← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 118

Sashe 57

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acan Espanol
Rahma suna shigowa gidan saman sofa ta zube, tana maida numfashi ta runtse kyawawan 'kananun idanunta, zuciyarta babu da'di bata jure fushin Abienta.
Meerah tazo tana musu sannu da zuwa, ta ce“Madam Rahma akwo miki koda tea ne me kauri kisha kafin kiyi wanka kuyi sallah na jera abinci a dining? â€
'Kananun idanunta ta bu'de ta girgiza kanta “No! Meerah ki barshi ngd.â€
Anee ta ce“Wlh baki isa ba Meerah kawo mata tea me kauri.â€
Meerah ta ce“Toh an gama wlh bata son cin abinci.â€
Anee ta kamo hannayen Rahma ta 'kura mata idanu ta ce“Haba! Rahma me ya yi zafi haka? Tinda aka kiraki awaya kika canza duk bakida nutsuwa da sukuni meke faruwa? Ko Rafeek ne bakya so har haka?â€
Rahma ta sadda kanta ta ce“A'a Abie nah ne, fushi yake dani, sbd yaji Rafeek ya kirani da Baby cute nafi zargin hakan.â€
Sam batajin da'di Abienta na fushi da ita ba.
Anee ta gane Rahma ba qara min so takewa Abienta ba bata iya samun nutsuwa
Idan Abien na fushi da ita.
Anee ta rungumeta tsam tana lallashinta, ta ce“Karki damu Abienki na sonki bazai ta'ba cutar da ke ba, tinda har ya ce miki idan kinada mijin idan bai miki ba zai rabaku ki auri wanda kikeso ai ba matsala yanzu zan fahimtar da Rafeek akan mgnarku ya yi hkr zuwa wani lokacin.â€
Rahma ta girgiza kanta, “A'a Anee wlh koda ace wanda yafi kowa tsufa aduniya ya kasance makaho kurma Abie ya auramin zan zauna da shi na masa biyayya har 'karshen rayuwarmu, bazan iya bijirewa Abiena ba, kinsan 'kaunar da nake masa? Wallahi bana fatan na ba'kanta masa rai sam bana iya jure fushinsa akaina, kawai Rafeek yay hkr Allah ya basa wacce ta fini.â€
Ta 'karashe mgnar cikin shasheqar kuka. Dan tana sonsa ba yadda zatayi ne shiyasa take baya² da lamarinsa.
Anee ta rungumeta tsam tana jin tausayinta da na Rafeek sbd tasan ba qara min so yake ma Rahma ba.
Meerah ta kawo tea 'din Anee ta sakata ta sha sai da ta shanye tass tana ha'da zufa.
Wanka ta shiga tana fitowa ana kiran sallar Maghreb tare da Anee sukayi sallah, suna kammalawa bayan sunyi azkhar suka fito falon.
Meerah tai serving 'dinsu.
Rahma bai fi spoon 3 ba ta yi ta ajiye spoon tana 'daukar cup glass wanda Meerah ta cika mata da lemon zallar strawberry sai ra'ba cup 'din yake tsabar sanyi, ta kafa bakinta sai da ta shanye, ta ajiye tana 'daukar wayanta ta latsa lumber Abie.
Ta gaji da ringing ba'a 'daga ba.
Goshinta ta dafe tana sauke numfashi.
Anee ta cika cikinta dam suka dawo falon, ganin yanayinta ya sanya Anee ta shiga bata labari me da'di sai da ta 'dan sake jikinta kadin Anee ta ce “Muje ki saka direba ya mayar dani gida.â€
Rahma ta marerece ta ce“Please mu kwana gobe sai mu wuce school. â€
Anee ta maqale kafa'da ta ce“Wlh bazan kwana ba haka kawai kinsan Ya Zahara da fa'da muje kawai asaukeni.â€
Rahma ba yanda ta iya ta raka Anee har gida suka jiyo.
Abie 2 Rahma ta kira suka Sha fira tana tambayarsa jikin Raiyana ya bata labari, amman bai ce ita ce ta musu asirin ba, ya dai ce mata ta warke ta kirata ta mata barka.
Rahma cikin farin ciki ta Kira Raiyana.
*Chad*
Zaune suke a falon Raiyana ta ra'be dan ko ta saka baki a hira Jaddatu ajiye hira take ta 'dauko wata.
Jin ringing wayarta ya saka ta duba ganin lumbar ba suna ta 'daga tare da sallama.
Rahma ta amsa tana fa'din.
“Ammie barka da arziqi Ashe kin warke?â€
Raiyana ta saki kuka tana fa'din.
“Ummi qarama ki yafemin dan Allah ki gafarceni wlh na tuba zan riqeqi da amana ki tayani roqon Abienki karma ya rabu dani.â€
Rahma ta ce“Subahanallahi! Haba! Ammi ni wlh baki min komai ba! Kuma idan ma kin min toh na yafe miki, Abie kuwa insha Allah kuna tare bazai sakeki ba! Toh me kika masa ma? Bari zan kirasa ki daina kuka dan Allah.â€
Raiyana sosai taji sanyi aranta ta share hawayenta ta ce“Ngd sosai Allah ya miki albarka.â€
Rahma ta amsa da“Ameen ammi ki gaishe da kowa sai anjima.â€
Jaddatu bata ma kalli inda take ba Hanan ce take bata hkr akan ta daina yawan kukan 'yan aiki na jinta.
Jaddatu ta ce“Ta baya ga wasa kenan.
Ai gaban 'yan aikin baqaqen aljanun suka fa'di munanan aikinta wannan me zai dameta dan sunji kukanta tana Neman gafara wajan wa'danda ta cutawa...â€

