← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 118

Sashe 51

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laraba na can tana lallashin Ibtisam akan ta kwantar da hanlinta dole Ja'afar sai ya saketa tinda bata sonsa. jin hakan ya saka ta daina kukan, Abie kawai yake mata gizo shi kawai take gani yana mata murmushi, duk wani gefen tana jin Ja'afar aranta.

Tanko da Ja'afar su na zaune suna mgna sama² kowa ransa ba da'di.
Lokacin sallah yana yi Tanko ya shiga ya koro Ibtisam tana kuka ta nufi 'dakin.
Tsaye ta iskosa yana fesa turare zai tafi masallacin da yake jin ana shirin tayar da sallah.
Baki ta zumb'uro tana gunguni.
Kallon arziqi bai mata ba, ya sanya kansa ya fice cikin takunsa na 'kasaita.
Tsaki taja ta nufi toilet 'din.

Yamma liqis jirginsu Rahma ya sauka a 'kasar Espanol, cikin babban birninsu (Madrid) .
Direbanta tare da masu tsaron lafiyarta sukazo tarbarta.
Sanye take cikin wata dark blue din abaya wacce taci uban adon stones, ta yane kanta da mayafin rigar tana sanye da baqin glass wanda ya qarama farar kyakkyawar fuskarta kyau.
Wani shegen rufaffan takalmi ne blue aqafarta wanda ya mata kyau matuqa, tana rataya da handbag 'dinta ta fara saukowa daga matattakar jirgin, tana jin wani irin farin ciki na ratsata.
Cikin harshen larabci cikin siririyar muryata mai da'di ta 'daga hannayenta tana fa'din.
“I miss you Espanol na dawo Alhamdllh Allah.â€
Kai tsaye wajan kayanta ta nufa bayan ta kammala duk abinda ya dace taja babbar trolley 'dinta ta nufi wajan da tasan ana jiranta.
Tsaitsaye ta iskosu, Aslim na riqe da wata farar babbar takarda mai kauri an rubuta *Welcome Rahmatullahi Abdulmajid Abdulwahab.*
Kyakkyawan murmushi tai musu ta 'daga musu hannu alamar ta gode, sbd daman ita dai ba gwanar mgna bace, hirata Abie sai Jaddatu Hanan su Ummita 'yan Morocco sai Anee Rafeeq ma ba wani mgna take masa ba sai katari.
Mota suka bu'de mata ta shige suka rufe, aka sanya trolleyn ta both, direba da securities biyu na kusansa haka suka bar airport 'din.

*Gabon*
Aishatu ahalin da ta samu Ma'aruf yasa tai shiru bata tanka masa ba, ta kwanta gefensa, haka suka kasance har kwana biyun Ma'aruf bai wata nutsuwa ko walwala.
'Bangaran Rabi'ah ta dage da 'karfi sai Ma'aruf ya sota ya aureta har ta shiga bin malamai.
Zaune suke anata kiran wayarsa yaqi 'dauka.
Aishatu ta ce“Dan Allah ka 'dauka bakasan alherin da yake cikin kiran ba...â€
Tsawa ya buga mata yana fa'din.
“Uban wa yace miki alkhairine?â€
Idanu ta zazzaro jin ya zageta.
Wani kiran ya kuma shigowa.
Cikin fusata ya 'daga kiran yana fa'din.
“Dan kutumar uban uwar babanka Inusa karka sake kirana agidana...â€
Daga can aka katse ko me aka ce masa ya miqe tsaye yana fa'din.
“What?â€......

