← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 118

Sashe 25

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jamilu tsaye qofar gidansu Ibtisam na kwa'da sallama.
Tanko ya tsame hannunsa cikin abincin ya fito.
“Ah Alhj Jamilu.â€
“Wai Baba har yanzu ba labarinta ne? Wlh na fara gajiya da jira kawai Ku harha'domin kayana na samu wata na aura.â€
Tanko ya ce“Wlh banda abinda zan baka bayan kayan lefenka.â€
“Oh haka kace? Tih wlh sai dai Ku ban Taslim...â€
Wani uban Mari Tanko ya 'daukeshi da shi ya ce“Wlh kayi ka'dan bazan bayar ba, kaje kayi qarana duk gidan Uban da zakaje itama na fasa aurama ko ta dawo.â€
“Ni ka mara sabida dukiyata na ce aban 'kanwa tinda ya ta shiga duniya? Ka jira kagani.â€
Ya qarashe mgnar yana tafiya.
Tanko ya dafe kansa da yake sara masa, sai yau yake jin takaicin kansa na amincewa da ya yi zai aurama Ibtisam Jamilu mutum kamar biri.

*Tchad*
Rahma bacci tai sosai a'dakin Jaddatu, Abie ya kwantar da ita. Sai da Jaddatu ta idar da,sallar Maghreb ta tasheta, dakyar ta tashi jikinta na mata mugun ciwo, ta yi duk tunanin duniya me ya kawota 'dakin Jaddatu ta kasa tunawa, takuma qi tambayar Jaddatu, sai kafa'da da ta ka'da alamar ina ruwanta ma, hakan yasa ta fito ta haye sama.
Wanka tai ta yi sallah tana saman darduma, ta 'dauki wayanta tana dubawa ko zataga kiran Ja'afar amman shiru bai kira ba.
'Kwalla ta tarun mata cikin idanunta, ta mi'ke sanye da abayar sallar ta sauko qasa.
Ba kowa falon sai qaran Tv.
Tsaki taja mai tsayi ta fice daga falon ta fito ta nufi part 'din Abie 2.

Ma'aruf zaune cikin falo waya yake yana 'kyal'kyala dariya.
“No! Kasan ni tamkar mage nake mai kwanciyar 'daukan rai, ai cikin lamurana ban gaggawa, sannu ahankali har na cinma burina, saura 'kiris na ma Tchad ban kwana na har abdan, tin ba a farga dani ba.â€
Ya qarashe mgnar cikin mahaukaciyar dariya yana shafa tumbinsa, ya yana katse kiran.
Kira ya shigo wayarsa yaga baquwar number ba suna.
'Dagawa yay tare da sallama.
Daga can Rabi'ah ta ce“Amincin Allah ya tabbata ga ma'abucin kyau fara'a kwarjini haiba da kyau, tsayayyan namiji mai jini ajika.â€
Ma'aruf ya ha'de fuska tamkar me mgnar na gabansa ya ce“Ban 'bata lokacina idan bansa da wa nake mgna ba.â€
'Kitt ya kashe kiran ha'di da kashe wayar baki 'dayanta, ya sheqe da dariya, yana tafa hannayensa ya ce.
“Wow! Amman yarinyar akwai kalamai sai naji kamar nasan muryan?â€
Ya qarashe mgnar yana 'daukan wayansa 'dayan ya Kira Aishatu.

