← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 118

Sashe 52

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Espanol*
Wani tamfatsetsan gidane na gani na fa'da, wanda aka ha'da jin da'din duniya, gidan ya ha'du matuqa wanda yake mallakin Rahma a'kasar ta Espanol, Abie ya Gina mata tin lokacin da ta za'bi 'kasar da zatayi karatu, sbd baida burin ta zauna amakaranta ko Kama gidan haya duk irin arziqin da Allah yay masa.
Dole idan mutum yaga tsarin gidan ya burge shi tsabar kyau, ya 'kayatu da shuke².
Falon yanada girma sosai yasha kayan alatu, tamkar gidan amarya ba 'yar makaranta ba.
'Dakuna kwana ukune manya biyu d'auke da manya gadaje na zamani irin na turawa, sai 'dayan wanda ba komai cikinsa sai katifa da carpet da Tv gefen kitchen yake, nan Meerah mai aikin Rahma take, biyun kuwa sai abin wani corridor ake zuwa ajere 'daya na kallon 'daya tsayawa fa'din tsaruwar 'dakaunan da kujerun ciki da sauran abubuwa 'bata lokacine.
Suna isa gida Rahma ta fito ta nufi hanyar falonta.
Meearh ta gyara ko ina sai 'kamshi yake tai mata dadda'dan girki sosai suka gaisa cikin mutunci, tana ma Rahma sannu da zuwa da jan trolley bakin 'kofa wacce direbanta ya shigo mata da ita.
Rahma tai murmusa lokacin da shiga 'dakin ta ga komai agyara ta murmusa ta ce“Thank you Meerah.â€
Kai ta jinjina ta ce“Ayi wanka azo aci abinci pls.“
Kai Rahma ta 'daga ta wuce ciki ta fara fatali da kayan jikinta ta 'dauki remote ta kunna Ac ta nufi bathroom.
Ruwan 'dumi ta ha'da sosai, tai wanka ta jima kafin ta fito 'daure da towel, kyakkyawan jikinta mai kyan surah na 'digar da ruwa, sanyin Ac sosai yake ratsata.
Amman bata wanke gashinta ba dan da safe katin tafiya ta wanke shi.
Saloli ta rama ta shirya ta fito falon ta 'dan ci girkin da Meerah ta mata, ta dawo falon ta kunna Tv plasma.
Ta zauna tana latsa waya zata kira Jaddatu, sai taga message 'din Abie.
Murmushi mai kyau kan fuskarta ta shiga wajan message 'din.
_“Hello Babyna ykk hope kina lfy kin iso lfy? I miss you muahhhhh sai na kiraki ina busy bye🥰._
Cikin murna ta shiga mayar masa da amsa.
_“Alhmdllh lfy nazo, A'a banida lfy Abie rashin ka ya saka min kasala inata kewarka, Abie rabin raina pls ina jiranka jibin Allah ni kuka zanyi tayi naqi cin abinci idan baka zoba.😢_

Tana tura masa ta kirasa tana ringing ba'a 'daga ba, sai taji wani iri.
Ranta ba da'di ta kira Jaddatu suka Sha hira.
Kiran Anee ya shigo wayarta ta 'dauka tana lumshe idanunta asanyaye ta ce.
“Habibty Anee ykk?
Daga can Anee tai tsalle ta dire tana murna ta ce“ina lfy barkan ki da zuwa Habibty, wlh tin 'dazu Rafeek yake damuna yana son ya ganki ya takura min da kira sai munzo.â€
Rahma ta saki sansanyen murmushi tana dafe goshinta ta ce“Uhmm! Ni wlh Anee acikin ru'du nake shiyasa ban basa fuska, sbd gudun abinda zaije yazo, shiyasa nake baya² amman bari Abie yazo zanyi qoqarin masa tambaya cikin nutsuwa idan na tabbatar da mgnar gaskiyace ba zai yuba naci gaba da kulashi, duk da daman sama² ne nake kulashin, sbd kar na zurma dayawa na dawo na cutu.â€
Anee ta ce “Me yake faruwa? Ko dai mgnar ce akan kinada aure?â€
Rahma ta numfasa ta ce.
“Eh ita fa! wlh, dan Abie wannan Karon ma ya tunatar dani.â€
Anee ta ce “Wlh nafi jin wayo yake miki dan ki tsaya kiyi karatu, karki fara soyayya, amman nawa kike da har za'ace kinada miji da 'da'dewa.â€
Rahma ta numfasa ta ce“Eh hakan nima nafi zargi, amman ki rabu da shi gobe zamu ha'du a makaranta...â€

