← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 118

Sashe 8

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdul Majeed ya zubawa 'yar tasa narkakkun idanunsa, ya saki wani irin guntin smile, ahankali ya tako zuwa dab da ita, wanda fitinannan k'amshinsa ya buwayi hancinta.
Tattausan hannunsa ya sanya ya janye mata dogon gashinta,wanda ya rufe mata kusan dukkan fuskarta, ya d'an rankwafo ya lek'o fuskarta, yana sakin smile.
idanunsa akanta ya kusanto fuskarshi dab da tata, har suna jin hucin junansu atausashe ya kirata “Baby ummina! Oya zo naji me Abien ya yi um? D'ago mana baby ummiterh.â€
Jin muryasa dab da kunnenta daddad'an k'amshin da yake fitowa daga bakinsa, ya mamaye mata dukkan k'ofofin hancinta.
Dad'in k'amshin ya sanyata jan wani irin wahalallan numfashi, wanda taji lokaci d'aya yana qoqarin barin gangar jikinta. Da iya kacin k'arfinta take janyo numfashinta da yake son tsaya iyakacin k'arfinsa.
Hakan ya sanya zuciyarta wani irin matsanecin rauni, wanda ya janyo zuciyar ta fara bugu da dukkan iya k'arfinta, jikinta ya fara wani irin b'ari, yayin da wani irin fitinannan sanyi ya kawoma dukkan illahirin jikinta farmaki, lokaci d'aya, sanyi ya fara bin gab'ob'in jikinta, da dukkan wata k'ofar mahudar gashin jikinta, sannan tin daga cikin tafin k'afarta zuwa har k'wak'waluwarta, sanyin yake ratsa.
Abienta ya ce“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ummina! Bakida lafiya ne?â€
Ya k'arashe maganar ya janyota cikin jikinsa ya rungumeta k'am-k'am, ya d'ago fuskarta yana shafawa yana hura mata d'umamanmiyar iskar bakinsa mai fitar da wani irin d'umi had'e da k'amshi marar misali.
Numfashinta da yake barazanar tsayawa ta fizgo da k'arfin gaske tana sanya dukkan hannayenta ta zagaye bayansa, ta fashe da wani irin rikitaccan kuka, cikin fizgo numfashi ta kirasa.
“Abiena zan sha ruwa mai d'umi.†ta k'arashe mgnar cikin shashek'ar kuka.
Abdul Majeed ya rikice yana famar buga bayanta ya ce“Ya Ilahi! Baby wai me na miki? ji yadda zuciyarki take bugawa. Ok naji muje na had'a miki tea me zafi, don Allah ki daina min kuka zo kiji yadda zuciyana ke bugun uku².â€
Ya k'arashe mganr yana kamo lallausan hannunta ya d'ora tsakiyar faffad'an k'irjinshi.
Rahma jin yadda zuciyar Abienta yake bugawa iya k'arfinta, ya sanyata tattaro nutsuwa ta k'arfi ta fara shafa k'irjin nasa ta tura kanta tsakiyar k'irjin nasa, tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, ta kira shi asanyaye.
“Abiena!â€
Ya amsa da “Na'am zuciyar Abienta! ke d'aya k'wal ubangiji ya mallaka min aduniya, banga anfanina ba idan har zan barki acikin damuwa.â€
Ya k'arashe maganar ya na d'aukarta cad'ak kamar baby ya juya ya fara taka matattakalar benin.
Rahma ta had'iye kukanta sbd kalamansa sun saka mata tausayinta, ta tura kanta tsakiyar k'irjin Abienta tana sauke ajiyar zuciya, ajere².
K'asa ya sauko da ita ya zaunarta saman kujera, ya manna mata kiss saman kumatunta, yaje ya kunno fitilun falon masu haske, ya shige kitchen.
Rahma ganin bai dace tabar mahaifinta ya yi mata aiki ba ya sanya ta mik'e cikin sauran d'an kuzarinta da ya rage mata ta iskosa kitchen.
Ashagwab'e ta ce“Abiena kawo na had'a.â€
“No! Ummina!â€
Kai ta d'ago ta kalle shi tana kwab'e fuska, gira ya d'aga mata yana sakar mata lallausan murmushi.
Itama murmushin yak'e tai dan ta rasa abinda yake damunta, bayan abinda Raiyana tai wa mahaifinta tabbas akwai damuwar da ta kasa gano meye.
Tayi nisa cikin tunani taji tattausan hannun Abienta ya rik'e nata yana janta tare da fad'in.
Muje naji me ke damun ummina.â€
Zaunar da ita yay ya zauna dab da ita, yana hura mata had'add'an tea d'in da ya mata da bakinsa.
K'ananun kyawawan idanunta ta zuba masa, tana sanya yatsarta aramun dimple d'insa, wanda yake lob'awa, sbd yadda ya dage yana hura mata tea d'in da Iskar bakinsa yana murmushi, ya ce“ Oya zo ki sha.â€
Ya k'arashe mgnar ya na tallafo gefen fuskarta, ya kafa mata cup a mitsitsin bakinta.
Marerece fuska tai tana kallonsa.
Fuska ya had'e ya ce
“Oya.â€
Luf ta lab'e ajikinsa ta lumshe k'ananun fararen idanunta tana shan tea d'in, cike da nutsuwa da kwanciyar hankalin da ta samu ayanzu², wanda take ta tafi duniyar tunanin abun da batasan meye shi ba.