Abie 2 bayan sun kammala cin abinci dare ya kira Abie 1 lokacin ya raka baqin da yay suna bakin gate bai 'daga kiran ba sai da suka tafi.
Da sallama ya fara.
Abie 2 ya amsa ha'de da gyaran murya ya ce“Abdulmajid! fatan kuna lfy ya me jikin?â€
Abie wajan wasu fararen kujeru ya isa ya zauna yana amsawa da.
“Lfy lau Alhmdllah ya kowa na gidan? Gobe insha Allah suke shigowa amman ni sai jibi zan biya wajan Ummi.â€
Abie 2 ya ce“Masha Allah! Abdulmajid kayi hkr dan Allah ka sassautama matarka tayi nadama naga tana son zama dakai fiye da komai arayuwarta.â€
Abie ya numfasa ya ce“Toh har na dawo zamuyi mgna insha Allah. â€
Hira suka ta'ba sukayi sallama.
Yana dates kiran kiran Rahma ya shigo.
'Dagawa yay tare da sallama.
Ashgwa'be ta amsa ta kirasa.
“Abie Rabin raina idan na 'bata maka rai ka yafemin ko na samu sassauci azuciyata.â€
Abie yay murmushi ya ce“Uhmm! Baby cute ko? No! Baki 'batamin raiba amman zamuyi mgna idan na iso gobe oya ki kwanta da wuri kinga tin sassafe kike tafiya school. Fatan kinci abinci?â€
Shasheqar kukanta yaji cikin kunnensa.
Idanunsa ya lumshe yana shafa sumar kansa ya furta.
“Ya ilahi! Babyna mene um?â€
Cikin kuka ta ce“Daman nasan kaji shine duk ka bi ka tayar da hankalinka ka tayar min da hankalina, Sam banida walwala banida sukuni komai baya min da'di sakammakon Abiena na fishi dani, ya hana kasan nutsuwa ya hanani.â€
Ta 'karashe mgnar cikim shasheqar kuka.
“Am Babyna kina jina?
Kai ta 'daga kamar yana ganinta.
“Yauwa kiyi shiru maza kije kici ka cikinki dam da abinci ki Sha ruwa ko lemo me sanyi ki nutsu na hkr na daina fushin gobe idan nazo zamuyi mgna OK baby love? â€
Ashagwa'be ta ce“Toh Abie kace ka yafemin, sannan kamin murmushi kace min baby Ummi I love you. â€
Abie dariya ta 'kwace masa harda riqe cikinsa yana 'kyal'kyala dariya.
Rahma kuka ta sakar masa yanajin sautin yadda take buga 'kafafunta 'kasa.
Cikin dariya ya ce “Ok..OK! Babyna zan fa'da na yafe miki I love you baby ummina ruhina.â€
Yadda ya fa'dan ya saka Rahma jin wani irin yanayi tin daga 'dan yatsar 'kafarta zuwa tsakiyar kanta, idanunta ta lumshe ta qamqame jikinta waje 'daya tana sauke ajiyar zuciya wadda sautinta ke fita da 'karfi yana ratsa dodon kunnen Abie ta waya.
Asanyaye ta ce“I love you too Abienah Rabin raina, yauwa sai mgnar ammi nah.â€
“No! Babyna sai nazo zamuyi yanzu ina busy good night ki ci abinci OK? â€
Kai ta jinjina tare da amsawa“Toh Abienah.â€
Kiran ya dates yana sakin lallausan murmushi.

