← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 118

Sashe 86

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Alokacin da labarin mutuwarsu yazo min wallahi tamkar zanyi hauka aranan, ga shi ke kuma aranan wani irin rigima kike min kuka ba qaqqautawa, kin qi kowa ya rab'eki sai ni, ga shi nine zanje 'dauko gawarsu ajirgin da gwamnati ta bayar sabida shugaban 'kasarmu Nada labarin komai.
Haka na barki hannun Ummi kina kuka natafi.
Wlh yadda naga gawarsu Inda aka killace nayi kuka idanuna har basa ganin kirki.
Abby da Zainabu suma sukayi lokacin da muka dawo dakayar aka samu suka dawo hayyacinsu har suka samu damar musu addu'a Abby 'karami kamar ka kirasa ya amsa duk da an masa yanka rago.
Hummm! Bayan rasuwarsu da sati biyu akayi bikina da Zuwaira wanda nace na fasa, amman Abbu ya rufeni da fa'da shi da abby da Ummi da Zainabu, haka na hkr ba'ayi shagaliba, sbd rashin da aka mana rai uku lokaci 'daya.
Zuwaira kwananta biyar ba abinda ya shiga tsanina da ita sai gaisuwa, tana sonki tana nuna miki kulawa, duk da ke awajena kike amman duk safiya zata shigo 'dakina ta miki wanka tin kina kuka bakyaso ganin bata FASA ba kika hkr amman bakya yarda ta tafi dake 'bangaranta.
Satinta biyu na yaba da irin kulawar da take baki tana nuna miki tsantsar kauna duk da bakya wani yarda da ita, hakan yasa na fara sakin jiki da ita, har takai ga na sauke mata haqqinta, amman aranan sai da kikayi bacci saman 'kirjina kamar kullun, na samu na kwantar dake na runguma miki follow naje gareta, badan so ba sai dan sauke haqqinta tinda ban kamata da wata mummunar halaiyaba alokacin da zai hanani sauke haqqinta.
Haka rayuwar tamu taci gaba muna zama na amana kamar yadda ta nuna har tsawon shekara 'daya lokacin kinada shekara biyu, kin fara yarda da ita, ka'dan, sbd yadda take baki kulawa, ta 'daukeki kamar 'diyarta ashe zamba cikin aminci ta mana.
Auremu shekara biyu ta samu ciki, nayi murna sosai za ki samu 'dan Uwa, sosai nake bata kulawa har Allah ya sauketa lafiya, ta haifi yaro namiji mai Kama dani da dake sak, kawai idanu yafi ki, kinyi murna sosai ranar, sbd bazan mantaba na fito daga wanka kenan ina goge jikina kika shigo 'dakin dawowarki da school kika isko jaririn.
Ta baya kika rungumeni kina murna kina fa'din.
“Abienah nayi qani sai mudinga zuwa makaranta tare ko?â€
'Daukarki nayi ina murmushi na beqa miki kumatuna kika sumbaceni, na ce“Toh oya fita na saka kaya sai ki dawo karki sake shigowa 'daki ba sallama.â€
Da gudu kika fita.
Ashe la'bewa kikayi jikin 'kofa baki tafi falo ba, na kammala shirina ina bu'de 'kofa na ganki, raku'be kina shan yatsa.
Sunkayawa nai na 'daukeki muka koma ciki na zaunar dake kan cinyata, na ce“Baby Ummi daman la'bewa kikayi?â€
Kai kika d'agamin.
Na tallabe kumatunki, ina kallonki kamar wata babbar mace haka na fara miki mgna na ce“Kinyi 'da ba 'kaniba 'danki ne Babyna ki yafeni naso ace kece zaki fara haifamin yara sannan kece zaki fara sanin Abineki ya sanki amman Zuwaira ta miki shigar sauri kiyi hkr haka 'kaddaramu tazo.â€
Sam bakisan Inda mgnata ta dosa ba, kika rungumeni kina ta'ba fuskata kina dariya kika ce“Abienah sunan 'kanina irin naka za'a saka kaji?â€
Ba tare da bata lokaci ba kuwa na amsa miki da “Toh my babyna muje na masa hu'duba da Abdulmajid.â€
Ranan naga farin ciki wajanki, wanda hakan nakeso har Abadan.