*Gabon*
Rabi'ah wani irin takaici ne ta turniqeta, wai baima san ita wacece, bayan tin suna soyayya da Aishatu suna yawan gaisawa da shi ido da ido, haka tana yawan zuwa gidan Aishatun.
Baki ta ciza ta ce“In kasan wata ai bakasan wata ba, wlh sai na mallakeka ba ruwana da amincina da matarka. Dan itace ta kwa'daitani da komai naka, wlh sai anyi kashi mu raba.â€
Ta 'karashe mgnar tana fitowa daga toilet 'din Aishatun.
Aishatu zaune tana shan kunun gya'dar da uwani tai mata, wayanta ta 'dauki ringing.
Ganin Ma'aruf ne tai picking call 'din ta Kara way an a kunnenta tana turo baki ta ce“Wai ina ka shiga yaune baby nata harbina.â€
Ma'aruf ya 'kyal'kyale da dariya ya ce“Shafomin shi kice yama babansa addu'a Allah ya basa mai 'duwawu yama mama kishiya.â€
Aishatu tai dariya ta ce“Sam yau bazaka 'batamin raiba Ma'aruf kaje komai kake kai da,Allah haka dai kakeson marar 'duwawun.â€
Dariya yay ya ce“Ashe madam ta gane mijinta 'dan tsokanane. Hope kina lfy?â€
Baki ta murgu'da ta ce“Ban saniba.â€
Rabi'ah da take tsaye ta kafeta da ido tana mamakin har ya kunna wayar ne.
Sun jima suna hira kafin ya ce mata zai kira video call anjima.
Aishatu ta ajiye wayan tana kallon Rabi'ah ta ce“Wai ina kika da'de haka¿â€
Rabi'ah ta zauna kusan Aishatu tana yamutsa fuska ta ce“Wlh cikina ya mur'da bari na tafi dare ya fara sai wani jiqon kuma. Ke kam bakya jimawa da waya.â€
Ta qarashe mgnar tana 'daukan wayan tana dubawa baqin ciki kamar zai kashe Rabi'ah da kishi.
Aishatu tai dariya ta ce“Wlh idan duk sati zan ce Ma'aruf ya siyamin waya zai siya min, sbd son da yake min, yanzu haka ya ce zai biyo min da wata rantsatsar Samsung Galaxy.â€
Rabi'ah ta ce“Allah ko? Tabb ai ke kam kin fimu morewa, Allah ya qara dan'kon 'kauna, ni kam na fasa auren wancan banzan can mai jiji da kai ba wani abin hannu yo kyau zanci dan ubansa.â€
Aishatu ta duma mata duka abaya ta ce“Wlh ki rufawa kanki asiri ba ruwana ah toh. Ai ni da kaina nasan Ma'aruf ya ha'du ga bai gajiya ashimfi'da sai dai kai ka gaji ga iya romantic kamar zan mutu nakeji sbd dad'in abin. â€
Rabi'ah ta matse qafafunta tanajin wani yammm jikinta tsabar jin son inama itace. Aranta ta ce“Wlh sai na aureshi naji abinda kikeji.â€
Takaicin jin labarin ya saka Rabi'ah miqewa ta ce“Toh ni na tafi insha Allah nida shigowa wannan gidan sai bayan aurena.â€
Aishatu ta ce“Wayyo ni babbar 'Kawa pls kiyi Ku tsayar da mgna kar azo ayi biki cikina ya tsufa na kasa ta'buka abin azo agani wajan auren 'kawata.â€
Rabi'ah ta ce“Nan kusa 'kawata karki damu bye.â€
Aishatu ta rakota ta saka Nura direba ya tafi ya kaita gida.
Ita kuma ta dawo ta fara kallonta Tv tana jiran Ma'aruf ya kirata.
*Tchad*
Ja'afar yana fitowa daga sallar isha, yay shirinsa cikin wata 'danyar shaddah mai kyau, maroon colour wadda Ma'aruf ya 'dinko masa, sosai tai masa kyau sai baza 'kamshi yake.
Yahuza ya kalleshi ya ce“wai ina zuwa ne kana 'kyalli sai ka ce ango?â€
Ja'afar ya shafi sumar kansa, ya 'dora hula wacce tai masifar masa kyau ya 'dan tauna le'bansa na 'kasa bai tanka su ba, ya zaro wayarsa ya fito yana latsawa. Jikin 'kofar gidan ya tsaya, ya dannawa number Rahma Kira.
Lokacin Rahma na wajan Abie 2 da farko, da ta shigo ba wata mgna suke sosai ba, amman bayan yaje yay sallar isha yazo, ya shiga bata lbri, yadda yake bata labarin wani makaho ya sakata dariya har takai ta riqe hannunsa tana 'kyal'kyalata dariya.
“Wayyo Abie 2 karka saka cikina ya qulle...â€
Dai-dai lokacin wayanta yay qara.
Duk number ba suna, jikinta ya bata Ja'afar ne.
Cikin rawan jiki tai picking call 'din ta manna wayar kunnenta tare da sallama.
Ja'afar daga can ya amsa sallamar yana lumshe idanunsa, cikin shaukin 'kaunarta ya kirata.
“My Qalbi! Muryaki sanyi ga da'di fiye da sarewa,gaki da tausasa murya. Wlh ina sonki,
so wani abu ne mai kyawu, kuma wani yanayi ne da mutum zai so ya dam'ke. So shi ne yanayin da kan sa ka ji ka a raye.
My Qalbi ina fatan kin fahimci cewa zan so ki har karshen rayuwata, sabida ba kin kasance budurwata ka'dai ba, ke ce Aminiyata, 'yar balarabiyata je t'aime. Ga ni nan tafe gareki tauraruwar mata, ki fito domin tarban masoyinki.â€
Rahma batasan lokacin da da'din kalaman Ja'afar suka sakata mi'kewa ba, ta fara taku cike da wani irin salo tamkar tana gabansa, murya atausashe cikin harshen French, ta fara maida masa martanin kalamansa.
“Habiby nah! Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyin mu na fita a tare. Ina so mu kasance a tare har abada, Ina Son Ka!
Ana gane kyawun shuka ne idan har an gama ta da taki.
Tayaya za a gane sama idan har babu 'kasa?
Kamar haka ne, farin cikina zai yi wuyar bayyanuwa matuƙar ba ma tare da juna.
Na kan shiga damuwa a dukkan lokacin da na duba gefena ban gan ka ba.
kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tunanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya nan kusa idan ubangiji ya amince mana Ina Son Ka! Habiby nah, Allah ya kawo min kai lafiya.â€
Ja'afar dukkan illahirin jikinsa rawa yake, tsabar ru'dewa da kalamanta, sosai yake jin 'kaunarta fiye da komai aduniya.
Manyan kyawawan idanunsa masu lumshewa ya bu'de yaja dogon numfashi ya ce“My Qalbi 'yar balarabiyata ina sonki ganinan tafe bye.â€
Ya katse kiran.
Idanunsa ya firfito da su waje sakammakon ha'da idanu da sukayi da Ibtisam, tsaye gabansa dukkan illahirin jikinta zanzana yake wata irin zufa ta wanke mata fuska tamkar an zuba mata ruwa.........!
2/12/22, 20:44 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_

25&26

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_
Chapter 25 · 0% Book details