← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 118

Sashe 54

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Laraba kallon Tanko take yadda ya juya mata baya, sosai yake fushi da ita ta kasa bacci.
Ahankali ta matsa kusansa tana kiran kiran sunansa.
“Abban Ibtisam! Don Allah kayi hkr, amman bai kamata kace zaka sakeni ka haramta 'yarka akan waccan yaron ba...â€
Katseta yay, “Dan Allah banson damuwa ki shafamin lafiya, nagaji da baqin halinki, wlh matuqar baki canza ba, dab nake da baki mamaki.â€
Shiru tai ta matsa jikinsa sosai ta rungumeshi bata sake mgna har 'barawo bacci ya saceta.
Kwance yake tsakiyar Royal bed 'dinsa, ya lulu'ba da blanket mai taushi da fitar da 'kamshi.
Waya hannunsa yana sakin murmushi idanunsa 'kur kan wayar.
Cikin sansanyar murya ya ce.
“No! Babyna ban yarda ba maza muga cikin ki idan yaci abinci na sani.â€
Daga Espanol, Rahma ce cikin shigar kayan bacci riga da wando red masu masifar sul'bi, kanta na sanye da wata irin hula mai shegen kyau ta 'boye dukkan gashinta aciki, tana saman lafiyayyan gadonta, tana daga cikin bargo fuskata ce ka'dai awaje da hannun da ta riqe wayan, kamar dai yadda Abien yake.
Ashagwa'be ta ce.
“Allah Abiena naci abinci sosai.â€
Abie yana kallonta yana 'dan lumshe narkakkun kyawawan idanunsa, yana shafa sumar kansa wadda ta sha gyara ya ce.
“Ok oya mugani babyna.â€
Kallonsa take tana langawa'bar da kanta asangarce ta furta.
“Shi kenan Abiena ya 'dauki babynsa maqaryaci.â€
Ta idar da mgnar tana janye lallausan pink bargon da take lulu'be da shi zuwa daidai cinyoyinta, ta miqe zaune ta shafi cikinta tana langwa'bar da kanta gefe ashagwa'be ta ce“Toh Abiena ka gani koh?â€
Abie ya shafi sajansa yana murmushi ya ce“Uhmm! Babyna ni banga komai janye rigar.â€
Rahma ta turo baki ta ce“ Promise Rabin raina bazaka sakani cin komai ba adaren nan?â€
Ta tambayeshi tana raurau da idanu.
Kai ya 'daga mata, “No! Baby banyi ba, idan bazaki gwadamin ba shi kenan, pls ki kwanta gobe kunada jarabawa.â€
Da sauri ta janye rigarta shafaffan cikinta wanda yake fari tass ya bayyana tana fa'din.
“Pls Abiena karka kashe wayan kaga fa wlh naci abinci.â€
'Kurr yama farin cikin nata wanda yake kamar bata cin abinci ramin cibinta ya qurama idanu ya kauda kansa yana fa'din“Baby ummina maza ta shi 'dauko lemo da cake kici agabana idan kina son jibi warhaka mu kasance tare.â€
Rahma ta shafi cikinta tana kallon Abie ta ce“Pls Abiena.â€
Wani kallo ya mata ba shiri ta sakko daga bed 'din ta nufi hanyar falo.
Cake ta 'dauko ta nufi kan 'dining ta ta'ba flask 'din ruwan zafi taji akwai ta ha'da black tea ta koma 'dakin ta rufe 'kofa.
Idanu ya zuba mata yana gyara kwanciyarsa yana sakin tattausan murmushi yadda take cin kawai kasan biyayya take masa.
“Baby! Kallonsa tai tana raurau da idanu, ta turo 'dan 'karamin Jan bakinta.
Gira ya 'daga mata.
“Ya isa babyna Allah miki albarka.â€
Cikin farin ciki ta farantawa Abienta rai ta ce“Ameen Rabin raina.â€
Bakinta taje ta wanko ta dawo ta kwanta suna ci gaba da hirasu.
'Barawo baccine ya saceta tana kallon Abienta.
Murmushi yay ya katse kiran yana 'Dora wayar saman bedside drower ya karaton addu'o'in bacci ya kwanta.
★★★
Washegari
*Tchad*
Raiyana hankalinta ya yi mugun tashi idan ta Kira Abie bata samunsa, ga Jaddatu ta sauya mata daga gaisuwarta bata yarda wani abun ya ha'dasu, ta rasa ya zatayi da ranta.
Bayan sun gama breakfast suna zaune falon, Jaddatu na kallon labarai tashar Aljazeera kasancewar nan ne tasharta.
Hanan ta miqe ta ce“Ummina zan kwanta wlh bacci bai isheni ba Abun Iman ya isheni da kira.â€
Jaddatu ta ce“Ai kun kusa min kewa dole Abdul yaje morocco ya 'dauko min Najwa, ummiterh ba zuwa zatayi ba.â€
Dariya Hanan tai ta nufi ciki.
Jaddatu ta 'kwalawa Latifa kira.
A ladafce ta iso ta rusuna tana addu'ar Allah yasa su rabu lfy.
Chapter 54 · 0% Book details