← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 118

Sashe 91

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rayyana kuwa tinda su Abie suka barta, ta zube wajan bakinta na fitar da jini, sai biegima take, tana bori sai sambatu take tana fa'din.
“Wallahi Abdulmajid ban sakuba, shin wai ya akayi naji yana cewa matarsa? Agidan uban wa uba ya ta'ba auren 'yarsa..? Kan buro uba wallahi ba'a isa ba, duk duniya ba mai rabani da mijina, wlh ban sakuba, Saki uku lokaci guda azaman Saki guda yake, dolene ka maidani 'dakina naci uwar shegiyar munafukar yarinyar nan, daman can shiyasa bana sonta sabida ina kallon idanunta naga tana ruwan karuwai munafukai, wayyo Allah na!! Jama'ah kuzo an sakeni Saki uku wlh bazan bar gidan nan ba akan karuwa...â€
Meerah ce taji ihun da kukan daga can ta bu'de 'kofa ta fito, ta sauko gudu sauri² ta iso wajan Rayyana tana fa'din.
“Subahanallahi! Auntie me ya faru?â€
Tana qoqarin Kama Rayyana.
Cikin zafin nama ta miqe ta wanke Meerah da mari ta ce“Uban babanki ya faru shegiya munafuka, sai naci uwarku keda munafukar karuwan uwar gidanki...â€
Latifa da Ummun Adnan ne suka iso suna fa'din.
Haba! Auntie me kikeyi hakan?â€
Takalmin 'kafarta ta cire ta jefa musu tana kuka ta ce“Karku ta'bani ni wallahi duk na tsaneku ace duk kuna gidan nan bakusan me akeba? Abie da Rahma suna iskanci bakuda labari dan na kamasu ya sakeni Saki uku wlh ban sakuba ina sonsa...â€
Latifa ta ce“Au sharrin da za ki k'ulla musu sbd ya sakeki? Ai wlh yamun daidai dan nasan ba kin tuba dan Allah bane...â€
Rayyana ta ce“Ke! 'Yar aiki zanci ubanki ki tsaya a matsayanki na 'yar aiki nan ba huruminki bane.â€
Bugo ta kaima Latifa, Latifa ta tare ta 'dauketa da mari ta hanka'data ta ce“Ai tinda Yalla'bai ya cika aiki alqur'an ba sassauci Ummun Adnan kuka mata mufitar da alqaqai wa za ki buga? Tab ni wlh sai muyi damben mutuwa ban tsoronki, Meerah shiga 'dakinta na da 'dauko hijabi mu cika aikin oga sbd nasan bazata fita da 'kafarta ba.â€
Aikuwa Rayyana na ihu Latifa ta riqe 'kafafunta sabida shegen 'karfine da ita.
Ummun Adnan da Meerah suka Kama hannayenta tana ihu suka 'dagata sama suka nufo 'kasa da ita.
Jaddatu da Hanan tsaye suna kallon hanyar bene.
Jaddatu ganin su Latifa da Rayyana kamar sun 'dauko kayan wanki, Jaddatu ta ce“Lah! Me nake gani ni Rahmatu? Latifa meyake faruwa?â€
Latifa suna tafiya ta ce“Oga ya ce“Muje mu fito da ita mu rakata har filin gidan, wai ya koreta taqi tafiya.â€
Jaddatu ta ce“Kai Masha Allah Abu ya yi kyau, wani mugun abun ta shuka musu asaman ko?
Rayyana kan atafi bari kiji Rahma matar Abdul ce ba 'yarsa ba ayau zan saka ranan tarewansu, muguwa azzaluma kinso 'bullo mana ruwa Allah ya jiqanmu, Aqara gaba abarmin yarana su hutu yanzu lokacin hutunsu ne ya 'dauki abarsa su tafi yawon bu'de idanu, agaishemin da dandab'asa duk da ita ba irinki bace.â€

Rayyana ihu take tana kuka ta ce“Allah ya isana kun ha'inceni ban yafeba...â€
Latifa ta buge mata baki suka jata suka fice da ita tana ihu.
Hanan ta girgiza kanta ta ce“Allah kyauta wane wulaqanci yafi wannan? Rayyana banso kukayi rabuwar rashin arziqi da Ya Abdul ba.â€
Jaddatu ta ce“Yo ai ba 'diyar arziqin bace, dole anuna 'dan hali muje muyi kwanciyarmu kan abin kari ya kammala.â€

Komawarsu 'daki daman ihun ya tashe su.
Duk nisan gate sai da suka kaita har bakin gate suka ajiyeta suka juyawarsu.
Rayyana irin kallon da taga Ana mata yasa ta fice daga gidan tana kuka.