*Australia*
Abie sai kusan magarib ya samu ya dawo gida, wanka yay suka tafi masallaci su uku, basu dawo ba sai bayan isha'i.
Laraba da Ibtisam zaune atsakar 'daki.
Laraba ta ce“Ince dai babu abinda ya miki?â€
Ibtisam ta zaro ido tana girgiza kanta ta ce,“Tabb abinda sai wani shan 'kamshi yake min, wai dan nace ban sonsa, wlh Anna yaban haushi wai ke kinga ranan, yadda yake mata kalaman soyayya ko tsoron Allah baya ji, na baro ku na gudu naje wajansa sbd son da nake masa na tsakani da Allah. Anzo an lanqayawa aljannu qarya hummm!â€
Laraba ta ce“Ai maganinki kenan ba yau nake ganemiki baqin yaron bazai yi wani abun arziqi ba, amman kika nace wa gari ya waya ga shi yanzu an 'daura aure, toh ke da ubanki wa kikeso yanzu?“
Ibtisam ta zum'buro baki gaba tana rau-rau da idanu ta ce“Ni wlh wannan babban balaraban wanda ya kawomu Allah Anna bakiji yadda nakeji ba akansa sai naji ashema Ja'afar abaya banso shi ba...â€
Wani irin bugu taji abakinta sai da ya fashe jini take ya fara bin gefen bakinta.
Ibtisam kuka take sosai tana 'boyewa bayan Laraba, wadda ita kanta ta gama tsorata da lamarin Tanko.
Cikin zafin rai ya ce“Laraba na rantse da Allah idan kika kasowa Ibtisam aurenta aranar zan sakeki karki ce ban gayamaki ba, kiji kuma tsoron Allah adukkan lamarunki, wlh idan kika tunzura yarinyar nan tai abinda Ja'afar ya saketa bani ba ita bake ke na yafe wlh wlh wlh kinji na rantse sau uku na fita daga rayuwarku har abadan idan kinaga barazana nake bismillah Laraba zaki san waye Shamsuddin. ke agidan uban wa kika ta'ba ganin anyi hakan? Kinada miji kice kina son wani? Wanin wanda mafarkinki ma bazai kai can ba, ke ko tsoron Allah bakyaji Ni za ki wulaqanta? Wato duk bayanin da aka miki baki gamsu ba?â€
Ibtisam ta shiga gorgiza kanta tana kuka tana ha'de hannayenta.
Laraba sosai tsoron ganin yadda Tanko ya koma lokaci 'kalilan.
Masifa yake sosai kamar ya Ari baki yana 'Kara musu kashedi, daga 'karshe ya ce“Ku tashi Ku ban waje idan kunga dama kuci abinci idan baku ganiba ku kuka sani ke Ibtisam daga nan har mutafi karki sake shigomin 'daki ki zauna wajan mijinki.â€
Cikin rawar baki ta amsa da“Toh Baba.â€
Suka fice sumi-sumi.

