sauketa lafiya ta haifo k'aton d'anta mai Kama d Ja'afar sak har baqin ba abunda ya bari.
Wai kai karkuso kuga murna wajansu Inna Hansatu mai waina, Mal Adamu tsabar farin ciki shi ya Kira Ja'afar ya gayamasa.
Ja'afar rasa idan zai saka kansa yay dan murna lokacin da Mahmoud ya tura masa hoton yaron.
Tabbas wannan zuri'a sunyi farin cikin haihuwar Ibtisam.
Ita kanta tana mamakin dangin Ja'afar haka suke son Ja'afar.

Tin ranan Ja'afar ya fara shirin tafiya su Harisu sukace bazai barsu a motarsa zasu zo wacce aka dubata sabida yasan abanza zasuci kwana uku ahanya.

Lokacin da yazoma Abie sallama zai tafi ba qaramin alkahiri Abie ya masa ba duk wata hidima da za'ayi ta suna ya d'aukar masa nauyinta komai ya basa yaqi karb'a sabida ayanzu yannada rufin asirinsa, amman ganin Abie ya b'ata ransa dole ya amsa, yay godiya.
Ai kuw kwanansu uku ahanya kafin su iso.
Inna sai tattalin Ja'afar ake an kasa zaune an kasa tsaye.
Ibtisam na shayar da yaron taji daga tsakar gida Laraba tna fad'in.
“Ah Ja'afar zauwar yaushe?â€
Zazzaqar muryasa taji yana gaisheta ya ce.
“Yau d'azu muka shigo Anna fatan mum sameku lafiya ya masu jiki?â€
Laraba ta amsa da lafiya bismillah ka shiga tana d'akinsu.â€
Ibtisam tai saurin zarema yaron nono ta kwantar da shi tai saurin kwnciya ta rufe idnunta.
Da sallamaa ya shogo d'akin kallo d'aya yay mata ya gane baccin qarya takeyi.
Murmushi yay ya d'auki yaron ya zauna dab da ita.

Idanu ya qurama yaron sam baiga wani banbancinsa ba da yaron, komai nasane yaron ya d'auko.
Bakinsa ya manna kunnen yaron yay masa addu'a duk da yasan anyimasa, sannan yay masa huduba da sunan mahaifinsa Adam.
Kuka yaron ya tsala, yay saurin mirgino Ibtisam ya janye rigarta ya saita masa abincinsa ya kuwa kame yana tsotsa.
Ibtisam ta qyalqyale da dariya ta ce.
“Idanuna biyu fa! Mon amour sannu da zuwa ya gajiya?â€

Rungumeta yay ya ce“Hahaha nasani Mon cherie, sannunki nagode sosai fa kinyi qoqari haifomin gwarzon namiji Allah yasa bad'i warhaka ki qaromin twins... â€
Dukan wasa ta kai masa tana kwab'e fuska ta ce“A'a gaskiya...â€

Masha Allah ranan suna anyi suna mai qayatarwa, suna yayi armashi Ja'afar da iyayansa sunyi komai na bajinta anci ansha, kowa na son barka yaro yaci sunan mahaifin Ja'afar Adam, ana kiransa da Rafael.
Ja'afar satinsa d'aya ya koma tchad wajan aikinsa Inda ya tafi yabar Ibtisam da iyayansa da 'yan uwansa da kewarsa.
Haka Ibtisam taci gaba da wankan ruwan zafi tana samun kulawa sosai ita da yaronta Rafael.

Acan kuwa Chad.
Rahma nada sati biyu da haihuwa akayi suna, an yanka raguna anyi abinci an raba sadaka tinda Rahma da Yara na asibuti anabasu kulawa.
Sai da suka kwashe wata biyu a hospital ana kulawa da yaranta wandan ayanzu sunyi mulmul sunyi wani irin qiba kamar ba bakwaini ba amman doctor ya ce baza'a sallamesu ba sai yaran sun cika wata uku sunga ba wata matsala.

Rayyana cikin wata hud'u da aure tayi wani irin kyau sabida wani irin so Nafi'u yake mata, sabida yadda ta kwantar da hankalinta tana binsa sau da k'afa, tana bin matansa a kullun sai ta shiga b'angaransu sun gaisa haka tana son yaransa hakan ba k'aramata kima yay wajansa ba.
Yau ita ce me girki tin k'arfe uku ta shiga kitchen ta fara shirya masa dadd'an abinci.
Misalin k'arfe 9 zaune take a falonta Wanda yasha turaren wuta sai qamshi yake, taci kwalliya tsaf abinta, sai yamutsa fuska take sabida mugun tashin zuciyar da ya sakata gaba tin yamma dakyar ta kammala girkin da yamma.
Kanta taji ya Sara mata ta dafe tana fad'in.
“Washhhh! Anya ba ciki gareni ba?â€
Ta tambayi kanta tana miqewa tsaye jin qaran buga qofar falonta.
Tana bud'ewa suka had'a idanu da Waheeda, wani irin tsalle tai ta dire gefe ta ce.
“A'uzubillahi minan shed'anin rajin bismillahi rahamanir rahim. Dan ubanki fitarmin agidana.â€
Waheeda ta zube qasa tana riqe k'afafun Rayyana tana fashewa da kuka ta ce.
“Don Allah ki yafeni wlh naga jarabawar ko nace miki naga sakayya bakiga yadda nakoma ba wlh alhakinku ne na qara nadamane Ajiya labarin irin hukincin da Allah yayima Malam yanzu haka yana yawo tsirara kasuwa² yana fad'in abubuwan da shuka arayuwarsa don Allah ki yafeni bazan sake ba na tuba wlh kowa guduna yake dan Allah ku yafemin...â€

Rayyana ta ingijeta da k'arfinta tace.
“Bani bake karki sake kallon titin gidana ma, kije na yafe miki amman babu alaqa ko ta gaisuwa tsakanina dake.â€
Rayyana ta qarasa mgnar tana turata ta janyo qofarta ta murza key taji zuciyarta na tashi ta nufi toilet aguje ta fara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta.