Abie 2 na zaune ya zubama qofar falon idanu, su Abie suka shigo da sallama.
Abie ya amsa yana hawaye ya warema Rahma hannayensa.
Hannun Abie ta matse tana kallonsa ta ce“Abienah naje wajan Abie2 ? Me ya samesa yake kuka?â€
Abie ya matsa hannunta sosai cikin nashi, ya mata ra'da akunnenta.
“My Baby my heart eh jeki, shi ne yayan Ummul Aymana, congratulation my baby naji da'din samun jinin mahaifiyarki zaku rayu tare.â€
Rahma ta qamqame Abie ta ce“Ngd ngd ngd Rabin raina.â€
Ta sakeshi ta fashe da kuka da gudu ta nufi wajan Abie2.
Jikinsa ta fa'da ta 'kam'kameshi tana kuka, ta ce“Allah sarki Abie2 nah ashe dai Abien nawane, Alhmdllh! Allah na godema zan rayu da jinin mahaifiyata, Abie2 ina sonka don Allah ka kasance tare da mu har abdan bazan barka ka koma Iran ba bare akashemin kai. Naso na rayu da ummata nasan macace me kirki zata riritani zan mata shagwa'ba zan dinga tsokanarta na zubawa da gudu tana bina tana ku kamomin ita yarinyar nan batajin magana fa! Wlh ina son ummina ina son Abbana ina son Mustapah, ina son Abienah amman son Abienah ayanzu na daban ne duk son da nake musu na ha'damasa shine kowa nawa sai yanzu da na sameka Abie2, kai zan ba rabin 'kaunar Abienah.â€
Abie2 shima kukan yake ya rungumeta ya ce“Nima bazan tafi ba 'diyar albarka muna tare insha Allah, Abienki shine uwarmu shine ubanmu dole ki masa son so amman ai shine mahaifinki ko.â€
Abie zama yay gefensa ya tallafe kumatunsa da tafukan hannunsa ya zuba musu idanu yana kallonsu kamar Tv, bai hanasu kukan su ba sunata sambatunsu.
Rahma ta basa dariya sabida ta kasa amsa tambayar da Abie 2 ya mata.
Numfashi yaja yay gyaran murya ya ce.
“Toh dai kukan ya isa haka pls ai Baby bazata amsa maka tambaya ba, bari na baka tarihin ha'duwata da Ummul Aymana...â€
Abie nan ya tsakura masa labarin Aymana na ha'duwarsu da soyayyarsu da sadaukarwa da yama Aliyu zuwa haihuwar Rahma da basa ita da sukayi da 'daura aurensu da Abbu yay da kashe shi da Naja'atu tai, da dalilin zuwansa nan.
Abie2 ya ce“Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Abdul Majeed sannu kai kam na daban Allah ya halicce ka acikin mutane, wlh bansan Kalmar da zan gayamaka ba, komai ka wuce akiraka tsakanina da kai kawai nayi ta maka addu'a da fatan alkahir har numfashina yabar gangar jikina, ban ta'ba murna da farin ciki ba irin na yau naji da'din 'diyar albarka matarka ce ba namijin da ya cancanta ya zauna da ita matsayin mijinta sai kai, kaine uwata Kaine babanta yayanta 'kawarta komai nata.â€
Abie ya murmusa yana jinjina kansa, ya kamo hannun Rahma ya zare wayarsa cikin hannunta, yana latsawa.
Rahma ta kalleshi ta kalli Abie2.
Abie2 Yay murmushi ya ce.
'Diyar albarka 'dagani na wanko fuskaâ€
Rahma janye daga jikin Abie2 tana goge fuskarta.
Hanyar bedroom ya nufa.
Kallon Abie tai yana waya.
“Hello yauwa a ha'doma komai na breakfast akawo mana 'bangaran Abie2.â€
Katse kiran yay, ya danna number Abby morocco.
Ringing biyu aka 'daga.
Da hannu ya yafito Rahma yana 'daga mata gira, yana mata nuni tazo kusansa.
Kanta ta kauda ta 'daga kafa'da ta ce“Naqi awajan babana nake.â€

'Yar dariya yay yana kallonta cike da so ya fara amsa wayar.
“Hello Abby! Baku taso ba?â€
Daga can Abby ya amsa da.
“Ai jirginmu sai 10 na safe zai taso insha Allahu, ina rigiman manka?â€
Abie ya ce“Gatanan ta ha'du da babanta ta shareni ina kiranta.â€
Yanayin da ya yi mgna ya sanya Rahma juyowa ta kalleshi tana girgiza kanta.
Abby yay dariya ya ce“Wani uban kuma?
Abie ya ce“Wlh dattijon da yake gidana ashe yayan Ummu Aymana ne, daman najima ina zargin hakan ban dai tabbatar bane.â€
Abby ya ce“Masha Allah naji da'di yarinyar mu ta sake samun gata.â€
Sunyi 'Yar hira yaba Rahma wayan akunyace yau ta gaisa da Abby ba kamar daba, har yana tsokanarta.

Abie2 na fitowa Latifa na shigowa da 'katon tray shaqe da kayan breakfast, da sallama.
Leda ta shimfida saman carpet ta ajiye tray'n atsakiya ta gaishe da Abie2.
Abie ya ce“Yauwa Latifa fatan kunyi aikin da na baku?â€
Cike da ladabi ta ce.
“Eh Yalla'bai ai tin yaushe har 'kofar gate muka kaita.â€
Abie ya jinjina kansa ya ce“Masha Allah Ngd tashi kije.â€
Rahma da kallo take bin Latifa har fita.
Abie ya ce“Baby sakko mu karya, ha'dama.â€
Baki ta zumb'uro ta sauko kusan Abie2 ta zauna ta ce“Abie2 kaga Abie ya saka na kori ammi ai bai kyauta ba ko?â€
Kallonta Abie 2 ya yi cike da mamaki ya kalli Abie wanda ya zubama Rahma idanu yana mata kallon mamaki.
Abie2 ya ce“A'a baka kyauta ba me ta yi?â€
Abie ya harari Rahma ya ce“Uhmm! Wlh kashemin ita ta kusa na isko ta shaqeta da bana kusa ai shikenan.â€
Abie2 ya ce“Subahanallahi bata kyauta ba.â€
Rahma ta ha'da musu tea me kauri ta zuba musu farfesun kan rago kubus gefe ga soyayan dankalin turawa normal ba kwai.
Akunyace take ci sabida kallon da Abie yake mata.
Chapter 91 · 0% Book details