Zaune Abie yake saman sofa ya lume yana waya murmushi 'dauke saman kyakkyawar fuskar shi.
Yana sanye da wani yadi mai shegen kyau da tsada fari 'kal, 'dinki ya amshe kyakkyawan jikinsa.
“No! Ummiterh wlh sam yau ban zauna ba, yanzu haka hospital zamuje nayi waya da Dr za'a duba yarinyar, koda Baby ban samu nayi waya ba naga kiranta nasan akwai rigima yau ni da ita.â€
Abie ya 'karashe mgnar yana 'yar dariya ya beqa hannunsa ya 'dauki cup glass me 'dauke da coffee zai kai bakinsa karaf idanunsa suka sauka akan Ibtisam da ta qureshi da idanunta tana matsar 'kwala tana goge gefen bakinta yana fitar da jini.
Idanunsa ya janye yana mamkin yawan kallon yarinya.
Kur'ba coffee 'din yay, wanda yay daidai da isowar Laraba ta zube tana gaishe sa.
Amsawa yay yana miqewa ya ce.
Me ya samu bakin Ibtisam yana jini?
Kuci abinci sai mutafi hospital. â€
Ya 'karashe mgnar yana qoqarin barin wajan.
Ibtisam cikin janyo numfashi ta gaishe sa bai waiwayo ba ya amsa yana fa'din.
“Kici abinci sosai kinji?â€
Cikin gaggawa ta amsa da “Toh insha Allah.â€
Tanko ya iso ya zauna yana binsu da harara ya ce.
“Zaman me kuke da bazaku je kuci abinci ba?â€
Miqewa sukayi suka nufi kan dining area.
Ja'afar zaune yake sanye da 'kananun kaya wanda suka masa masifar kyau, sun bayyana kaykkayawan jikinsa wanda yake mummur'de, gashinsa luf kwance baqi qirin, sai wani irin 'kamshi yake.
Laraba ta zabga masa harara ba wanda ya masa mgna suka ja kujera suka zauna.
aladabce ya gaishe da Laraba.
Ciki² ta amsa.
Ai kuwa sun kasa bu'de kulolin abincin sai kiciniyar sukeyi.
Ja'afar dariya kamar zata kasheshi ya danneta ya miqe ya bu'de musu yabar wajan baki 'daya dan suci abinci anutse.
Laraba ta ce“Ko ance masa bazamu iyaba ne.â€
Ibtisam ta kicin-kicin da fuska batace komai ba.
Abie yana shiga ciki ya kira Rahma.
Bugu 'daya ta 'daga kiran.
Kuka ta sanya masa tana kiran.
“Abienah!â€
Kwanciya yay saman sofar bedroom 'dinsa yana dafe goshinsa yana lumshe idanunsa. Ahankali ya amsa.
“Na'am Babyna! Pls yi hkr zan miki bayanin abinda yasa ban samu 'daukar kiran ki ba tin yamma, barmin asaran hawayenki masu daraja.â€
Daga can Rahma tana kwance tsakiyar gadonta ta lullu'be dukkan jikinta da tattausan bargo, yana fitar da 'kamshi idanunta arufe ruf tana shasheqar kukan sannu ahankali.
Abie ya ce“Babyna! Kina son tayar min da hankali ko? Wlh kina maqale acikin zuciyata, ban zauna bane, kinsan da zaran na kasance a'kasar nan banda wani sukuni an dameni da meeting da sauran abubuwa.
Yi hkr pls kinci abinci ummina?â€
Daga can ta langwa'be kai ashagwa'be ta ce“Eh ka'dan bana jin yuwa kewarka ta dameni Abienah.â€
Murmushi mai sanyi ya mata ya ce“Wlh nima Babyna so ki daure ki ha'da ko tea me kauri sai kici ko cake ne OK babyn Abienta?â€
Cikin cika umarninsa ta ce“Ok rabin raina an gama amman ni dai Abie kazo wlh bazan iya jarabawar nan ba cikin nutsuwa idan ban sanyaka idanuna ba.â€
Ta 'karashe mgnar kamar tana son sanya kuka.
“Ya Salam! Baby ki nutsu pls ai mun gama mgna zanzo don Allah gobe ki shiga aji cikin nutsuwa ki 'dauka abinki na wajan zaune yana kallonki kina zana jarabawarki OK? â€
Cikin farin ciki ta amsa da “Ok Abiena ina sonka, ina jiranka.â€
Murmushi yay ya ce“Ok je maza kiyi abinda na sakaki idan mun dawo zan kira video call naga cikin babyna idan yaci abinci.â€
Sallama sukayi cikin farin ciki.
Chapter 52 · 0% Book details