Awahalce ta fito tana maida numfashi taji ana knocking.
Awahalce ta isa ta bud'e.
Ganinsa ta afka jikinsa tana sauke numfashi.
Alhaji Nafi'u ya tarairayota jikinsa yana fad'in.
“Subahanallahi Habibiya bakida lafiya ne?â€
Kai ta d'aga masa tana narkewa ajikinsa.
Alhaji Nafi'u duk ya rud'e sai tattab'ata yake ya ce.
“Muje ki saka hijab muje hospital.
Rayyana bata musaba tafison ta tabbatar da zarginta.
Aikuwa suna zuwa asibiti gwajin farko Rayyana na d'auke da cikin sati hud'u.
Wai karkaso kuga farin ciki wajan alhaji Nafi'u tamkar yau za'a fara masa haihuwa, kaf iyalansa ba wanda baiji ba wannan cikin, hajiya Sha'awanatu har mamaki take duk da tasansa mutum mai son 'ya'ya sosai.
Wannan dare sun rayasa cike da wata irin soyayya ko motsi tai zai tambayeta me takeso, Rayyana banda godiyar Allah ba abinda takeyi, dan ita kanta tazan ta samu mijin da kowace macs zataso mallakarsa.

*Gabon*
Aishatu zaune a falo tana shirya Farook yaro d'an kusan kimanin wata 4 yayi wata irin qiba me burgewa fari Tass da shi masha Allah.
Sai yakushin Aishatu yake yana dariya, tsantsar kamarsa ta sake bayyana da Ma'aruf.
Kumatunsa taja tana dariya ta ce.
“Idan ka ciremun idanu naga wa zai maka wasa ja'irin d'ana kawai...â€

Shi dai dariya yake ya fara qoqarin sanya hannunsa cikin rigarta.
“Uwani! So don Allah kamamun yaron nan naje na shirya mutafi kasuwar nan.â€
Ta k'arashe magana tana sanya masa takalmi.
Uwani ta iso tana sanya hannu zata d'aukesa ya qamqame Aishatu ya sanya kuka.
“Ai kam kin sansa da naci bazai jeba je abinki Dadynsa zai fito yanzu ne.â€
Ta k'arashe mgnar tana janye rigarta ta fara shayar da shi.
Uwani ta tattare kayan da aka ciremasa ta gyara wajan ta tafi.

Ma'aruf ya fito cikin shirnsa yayi kyau sosai ya zauna kusan Aishatu yana sumbatar wuyanta, ya ce.
“Eh lallai zaku hau taxi kuwa tafiyata zanyi idan kin biya D'an nan naki komai bazakiyi ba!â€
Ya fad'a yana Jan hancin Farook, ya saki Maman yana b'angala masa dariya.
“Yauwa toh riqesa ban 5 minutes na shirya.â€
Ma'aruf kallonta yake cike da tsantsar k'aunarta ya riqe fuskarta da tafukan hannunsa yana fad'in.
“Haqiqa da na rasa amatsayin matata nayi babbar asara wlh samun irinki aduniyar nan ta yanzu akwai wahala, banida bakin da zan miki godiya sai da na miki fatan gamawa da duniya lafiya, ubangiji ya bamu zuri'a dayyaba.â€
Ya qarasa mgnar yana sumbatar bakinta.
Aishatu ta ce.
“Ameen ya Allah Abban Farook mijin AISHA. â€
Dariya suka sanya suna rungume junansu, yaronsu na tsakiya shima dariyar yake b'angalawa, Aishatu ta ce.
“Oya je wajan Abba na shirya.â€
Ta k'are mgnar tana beqawa Ma'aruf shi ta shiga ta shirya ta Kira Uwani suka tafi akasuwa ya ajiyesu ya wuce shagon gwanjonsa Wanda yanzu abun ya bunqasa yaransa ma mutum biyar ne sari d'aurin dila kawai yake bayarwa an daina siyar da guda².
Daga kasuwa suka biya gidansu Rabi'ah sun jima sosai acan kafin daga can suka wuce gidansu Ma'aruf, qarshe suka yada zango gidansu Aishatun sai dare Ma'aruf yazo ya tafi dasu gida.

Rahma yadda suke samun kulawa da yaranta abin ba'a cewa komai ita kanta tayi mulmul sai kewar soyayyar Abienta ke d'awainiya da ita, sabida bakinsa da ita sai gaisuwa Jaddatu da Ummu Adnan suke kula da ita yaran kuwa likitoci bakinsu da ita susha nono.
Ahaka Jaddatu tayi qoqarin sake shirya Rahma ta mata gyara sosai a asibitin dan tasan Ana sakinsu ba saurara mata Abie zai ba.
Abie ya qara bud'e makarutun boko da islamiyya, sadaka da manyan masalllatai biyu da sunan 'ya'yansa, an kammala ginin asibitin Rahma an zuba makaita k'wararrun likitoci, Abie ya soke karatun Rahma ya ce baya buqata ba magnar idan yaranta sunyi wayo taci gaba.
Sadaka kamar yadda ya Saba duk juma'a k'ofar gidansa acike take har gobe hakane baya fashi hakan ba qaramin d'aukakasa ya qara yiba.
Chapter 116 · 0% Book details