← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 118

Sashe 26

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin azababban numfashi,wanda yake dab da barin gangar jikinta. Ibtisam ta janyo shi da qarfin tsiya, tamayar da shi mazauninsa, da kyar ta ha'diye wani yawu mai 'dacin gaske, still idanunta cikin nashi. cikin fitar haiyaci tana nuna shi da yatsarta jikinta na kyarrrma ta ce. “Ja'afar! Kanada wacce kake so anan Tchad? Me yasa baka fa'damin ba ka canza ni amatsayin abokiyar rayuwarka? Har na tako 'kafata nazo wajanka, na za'beka . Tabbas ka nunamin halin maza, kuma ka koyamin hankali ka tashe ni a bacci, tabbas na gode sosai Ja'afar ina maka fatan alkahiri.†Ta qareshe mgnar tana danne kukanta ta sakar masa 'kayataccan murmushi ta juya zata tafi, wanda dakyar take ganin gabanta, wani irin jiri ya kwasheta, luuuuu zata zobe, Ja'afar yay saurin tarota ta fa'do jikinsa, ya riqeta yana fa'din. “Ibtisam me kike hakane za ki jima kanki ciwo fa!†Kallonsa tai da kyawawan idanunta masu girma da suka rine lokaci 'daya sukayi jajir, ta sakar masa murmushi ta ce“No! Bazan jimu ba, jeka sai ka dawo bye.†Ta qarashe mgnar tana janye jikinta, anasa ta nufi kewayan su cikin jarumta, take tafiyar wanda bata wani ganin kirki, amman hakan jikinta yake motsawa tamkar tarwa'da, wanda zaka 'dauka da gayya takeyi, sai dai haka halittar tafiyarta take. Ja'afar jikinsa ya yi sanyi, ya kafeta da idanu, yanajin sonta sosai, amman ya kasa ya bita ya rarrasheta. Kansan ya sanya ya fita agidan ya bu'de motar Ma'aruf ya shige yaja ya tafi wacce daga can zai biya ya ajiyeta agidan sai ya dawo a taxi. 'Bangaran Rahma kuwa, lokacin da ta bar wajan Abie2 ta la'be tana zubama Ja'afar kalaman soyayya, cike da shauki Abie 1 na dab da shogowa yaji komai da take fa'dama Ja'afar. Hankalin sa ba 'karamin tashi yay ba, sai da ya jira suka gama wayan, wanda numfashinsa yake barazanar 'daukewa, amman tsabar jarumta irin tasa, yay surin ri'ko hannunta, cikin fizgo numfashin sa wanda yake barazanar barin ruhinsa ya kirata. “Ummina! Waye wannan? Yaushe kuka ha'du? A ina yake? Yaushe ya lalata miki rayuwa da soyayya haka?†Rahma ta kalleshi da 'kananun kyawawan lumsassun idanunta, fuska ba walwala tana qoqarin 'kwace hannunta, ta ce“ Shine za'bina sonsa nake idan ba'a aura min shi ba, komai zai iya faruwa damu, sabida muna son junanmu, Allah ne ya ha'damu...†Wata irin cakumowa Abie 1 ya mata ya matseta jikin bango ya 'daga hannunsa zai wanka mata mari Abie 2 ya riqe ya, yana fa'din subahanallahi! Abdul Majeed da kanka? Haba! Idan rai ya 'baci hankali ke nemoshi.†Ya qarashe mgnar yana kamo hannun Rahma da Abie 1 ya nufi falon dasu, ya zaunar da su. Sai lokacin Rahma ta saki wani irin rikitaccan kuka ta riqe qafafun Abie 2 ta ce“Don Allah ku auramin Ja'afar kar na rasa raina wlh zan iya mutuwa ko mubar gari ni da shi...†Abie 1 ya furta. “Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ummi kina cikin haiyacinki kuwa?†Abie 2 ya kama hannayen Rahma ya ce“Ok ok! Munji zamu aura miki, yi yaushe kuka ha'du da shi?†Rahma ta tsagaita kukanta ta ce“Yaune Allah ya ha'damu.†Abie 1 and 2 suka tsirawa junansu idanu cike da abin al'ajabi jin wai yau amman ta haukace musu hakan? Abie 1 zai magna Abie 2 ya katse shi ta hanyar cewa“Ok ba damuwa bari yazo mu tattauna idan munji asalinsa mun yaba da hankalinsa ba damuwa.