Zuwaira na zaune kusana, Kina maqale ajikina ina rungume da babyn na masa kiran sallah akunnensa na ra'dama masa suna, na kalleki na ce“My Baby yaronki an saka masa sunan da kikeso?â€
Dariya kikayi kina shafa fuskana kika sumbaci kumatuna kina dariya kika ce“Yeee Abienah nayi Abie babba da Abie 'karami.â€
Dariya muka saka ni da ke, na kalli Zuwaira wacce ta kafemu da ido sai naga kamar hararenmu take, na shafi fuskarta na ce“Zuwaira ya dai ko bakiyi farin cikin sanyama yaron naki sunana ba?â€
Harara wasa ta min tana 'Yar dariya ta amshi babyn tana shayar da shi ta ce“Haba hubby wlh naji da'di ai ka nemi shawara kafin ka ra'damasa farin cikin Ummi shine namu hubby.â€
Naji da'din bayaninta na rungumeku ku ukun inajin da'di da farin cikin samun mace tagari.
Bayan suna ta tafi wanka gida dagani sai ke nima tafiya tasomin dakyar kika yarda na kaiki gidan Ummi daga can kullun ake kaiki wajan baby ki wuni ki dawo.
Bazan ta'ba mantawa bayan ta dawo daga wanka muka 'Dora zaman lafiya, satinta biyu ranan da dare bayan na fito daga wajanta na zauna a falo na kunna Tv ina kallon Al'jazeera sbd ciwon da kaina yake, sai naji ihunki daga bedroom 'Dina, aguje na tafi.
Ashe mafarki kike kina shure² kina kirana kina fa'din.
“Abie zai mutu za'a kashe shi don Allah ka temaka masa wayyo Abie zai mutu.â€
Aguje na iso na kamaki ina girgizaki ina kiranki.
'Daukarki nai muka fito falo na rungumeki ina tofa miki addu'a can naga kin dawo normal kin rungumeni kina sauke numfashi kika tambayeni“Abienah ina Abie 'karami?â€
Kanki na shafa na sumbaci goshinki na ce“Yana bacci shi da mamarsa daga yau idan kinyi mafarki ki dinga addu'a kamar yadda na koya miki kuma daga gobe makaranta zaki na zuwa shekaru biyar kin isa ki shiga makaranta islamiyya.â€
'Yar dariya kikayi kina maqaleni, nace“Ta shi muje mu kwanta.â€
Kafa'da kika maqale kika ce“Abie anan zamu kwana.â€
Ban Musa miki ba na kwanta kan sofa na 'doraki 'kirjina kika rungumeni gam ina shafa bayanki nan kiga shiga min hira ina biye miki muna 'kyal'kyala dariya, duk kinbi kin caku'demin gashina, kamar daga sama naji ihun Zuwaira tana kuka ta fito ta nufomu tana fa'din.
“Abien Ummi Abie 'karami baya motsi...â€
Wata irin fa'duwar gaba naji na miqe kina jikina na zaunar dake na nufi 'dakin Zuwaira aguje har ina Neman fa'duwa.
'Daukarsa nai Kallo 'daya nama yaron na gane ya mutu sabida a 'kalla naga gawa arayuwata tafi dubu, gaba da gaba, ta sojoji ma bazan Iya lissafata ba.â€
Numfasawa yay ya sake shigar da Rahma jikinsa wacce take kuka tana qamqameshi.
“My Baby pls yi shiru mana kiji me ya faru.â€
Kai ta girgiza cikin kuka ta ce“Abie ina son babyn duk da na kasa tunano komai.â€
Bakinta ya kame, yana jujjuya harshensa aciki ba tare da ya tsotsaba, yana buga bayanta ha'di da shafa gashinta.