Musalin 11 Ja'afar zaune gefen bed yana waya dasu Harisu cikin nisha'di yana gayamu su gobe zasu taso.
Ibtisam sai turo baki take wai ya hanata bacci.
Bayan ya gama yay shirin bacci ya hauro gadon ya rage hasken 'dakin ya kwanta, ya matso jikinta ya sanya hannayensa ya zagaye 'kugunta ya tura fuskarshi tsakanin wuyanta yana jujjuyawa ya Kira sunanta cikin wata irin murya.
'Kam'kame jikinta tai tana sauke ajiyar zuciya.
Murmushi yay bai mata komai bakinsu kawai ya ha'de yana mata wani irin fitinannan kissing wanda ya zautar da ita ta rungumeshi 'Kam tana maida masa martani, har bacci ya 'dauke su.

Washegari cikin shirin tafiya suka ta shi, Abie ya saka an zagaya gari dasu sunyi kalle² laraba idanunta kamar xasu fa'do waje sayayya sosai Abie ya musu yana taka tsantsa da Ibtisam sbd yadda take qoqarin shige masa shiyasa wajan siyayyar yaqi shiga wajan yana mota Pa 'din Abie ne yake biye dasu.
Tanko ganin irin ku'din da Abie ya kashe musu harda kuka ya riqe 'kafarsa yana masa godiya.
Misalin 'karfe 1 na rana jirginsu Ja'afar ya 'daga zuwa Chad Abie shi kuma nasu 2 na Rana ya 'daga Australia.

Espagne
Rahma yau ta ci sa'a 'karfe 3:30 na yamma suka dawo daga school.
Murna ta hanata zaune ta hanata tsaye, da kanta tinda tai sallar la'asar ta shiga ma Abienta girkin da ta San yana so fiye da sauran abinci.
Sai da ta kamamla komai Meerah ta shiyar kan dining area ta shiga wanka.
Bayan ta yi sallar Maghreb Wata irin kwalliya ta cancara wuyanta da kunnen and hannunta ta zuba gold haka yau ta canza sarqar 'kafarta ta saka ta diamond har tafi waccan kyau da tsari.
Riga da wando na Pakistan ta saka maroon sunyi mata masifar kyau wani irin 'kamshi take na ban mamaki, ta tufqe gashinta ta Saki jelar har gadon bayanta, ta yafa mayafin kayan.
Meerah kanta da take mace ta yaba kyan da Rahma tai da tsarin surata, sosai take mamakin tsantsar 'kaunar da Rahma takewa mahaifinta kamar dai saurinyata ko mijinta irin wannan girkin da 'daukar wanka.
Zaune take tana duba lokaci.
Zabura tai ta ce“Wayyo na makara zuwa airport maybe muje kusan tare, Meerah na tafi sai na dawo.â€
Ta 'karashe mgnar tana tafiya abinda taji a Tv yasa tai saurin dawowa baya ta qurama Tv 'kananun idanunta masu matuqar haske da kyau tana kallon labarun da ake, cikinta taji ya hautsuna zuciyarta tai wata irin bugawa lokaci 'daya taji duniyar na juya mata idanunta suna lumshewa kafin ta fahimci sauran bayani ta sulale nan 'kasa sumammiya...

_💃ðŸ»'Yar Ajin Ma Sha Allah🥰_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/12/22, 00:27 - Buhainat: ```D A```

```57&58```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_
Chapter 57 · 0% Book details