†Ya 'karashe mgnar yana kamo fuskar Rahma ya ce“Kalleni 'diyar albarka.†Rahma ta kalli Abie 2 da guntin hawayenta. Idanunta ya gwala sosai yana leqa qofofin hancinta, ya dawo ya cire mata hijabi, amman daga sama ya janye iya kanta, ya bu'de tsakiyar gashinta. Mugun firgita yay sakammakon ganin abinda ya fara zargi. Ayatul kursiyyu ya fara tofa mata da Amanar rasulu. Ya gama ya jamata hijab ganin yadda jikinta yake 'bari ta cakume Abie 1. Abdul Majeed ya sakata cikin jikinsa shima addu'ar yake tofa mata, tana wani irin zanzana. Abie 1 ya ce. “Barta haka aikin babbane miji da matane akanta ayanzu bataji bata gani akan Ja'afar barta kar tai bacci har yazo ina son na fahimci meke faruwa gamone ko aiko mata akayi.†Abie 1 ya sauke 'katuwar ajiyar zuciya ya ce“Ya Allah ka dubeni ka kawomana sauqi cikin wannan musibar da take kunno kai.†Rahma ta janye jikinta tana hararensu ta ce“Sbd na za'bi wanda nakeso kuka laqabamin ciwon aljannu?†Abie 2 ya ce“Kiyi hkr je ki kawoma ba'kon naki abin motsa baki kafin ya iso anan za'a sauke shi.†Ya qarashe mgnar yana 'dauke wayar tata. Cikin murna ta mi'ke tana fa'din. “Ngd Abie2.†Ta fice. Abie 1 ya bita da kallon mamaki. Hannunsa Abie 2 ya riqe ya ce“Kabi asannu ayanzu zata iya maka mummanar tsana idan ta gano baka sonta da Ja'afar, sam bata haiyacinta mugayen she'danune akanta, ka bari muga yaron insha Allahu komai zaizo da sauqi zan rabata da wannan she'danu cikin kwana qalilan insha Allahu zata dawo Rahma sak.†Abie1 sosai ya shiga tsananin tashin hankali, amman jin abinda Abie 2 ya fa'da sai yaji ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali ka'dan, ya jinkina kansa ya kasa cewa komai. Wayar Rahma ta 'dauki ringing. Abie 2 ya 'daga da sauri dan yana zargin Ja'afar ne. Ai kuwa yaji yay sallama ya 'dora da harshen French, ya na fa'din. “Tauraruwar zuciyata ga ni nazo ina 'kofa.†Abie 2 baice komai ba ya mi'ke ya fice. Rahma falo ta isko Raiyana da Jaddatu and Hanan iman. Zama tai can gefe tana ka'da 'kafa 'daya kan 'daya, ta girgizawa ba wanda ta kalla acikinsu bare ya samu arzi'kin mgna. “Latifa!†Ta kira cikin 'dan 'daga murya wanda yake ba halinta bane. Latifa ta iso aguje jin yanayin murya Rahma. “Uwa 'dakina ga ni, barka da hutawa.†Rahma ta jinjina kai ta bu'de 'dan 'karamin bakinta ta ce“Abubuwan motsa baki za ki harha'do ki ha'do da bottle na faro gida kwalin drink 'daya, ki tabbatar jero duk wani abinda zai gani yaji sha'awar cinsa, sai ki kai 'bangaran Abie 2 bari naje na canza kaya.†Ta 'karashe mgnar tana mi'kewa ta kalli Jaddatu ta ce“Jaddati ya dai kallo haka kamar na canza?†Bata jira me zata ce ba ta nufi saman. Latifa kuwa ta mi'ke ta nufi kitchen, domin cika umarnin uwar gidanta. Jaddatu ta ce“Kai wannan abin ba na wasa bane, Rahma batada lafiya wlh ko shakka babu aljanu sun shafeta.†Raiyana ta ce“A'a Ummi wlh Rahma lafiyarta lau, qila wasane irin na jika da kaka...†“Ke! Raiyanatu ki min shiru banson hauka, kece amatsayin Uwa ya kamata ki gano wannan yarinyar ta canza har ubanta da take masifar so ta daina shiga lamuransa, ta daina walwala bata son shiga sabgoginmu kice tana lafiya?