Ajiyar zuciya ta sauke ta 'dan kalleshi ta sake shigewa jikinsa ta sanya hannayenta ta zagaye bayansa, itama ta shiga buga bayansa.
La'bbanta ya tsotsa na second 7 ya zaro bakinsa yana lashe yawunta da ya biyosa.
Bakinsa ya manna saman kunnenta cikin wata irin murya mai tattare da abubuwa dayawa, amman damuwa tafi yawa.
Hannunsa cikin gashinta 'dayan abayanta, ya ce“Uhmm!
My baby kinsan me ya faru bayan mutuwar Abdulmajid?â€
Ahankali ta girgiza kanta tana buga bayansa.
“Baby keda Zuwaira sai na rasa wa zan lallasa duk kun fita hayyacinku, ita mutuwar 'danta, ke kuma rashin ganinsa ya sanya baki 'daya kin tayar mana hankali sai an dawo da Abie qarami, na kwantatan miki idan mutum ya mutu baya dawowa amman ina kinqi sam. Sai bayan wata uku kika dawo normal wanda har lokacin Zuwaira da ni mun kasa manta yaron.
Bayan mutuwarsa da wata 5 nayi wata tafiya sai dai na kwashe wata uku ba nan, ranan da zan dawo na cika da muranan ganinku da yake dasu Ummi, 'kin fa'dawa kowa nayi na ce surprise zan muku .
Abinda na isko a cikin falon ya rikitani da gigitani, Zuwaira tana jibgarki kamar Allah ya aiko tana fa'din.
“Shegiya me idanun munafukai, na tsaneki sbd ke na rasa 'Dana jin kuna dariya keda mahaukacin uban riqonki na fito aguje ashe na toshe Abdul hanci da pillow ban saniba, na shagala da kallonku sai da kuka gama haukan na koma na iske yarona baya motsi.
Ga buqatar mahaifina bata biya ba, na son mu mallaki dukiyarku tin yaron da muke taqama ya mutu, ga shi na rasa ciki kusan shekara 'daya wlh ke kam kin zame min annoba na tsaneki tin Randa kika zabarma yarona sunah...â€
Wata irin gigitacciyar tsawa na buga mata jikina na rawa na nufi wajanta.
Kekuma kika miqe aguje kika nufi wajena kina kuka kika rungumeni kina nunata.
'Daukarki nayi na rungume ina kallon jikinki duk ya yi ja.
Zuwaira idan nace jikinta ba jini alokacin tsabar tsoro baby banyi 'Karya ba! Sbd ta diririce baki 'daya tsoro ya shigeta, ta rasa me zatace kawai ta fashe da kuka ta yi zaman 'yan bori.

“Ngd Zuwaira da abinda kika min kije duniyace zata koya miki hankali, kisani ni bazan tozarta ki ba amman na gama zama dake, Allah zai sakamin 'dana da kika kashemin, babyna bansan iya lokacin da kika 'dauka kina zalumtarta ba, ba zan ta'ba zama da macan da bata son Rahma ba, kije na sakeki Saki uku bana buqatar zama dake har Abadan. â€
Ina gama mgnar na juya na nufi bedroom kina rungume ajikina sai ajiyar zuciya kike saukewa.
Zuwaira ina jinta tana ihu kamar mai aljanu ta ce bazata bar gidan ba, sai na maidata.
Wanka na miki na shiryaki nima.nayi wanka na zabar mana kayan sawa kusan Kala ishirin na zuba acikin trolley na 'dauke ki muka fito.
Har lokacin tana falon.
Biyomu tai da gudu na sanya qafa na hanka'data ta fa'di na wuceta.
Kai tsaye gida muka tafi na zayyane musu komai amman bance ta kashe 'danta ba na ce dai bazan zauna da MATAR da batason Baby ba shiyasa na dates igiyar aurena akanta.
Chapter 86 · 0% Book details