Dariyar Abienta ta dawo da ita daga duniyar tunanin.
Kyawawan k'ananun idanunta ta bud'e ta tsurama kyakkyawar fuskar Abienta ido yadda yake mata dariya yana rik'e da fuskarta, ya nuna mata cup d'in vide ma'ana ba komai, ya shanye tea d'in amman sai famar rik'e hannunsa take tana kai cup d'in bakinta.
Fuska ta kwab'e tana tura yatsarta a ramin dimple d'insa, tana matsar k'ananun lumsassun idanunta.
“Sorry mah baby ummina muje ki kwanta, yau busy nayi dayawa ba shareki nayi ba kinji bugun zuciyata ummina.â€
Rahma ta zumb'uro k'aramin bakinta gaba, cikin sanyita da rauninta akan Abien ta ce“Abiena! Ko kirana baka d'aga ba fa! Ga shi gobe zaka tafi tsawon kwanaki ban ganka ba Abiena!â€
Ta k'arashe mgnar cike da rauni wanda ya bayyana qarara akan kyakkyawar fuskarta, har k'walla sun fara taruwa, tai saurin mayar da k'wallar, ta daure batayi kukan ba!
Wani irin wahaltaccan numfashi ya janyo da k'arfi, ya feso da iskarsa waje, saman fuskarta, tare da shafa fuskarta a raunace cike da tausayin 'yarsa d'aya tilo kamar tsoka d'aya acikin miya, ya ce “Afuwan Baby ummiterh zanyi qoqarin dawowa akan lokaci domin na baki dukkan kulawar uwa da uba suke bawa d'ansu,na ji dake na tarairaye ki na baki lokacina fiye da kowa har sai hutunki ya qare kin koma Espagne, oya muje ki kwanta kinji Babyn Abienta.â€
Cike da rauni ta jinjina kanta tana janye jikinta.
Kama lallausan hannunta yay suka nufi wajan kashe makullan fitulun falon wanda k'wayayen sun kai guda 12 kala² hannunta ya sanya saman ma kashin fitulun ya danna yatsotsinta falon ya gauraye da duhu, yay murmushi k'asa² ya ce“Oya dodo Kama ummina...â€
D'an guntun qara tai ta fad'a jikinsa ta k'ank'anme shi cike da zallar shagwab'a ta ce“A'a fa dodo oya tafi sha'aninka Baby na tare da Abienta ba wani abin cutarwa da zai iya cutar da ita.â€
Ta k'arashe mgnar tana murmushi.
Ba sake mgna ba yay murmushi ya kunna fitilun haske ya bayyana, janyeta jikinsa ya kama hannunta suka nufi sama.
Ak'ofarta ya saki hannunta ya mata kiss agoshi ya ce“Oya ummina bacci mai dad'i ki kasance cikin amincin Allah har zuwa wayewar gari.â€
Ya k'arashe mgnar ya d'auki wayoyinsa da system d'insa.
Rahma ta ce“Abiena kaima ka kasance cikin duk abinda ka lissafomin fiye da hakan, I love u Abiena bye.â€
Ta d'aga masa hannu tana shigewa ciki ta murzawa k'ofar key.
Juyawa yay ya fara tafiya wani irin sihirtaccan murmushi d'auke akan fuskarshi.
Yana saukowa daidai k'ofar d'akin Raiyana yaji motsi, hakan bai saka shi waigawa ba, ya gifta ya ji muryan Raiyana, tana kiransa.
“Abien Ummi inada mgna.â€
Waigowa yay ya fad'ad'a murmushin fuskarshi, ya ce“Ok inajiâ€
K'arasowa tai tana danne mugun haushinsa da takeji, ta marere fuskarta kalar tausayi, ta ce“Sbd Allah tin yaushe wajan Ummi kake? amman ni kuma kamar ba matarka ba? Gsky gatan da kakewa...â€
Da sauri ta had'iye abinda zata fad'a ta waske ta gyara kalamanta ta ce“Allah ya qara maka lfy ya barma kai nida Ummi babba da Ummi 'yar lelen Abdul Majeed, kana son 'yar dayawa gaskiya, nima Allah ya bani haihuwa da kai.â€
Ta k'arashe maganar tana qoqarin rungumeshi.
Bai hanataba ta wani shige jikinsa ta k'ank'ameshi tana shak'ar daddad'an ni'imataccan turarensa, wanda ya gauraye da turaren Rahma.
Can k'asa ya ce“Hankalinki ya kwanta? sakeni toh, Sam bakida kunya har kin manta tijaran da kika min?â€
Ya k'arashe mgnar yana zamewa ya juya ya nufi bedroom d'insa.
Raiyana sororo ta tsaya tana kallonsa har ya shiga ya rufo k'ofa.
“Hummm Abdul Majeed zaka shigo hannune da izinin Allah.â€
Ta fad'a tana shigewa ciki.
Rahma kai tsaye saman bed ta fad'a ta shige wani irin lallausan bargo mai fitar da sihirtaccan k'amshi,ta rungume k'atuwar Teddy d'inta, tana mai karanto addu'o'in bacci.
Minti 7 bata cike ba wani irin dadd'an bacci yay awon gaba da ita.
Abdul Majeed yana shiga, shirin bacci yay ya shirya cikin wasu kayan bacci masu masifar kyau da laushi, ya kashe dukkan wayoyinsa yabi lafiya royal bed d'insa, bakinsa bai daina karanto addu'a ba har bacci ya d'auke shi mai cike da nutsuwa.

