← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 118

Sashe 19

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Su Rahma ba 'karamin tsorata sukayi ba, lokacin da Ja'afar ya bugi bayan motar tasu, wanda take gefen 'daya ya lo'ba, “Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!â€
Shine su Rahma suke maimaitawa dukkanun su.
Jin yadda aka bigi motar su daga baya wanda har far 'din baya na hagum ya fashe take dukkansa ya zube tsakiyar titin.
Security's da suke biye da su hankalinsu ba 'karamin tashi yay ba, aguje suka qaraso wajan dab da motar su Ja'afar,
Sukayi parking suka fito ganin har yanzu mai motar yaqi fitowa ya bada hkr, ga shi jama'ah sun taru sosai.
Rahma ta ru'de tana rungume Raiyana da Iman. ta le'ka Abie 2 jikinta na 'bari ta ce“Abie 2 bakaji ciwo ba ko?â€
Abie ya ce“Fatan kema jijjigar motar bata saka zuciyarki ta tab'u ba?â€
Hanan ta ce“Wannan wane irin jakine ya bugemu a mota amman bazai so ya bamu hkr ba?â€
Rahma ranta ya 'baci ta ce.
“Ai kuwa rashin mutunci ba abinda yake cikin tsarina bane amman wlh sai naga me yake taqama da shi. Ya bugi motar mu amman mu yake jira mu fito ko me? Kodai macace a motar ina zuwa.â€
Ta 'karashe mgnar tana qoqarin bu'de motar dan ta fita.
Abie 2 ya ce“A'a 'diyar albarka zauna bari zan duba muga ko dai yaji ciwone, ayi masa uzuri.â€
Yahaya direba ya ce“Eh hakane kam hajiyar gida kiyi hkr 'barna ce an Riga an mana ita.â€
Raiyana ta ce“Hakane amman kowaye bai kyauta ba, kamar da niyya akayi.â€
Abie 2 ya girgiza kansa, ya bu'de motar ya fito Yahaya na bin bayansa.