†Hanan taja dogon numfashi ta ce“Wlh batada lfy bari Abienta yazo.†Raiyana taji hankalinta ya tashi karfa su 'bata mata shirinta tun ba'aje ko ina ba. Amman sai ta cije tace“Ai kuwa idan hakane bamuga ta zamaba Ummi.†Jaddatu ta kalleta ta watsar ta ce. “Ai naga yanzu atsaye kike.†Rahma ce ta fito cikin wata rantsatsiyar Abaya blue mai adon stones ta mata mugun kyau sai baza 'kamshi take, tana sauri sbd ta manta wayarta acan. Da kallo suka bita har ta 'kullema ganinsu. Abie2 yana fita ya saka aka bu'dema Ja'afar 'katon gate 'din ya shigo da motar ciki. Bayan yay parking ya fito yana kallon irin girman gidan da tsaruwarsa. Amman kasancewarsa mutum mai masifar kamun kai da basar da abu kallo 'daya yama gidan ya kawar da kansa, ya sake danna kiran Rahma. Abie 2 ya 'daga da sallama yana isowa wajansa ya katse kiran ya basa hannu. Ja'afar ya rusuna cikin girmamawa ya gaishesa. Abie 2 ya yi matuqar mamaki ganin Ja'afar baqar fatane, ba ma shi ba shine yaron da ya ta'ba bugar masu mota, toh me hakan yake nufi? Shi dai alokacin yaga basu nuna sun San juna alokacin ba. Fuska ya Saki ya amsa gaisuwar ya Kamo Ja'afar ya miqar da shi, ya ce“Ja'afar ko? Sannan kaine kwanaki ba'ama fi sati biyu ka bugi motar mu†Sai lokacin ma Ja'afar ya tuna. Kai ya jinjina cikin girmamawa. Abie ya ce“Tin yaushe kuka ha'du da Rahma sannan zan maka tambaya tsakaninka da Allah me kamata wanda idanunta suka rufe akanka, har bata son kasancewa damu yanzu?†Ja'afar ya ce“Ni kuwa me zan mata? Wlh ban mata komai ba, ni asalima yaune Allah ya ha'damu amman sai mukaji kamar daman can mun jima, kuyi hkr don darajar Annabi Abba Ku bani Rahma na aureta karku bi cewar ba jansin mu 'daya ba.†Abie 2 ya ce“Dan Allah sunkuyo ka'dan naga kanka.†Kasancewar Ja'afar dogon namiji ne ingarma, Abie 2 bazai iya ganin kansa sai ya rankwafo. Ja'afar bai musa ba, ya sunkuyo da kansa. idan ba idanunsa suke masa gizo ba tabbas abinda ya gani akan Rahma shine akan Ja'afar, toh idan hakane waye ya yi aikin nan? Me hakan yake nufi? Abie ya shafi kan Ja'afar, aransa ya ce“Ina buqatar dogon nazari da wurudin dare na kaima Allah kukana ya nunamin abinda nake son gani acikin baccina. Azahiri ya Kama hannun Ja'afar ya ce“Muje ciki.†Abie 1 na zaune ya buga tagumi suka shigo da sallama. Kallonsu yay yana amsa sallamar, ya mi'ke tsaye. Abie2 ya ce“Karkace komai insha Allahu komai zai warware basa hayyacinsu, dan haka mubasu lokaci qalilan mu bisu da abinda sukeso ka cije ka daure karka mu sa musu.†Abie 1 ya koma ya zauna. Ja'afar ganinsa da kamar Rahma sosai afuskarshi ya gano mahaifinta ne. Ya zube yana gaishesa. Amsawa yay ya nuna masa wajan zama. Ya zauna. Latifa ta shigo da sallama ta dire babban tray da ta shaqo da abubuwan motsa baki da ruwa and drink. Ta tsiyaya a cup ta beqawa Ja'afar ta tafi. Abie 2 shi kawai yakema Ja'afar hira yayin da A 1 ya sadda kasan zuciyarsa tamkar zata tarwatse yakeji. Rahma ta shigo cikin sauri tana mai fito da damuwarta kan fuskarta, sbd tasan Ja'afar ya kirata. Tiris taja ta tsaya ganinsa zaune. Wani irin farin ciki ya baibayeta sai lokacin ta saki fuskarta har batasan lokacin da ta kirasa. “Habiby nah oyoyo.†Dukkansu suka 'dago suka kalleta. Ja'afar ya sakar mata tattausan murmushi, abinka da
Chapter 26 · 0% Book details