*Washegari.*
Niger Diffa

K'arfe 5 saura na asuba bus d'insu Ja'afar ta cira daga garin damagaram zuwa Diffa.
Tafiya ta tsawon 7 hours sukayi acikin bus, kafin su iso garin Diffa.
Suna sauka daga gidan bus suka shige rumfuna da aka tanada dan bak'i, suka zazzauna bayan sun huta sunyi abinci sunyi sallah, sun nutsu.
Ja'afar ya kalli wayansa yana jujjuyata zuciyar ba dad'i tun jiya, dan tabbas yasan Ibtisam d'insa tana cikin damuwa.
Manyan idanunsa ya lumshe ya bud'e ya kalli Yahuza da Harisu abokan tafiyarsa, sai hirasu suke cikin walwala, sunata dariya.
Tsuki yay ya shafi sumar kansa, ya ce.
“Kufa ku tashi musan nayi hutun ya isa haka.â€
Harisu ya ce“Uban gidana kak'i fad'in garin da zamu dosa kai tsaye, tsakanin Tchad da Cameron? Ko muje Tchad idan baja sai mudawo Cameron ko?â€
Ja'afar ba tare da ya kallesu yana danna wayasa, yay dialing d'in number Baaban sa, ya ce“Inaga muje Tchad zaifi ko?â€
Yahuza ya ce“Wlh nima nan nafi kwad'aituwa, Allah yasa mu samu aiki na k'warai acan.â€
Ja'afar ya amsa da
“Ameen. Oh! Na rasa Baabaâ€
Ya fad'a yana sake kiran number mahaifinsa bata shiga.
Harisu ya mik'e ya d'auki jakarsa ya ce“Muje zama ba namu bane.â€
Basu musaba suka mik'e kowa ya d'auki jakar matafiyansa suka fito nan k'ofar sonef suka shiga keke napep.
Ja'afar yace ma me napep.
“Yauwa don Allah tashar mota zaka kaimu inda zamu samu motar Tchad. â€
Me napep ya ce“Akwai kuwa amman yanzu kwanan hanya zakuyi dan akwai tafiya.â€
Ja'afar ya ce“Ok muje mun gode fatanmu mu sauka lafiya shine kawai.â€
Nan me napep ya nufi babbar tashar motocin, ya kaisu har layin motocin Tchad, cikin ikon Allah mutum ukune daman suka rage sai ga su Ja'afar. Nan suka shiga mota kamasho ya amshi kud'insu ya sallami direba nan mota ta tashi jama'ar ciki kowa na addu'a, cikin nasara yanzu Ja'afar ya gwada kiran mahaifinsa ya sameshi.

*TAHOUA*
Unguwar Moray
Chapter 8 · 0% Book details