Ma'aruf kuwa tsabar tsoro da ru'dewa yasa ya rufe idanunsa ya toshe kunnuwansa, yana kiran sunan Allah, dan ji yake yau sun gama mutuwa zatonsa sun shiga motar sosai sam sai lokacin da Ja'fara ya masa mgna yana 'ko'karin bu'de motar.
“Oga muje muba masu motar hkr don Allah, mune da laifi.â€
Ma'aruf ya kalli Ja'afar ya ce.
“Su basu san tsautsayi ba ai nima an kashe min far 'din mota...â€
Securities ne suka katse masa magana suna 'kwan'kwasa glass 'din motar.
Ja'afar bai tsaya sauraren Ma'aruf ba ya bu'de motar ya fito.
Tsaye suke fuskar nan ba fara'a, sun game rai.
Ja'afar aransa ya ce“Tabb ashe ba hausawa bane, ni kuma ban iya larabci ba.
Cikin harshen français ya ce “Kuyi hkr wlh ku'buce min tai bansa ya hakan ya faru ba.â€
Abbas ya ce“Amman shi ne bazaka fito bada hkr ba kun ha'dawa mutane gosulo?â€
Ja'afar ya ha'diye 'bacin ransa, dan yasan shine baida gaskiya, ya ce“Kuyi hkr...â€
Ma'aruf ya ce“Kar Allah yasa su hkr, ai muma an mana 'barna.â€
Abbas ya harzu'ko zai kaima Ma'aruf duka, Abie 2 ya ce“A'a ku dakata! Me yake faruwa ne harda bugu? Ai mugodewa Allah abinda ya tsaya anan, ba wanda yaji ciwo Allah ya kiyaye gaba.†Ma'aruf ya ce“Bayan ka turo acimin mutunci a baina nasi ni za'a Mara? Ja'afar ya ce“Haba! Me kake hakane? Wannan babban mutum ne, duk abinda zakayi ka guji yiwa babba magana gatsal.â€
Rahma tana kallon komai ta can, ta bu'de motar aharzu'ke ta fito ta dimfaro wajan.
Tana zuwa ta Kama hannun Abie 2 ranta a'bace ta ce“.
Abbas tinda basuda mutunci kuyi duk abinda ya dace sannan gyara mana motar mu kamar yadda muka fito da ita...â€
Ja'afar ya kalleta ya kauda kansa, baisan me ta ce da larabci ba, amman ya mayar mata French ya ce“
Don Allah kiyi hkr ba da gangan bane...â€
Da sauri ta waigo ta kalleshi taja tsaki ta maida masa da French ta ce“Anqi a hkrn kun rainawa mutane hankali, ashe ko Arab 'din ma basaji, duk wanda ya ce zai ta'bamin Abie sai naga bayansa...â€
Abie 2 ya rufe mata baki ya ce“
Abbas muje Ku kuma Ku tafi Allah kiyaye gaba.â€
Ja'afar yarinyar tai mugun ba'kanta masa rai yaji ya tozarta, amman ya danne 'bacin ransa ya ce“Merci beaucoup papa.â€
Ma'aruf bai ce komai ba, sbd yay nisa wajan kallon Rahma da nazartar ta idan zai fara, ga dai Raha Abdul Majeed Abdulwahab Marocco amman ba damar saceta.
Raiyana tana kallon duk abinda yake faruwa.
Murmushi mai taushi tai, aranta ta ce“Anzo wajan.â€
Zaunar da ita Abie2 yay mazauninta yaja kumatunta ya ce“Baby rigima! Mu gode Allah babu wanda yaji ciwo.â€
Rahma ta turo baki batayi mgna ba, ya rufe motar ya isa mazauninsa Yahaya yaja motar yabar wajan.
Yayin da su Abbas ke biye da su.
Ja'afar na driving cikin 'kwarewarsa yana fesar da zazzafan huci, yana mamakin me yama yarinyar? Ya ga hkr yake basu, idan ba dan shine baida gaskiya ba su isa ya basu hkr ba, koda kuwa za'a tara masa mutanan tchad baki 'daya ba wai kallon suna larabawa ba.
Tsaki yaja yana fa'din.
“Shiyasa na tsani yawancin masu ku'di basuda adalci...â€
Ma'aruf ya ce“Hummm! Har ni?â€
Ja'afar ya ce“Ka gyara gaskiya bansan naga mutum nawa babba rashin kunya, wannan zai kusa haifarka fa, koma ya haifar kake neman masa rashin kunya.â€
Ma'aruf da yake yana son shirya iya shege ya ce“Na bari Ja'afar Ngd da shawara, yarinyar nan tanada jin kai, ko dan ta ga tanada kyau.â€
Ja'afar bai tanka masa ba ya ta'be baki, shi kam baiga kyau ba, haushinta ma yake ji, kyawun mace 'daya yake gani cikin 'yan matan duniya Ibtisam 'dinsa.
Kusan tare su ka shiga airport, Ma'aruf sai message yake da wata number yana dariya.
Ma'aruf bai fice minti 15 jirginsu ya 'daga zuwa Gabon, Ja'afar ya juya zuwa gida.
Su Rahma sun shafe 25 minutes kafin jirgin su Abie ya iso. Abie 2 ya mi'ke ya 'dan zagaya ya dawo.
Su na zazzaune wajan da ake jiran matafiya sai ga shi shi da security 'dinsa, sanye da wata narkekiyar shaddah me mai'ko.
Rahma ta mi'ke cikin matsanaicin farin ciki ta ruga aguje.
Hannayensa ya ware mata cikin tsananin farin ciki ta fa'da saman faffa'dan 'kirjinsa, ta 'kan'kameshi tana sakin wani irin numfashin, ta ceâ€Abiena Rabin raina, I miss you so much.â€
'Kan'kameta yay ya shafa bayanta, bakinsa dab da kunnenta murya atausashe ya ce“
Miss u too my baby ummina. Kinyi kewar Abie sosai ne¿â€
Luf tai ’Kirjinsa tana 'daga kanta alamar Eh.
Rainaya ta iso ta ce“Toh Iyayan soyayya uba da 'yarsa Abien Rahmerh barka da zuwa.â€
Rahma ta janye jikinta ta Kama hannun Abie tana murmushi.
Amsawa yay fuska sake ya 'dauki Iman Hanan ta turo baki gaba tana fa'din.
“Yaya Abdul ta 'yarsa yake da matarsa baiga 'kanwarsa ba?â€
Abie ya rungumeta yana murmushi ya ce“Ban isa naqi ganin Ƙanwata ba.â€
Abie 2 ya ce“Yalla'bai barka da zuwa.â€
Abie 1 ya sakesu ya rungume Abie 2 sukayi musahaba.
Rahma sai murna take ta yi Abie biyu.
Motar su Abbas Abie 1 ya shiga Rahma ta ce nan zata shiga. Ai kuwa ahaka suka jera zuwa gida, Abbas na masa bayanin tsautsayin da ya faru.
Abie ya ce“Allah ya tsayar nan.â€

Ja'afar kai tsaye wajan gyara yakai motar, sbd far 'din gaba guda ya fashe, sai an saka sabo, daga can ya nufi gida.
Ibtisam bayan ta gama cin abincin ta fito ta leqa kitchen ta ga ruwan zafin har ya tafasa, ta kashe reshon ta juye abokiti ta, ta shige bayin, tai wankanta tass, ta fito.
Mai ta shafa na Ja'afar mai azabar 'kamshi, ta sanya Riga mai shegen kyau ta mata cif har 'kasa ta yane kanta da mayafin abayar, ta fesa turaren Ja'afar ta kwanta saman katifar tana fa'din.
“Mon amour ina sonka har na mutu. Yaushe zan tsaya na auri mutum kusan sa'an Babana, Anna Baba ku yafemin ban gudu dan 'bacin ranku ba.â€
Ta 'karashe mgnar tana sakin kuka abin tausayi.
Ja'afar tinda ya shigo yake jin shashek'ar kukanta.
'Dakin ya shigo ya ga ta ha'da kai da guiwa, tana rusar kuka.
Wani irin tausayinta yaji ya kamasa, amman yana son ya nuna mata kurenta.
Chapter 19 · 0% Book details