_💃ðŸ»'Yar Ajin Ma Sha Allah🥰_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/5/22, 18:19 - Buhainat: ```D A```

```51&52``

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_

Ficewa yay daga cikin falon yana kirta ruwan masifa.
“Wai me kake fa'da ne haka? Ba nace adakatar da komai ba, har na nemeku? Toh dan kutumar ubanku ku mayar da kayan muhallinsu, tare da kiyaye dokokina wlh idan aka samu akasi! Hummm! Adakatar da komai nace bana buqatar komai me yasa ba kwaji ne? Na ce mgnar Rahma abarta,ta kowa maâ€
Ya 'kare mgnar cikin 'daga murya yana huci. Ko me aka ce masa ya sauke ajiyar zuciya, yana fa'din.
“Ok nima ina tafe jiya naso zuwa akwai dalilin da ya tsayar dani.â€
Bayan sun gama wayar, ya kira wata number, bugu 'daya aka 'daga ya ce.
“Duk na tsayar da komai asakesu cikin sirri.†cike da bada umarni yay mgnar yana katse wayan, zai koma ciki sai ga kiran Rabi'ah.
Tsaki yaja ya kashe wayar baki 'daya.
Inda ya barta nan ya iskota zaune ta yi tagumi.
Zama yay ya rungumota jikinsa yana shafa cikinta, ha'di da kissing 'din wuyanta.
Kuka ta sakar masa tana fa'din.
“Ma'aruf yau ni kake zagi ko?â€
Matseta yay yana fa'din.
“No! Masoyiyata wlh aharzuqe nake bake na zaga ba kiyi hkr, bakisan halin da nake ciki bane, idan na zageki iyayena na zaga tinda ni dake abu 'dayane.â€
Zatayi mgna wayarta ta 'dauki ringing.
Ganin Rabi'ah jikinta na rawa ta 'daga kiran.
Ma'aruf yaja tsaki yana fa'di.
“Kibi asannu makashinka na tare da kai!†baki ta saki tana kallonsa ha'di da amsa wayar.
“Hello 'kawata ykk? Kwana biyu kin 'buya?â€
Daga can Rabi'ah ta ce.
“Uhmm! Bari kawai, y bbyna? Hope kina lfy? Ke 'daya ce nazo yanzu?â€
Aishatu ta kalli Ma'aruf wanda idanunsa suke rufe ya miqe saman sofa ta ce“A'a ogan na kusa idan ya fita zan kiraki ko kuma ma kizo ai baida matsala.â€
Rabi'ah tai kicin² rai 'bace ta ce“No! Ki barshi kawai sai anjima.â€
'Kitt ta kashe kiran.
Aishatu tai dariya ta ce“Au yau 'yan kunyar ne da naga kina zuwa idan yana nan.â€
Ta 'karashe mgnar tana ajiye wayar.
Ma'aruf ya ce“Bakida wayo sai duniya ta koya miki hankali.“
Ashagwa'be ta kwanto jikinsa tana sakin kukan takaicin kasancewar shi 'dan kidnapping da safaran mata.
“Dan Allah karki qaramin zafi kiyi shiru me ya faru? Cikin kuka ta ce“Damuwarka nakeson sani?â€
Kai ya girgiza aransa yana fa'din.
“Kwanciyar auren mu da duk wani abu da zan miki na kyautatawa, da akasin hakan, sai kin shelawa duniya bare wannan gagarumin lamari.
(Haba Ma'aruf wa ya ce maka Aishatu bata san sirrinka ba?😂)
“Ni ba abinda yake damuna ki tayani da addu'a kawai.â€
Kai ta girgiza ta Kama hannunsa suka shiga daga ciki, sosai ta jiyar da shi da'di marar misaltuwa sbd sun jima basu ha'duba. Bayan sunyi wanka sun nutsu suka shirya suka bar gidan zuwa yawo duk 'ko'karinta na son ta ga ta cire masa damuwarsa.
Rabi'ah kuwa sai kai komo take ranta 'bace wulaqancin da Ma'aruf yake mata, takaicinta asirin da ta masa har yanzu shiru bai kamasa ba, Malam ya ce da kansa zai kawo kasan kirane zasu masa.

*Tchad*
Raiyana tajima sosai tana baccin na ban mamaki kafin ta farka.
Da idanu take bin 'dakin da kallo, 'dakin baqi na 'kasa.
Idanunta ya sauka akan auntie Saro wacce ta rafka uban tagumi, hawaye na zabu akan fuskarta.
Raiyana ta zabura tana fa'din.
“Aumtie Saro lafiya? Me nake a'dakin saukar baqi? Me ya faru dani?
Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Shi kenan wani abin ya sameni ko auntie Saro?â€
Cike da jin haushinta da 'kyamar halinta, auntie Saro ta ce.
“Tirr da halinki Raiyana iyayanmu basu bamu gur'batacciyar tarbiya ba, me kika nema kika rasa aduniya agidan bawan Allahn nan, da har kika yarda kika fa'da halaka, kike son nakasa masa rayuwar 'yarsa 'kwaya 'daya? Ashe duk yadda nake baki shawara baki 'dauka ba? Kika shiga bin bokaya da 'yan tsubbu, kina sa'bon Allah kina shirka kawai dan ki 'batawa Rahma rayuwa.
Shin me ta miki ne? Ai yanzu wa gariya ya waya, ke samun namiji irin wannan ba abin alfaharinki bane...â€
Raiyana ta fashe da kuka tana 'Dora hannunta akai tana zazzaro idanunta ta ce.
“Na shiga ukuna! Wa ya lanqayamin sharrin wannan?â€
Saro cike da takaici ta ce“Aljannu da kika tura musu suka dawo kanki...â€
Kakaf ta bata labari.
Raiyana kanta ta saddda cike da kunya tana kuka tana fa'din.
“Kaicona da rayuwata Abien Rahma da kansa ya nemomin magani na warke? Allah sarki na zalumci kaina amman auntie Saro ba laifi na bane wlh kishin Rahma nake duk da tana 'yarsa natsani kulawar da yake bata, ina sinsa kamar na ha'diye shi, kulawar da yake bata, wlh tana min ciwo sosai, shiyasa nayi hakan dan na nisantasu ni banyi dan na cutar da ita ba...â€
Auntie Saro ta ce“Humm! Mamaki ai cutarwa ta nawa kuma Raiyana ka gama mutum da baqin aljani kace baka cutar da shi ba?â€
Raiyana ta fashe da kuka tana fa'din.
“Yanzu kowa yasan abinda nayi kenan? Wayyo Allah na! Na cuci kaina da rayuwata, auntie Saro ya sakeni ko? Wlh mutuwa zanyi ku tayani basa hkr.â€
“Ni ban saniba wannan sai ki jira shi, yazo baya 'kasar kije ke kika sani dan kin gama cutar da kanki, ni kinga zan tafi tinda kinji sauqi, bazan iya da kayan kunya ba, Allah ya jisehemu alkhairi.â€
Auntie Saro ta miqe ta shiga ha'da kayanta.
Raiyana tai tagumi tana kallonta har ta gama ta kalleta ta ce“Ni zan tafi.â€
Raiyana ta miqe tana 'dauka hijabin da ta gani gefen gado ta saka jikinta ba 'kwari ta ce“Bari nazo.â€
Fitowa tai.
Jaddatu suna zaune ita da Hanan Iman na game awayar Hanan suka ga Raiyana tana nufosu.
Jaddatu kallo 'daya ta mata ta 'dauke kanta, tana karka'da sanda.
Raiyana jiki ba kwari cike da kunya ta zube tana gaida Jaddatu.
Ada'kile ta amsa, ba tare da ta kalleta ba. Hanan ta ce“Masha Allah Raiyana ya jikin? Sannu Allah ya qara sauqi.â€
Raiyana kanta a'kasa ta amsa.
“Da sauqi Amin Ngd.â€
Miqewa tai ta haura sama Jaddatu na binta da harara.
Hanan ta ce“Don Allah Ummi ba ruwanki ki saka musu ido ita da Ya Abdul.â€
Tsaki Jaddatu ta ja batace komai ba, ta maida hankalinta kallon Tv tashar Aljazeera.
Raiyana 'dakinta take bi da kallo ya fara 'yar 'kura alamun kenan ta kwan biyu akwan? Hawayen fuskarta ta share ta kwaso sabulu da turare da mayuka da ku'di da turaman atamfa biyu ta sauko.
Jaddau na binta da kallo bata tanka ba.
Auntie Saro taqi kar'ba ba yadda Raiyana batayi ba, ta ce“Ko ya kike ke jinina ce ba dan ki biyani ba nayi jinyarki na tafi Allah yasa hakan ya zama darasin Rayuwa agareki Allah yasa kin shiryu, yanzu kin gane Wahida ba 'kawar arziqi bace.â€
Tana gama mgnar ta fice.
Sallama ta wa su Jaddatu ta tafiyarta.
Raiyana tana kuka wiwi ta gyara 'dakin tsaf ko ina ta sanya turare ta kwashi kayanta ta nufi sama, tana cikin tashin hankali da mugun tsoron tararrabi take bata san irin hukucin da Abie zai 'dauka akanta ba.
Chapter 51 · 0% Book details