← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 118

Sashe 20

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Kukan me kike tinda kin gudo?
'Dagowa tai tana kallonsa idanunta sharkaf da hawaye.
Zama yay ya ce“Fa'damin me yasa kika za'bi barin iyayanki da kowa sbd ni? Ko dan ki tozarta iyayanki?â€
Ibtisam duk da tana tsoron Ja'afar amman hakan bai hanata shigewa jikinsa ba, cikin kuka ta ce.
“Kasani ban ta'ba son kowa ba sai kai bazan iya jure rashinka na har abada ba.â€
Zazzafar iskar bakinsa ya fesar ya Sani Ibtisan son so take masa, tana qaunarsa matu'ka kamar yadda yake sonta.
Fuskarta ya riqe da tafin hannunsa biyu, ya jefa mata gajiyayyun idanunsa ma'abuta lumshewa.
Cike da kasala ya ce“Mon cÅ“ur kalleni.â€
Wani irin fitinannan sanyi Ibtisam taji lokaci 'daya ya kama sassan jikinta, sbd yadda yay mata mgnarsa mai wujijjiga mata zuciya da gangar jikinta.
Kallonsa tai ta yi saurin rufe idanunta ta kirasa“Mon amour pls muyi aure wlh ina sonka ka ji.â€
Ta 'karashe mgnar tana fashewa da kuka,ta kifa fuskarta saman kafa'darsa.
Ja'afar yaja dogon numfashi ya ce“Ya Rabbi! Ok fa'da min ya akayi kika zo Tchad ke 'daya? wlh idan ba hakaba zan fita daga sabgar ki gobe na mayar dake gida.â€
Ibtisam cikin kuka ta ce.
“Randa na tambayeka sunan garin da kake a Tchad daman na gama ciro ticket 'Dina zuwa zinder duk da bansan inda zan dosa ba na gwammace nabar garin, shine fa da asubah bayan an tayar damu yin sallah na faki idanun Anna bayan ta koma 'daki, na tula tsunmakarai na rufesu kamar mutum,na fice gidan bus wadda tana shirin fita nazo.
Ku'din wajanka da ka ban shine kawai ban ha'da Dana kowa ba.
A zinder na kwana washegari da asubah muka wucce diffa daga nan muka samu motar Tchad naci wuya sbd sai da na kwan na wuni banci komai ba kud'ina ya 'kare, shine d mukazo na amshi aron waya na kiraka.â€
Ja'afar ya ce“Uhmm! Kinyi son ranki amman kinsan irin halin da kika jefa iyayanki?harda nawa iyayan tinda anacewa ni na 'boyeki da ni kaina kinsan yadda na shiga tashin hankali? Sannan Inda wani abun ya sameki fa?â€
Ibtisam ta kalleshi ta ce“Zan iya mutuwa dominka Mon amour. â€
Ta 'karashe cikin shashe'kar kuka.
Matseta yay jikinsa yana buga bayanta.
Ya furta“Ya Allah! Ok yi shiru baby ya isa ok.â€
Ya 'karashe mgnar yana ciro wayarsa ya kira number Baaban sa.
Bugu 'daya Malam Adamu ya 'daga da sallama.
Ja'afar ya 'kas'kantar da murya ya ce“
Baaba barka da yamma ina yini?â€
Daga can Malam Adamu ya ce.
“lafiya ba lau ba, Ja'afar iyayan yarinyar nan sun sakamu gaba wlh na rasa yadda zanyi, don girman Allah ka fa'damin gaskiya kasan inda Ibtisam take?â€
Ja'afar ya kalli Ibtisam tai luf 'kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya idanunta lumshe, hawaye na saukowa saman kyakkyawar fuskarta.
Mugun tausayinta yake ji, yarinya 'karama mai shekaru 17 ta iya takowa tin daga Niger har 'kasar Tchad dominsa sbd son da take masa, taya zai iya jure barinta cikin 'kunci?
Idanunsa ya runtse zuciyarsa na matsanaicin bugu, aransa ya ce“Ga 'koshi ga kwanan yunwaâ€
Sake matseta jikinsa yay ya aro jarumta ya ce“Baaba kuyi hkr komai zai wuce ina tayasu da addu'a insha Allahu Ibtisam tana hannu nagari.â€
Malam Adamu ya ce“Allah yasa Ja'afar ya kk da aikin fatan komai lafiya? Ina so Yahuza? Jiya munyi fira da iyayansu sai albarka suke saka maka wai duk sunsan Kaine jarumin.â€
Ja'afar ya ce“Baaba zan kiraku anjima.â€
Sallama sukayi Malam Adamu na sanya masa albarka.
Ja'afar ya ce“Malama 'dagani.â€
Numfashi ya ga tana fitarwa cikin nutsuwa alamar ma ta yi bacci.
“Ya Allah!â€
Ya furta yana kwantar da ita ya lulu'ba mata bargonsa, ya 'dauki wayarta ya ga ba chaji amace ya jonata chaji ya fito waje.
Zaune yay saman tabarma ya kira Baba Tsalha.
Bugu biyu ya 'daga.
“Yauwa Baba 'dazu ina gaggawa na cema sai nadawo, ya zanyi da yarinyar nan? Gaskiya ban son ta kasance cikin damuwa ko 'kunci, ya zanyi ma wlh dubara ta ku'buce min. Ga can ana zarginko ta gudo wajena, ya zan maidata ma ban saniba, tinda bazai yuba mu zauna waje 'daya ba aure tsakaninmu.â€
Baba Tsalha ya ce“Tashin hankali! Amman sai nake ganin bai kamata ka maidata ba gudun karta kuma guduwa ta shiga duniya arasata baki 'daya, bari na dawo gida zamuyi mgnar sai ta zauna nan wajan Falmata tinda ga Yara nan, kaga bazai yuba Ku zauna tare.â€
Ja'afar ya ce.
“Ngd Baba Allah ya qara girma.â€

Rahma tinda suka iso gida ta tattara ta tare wajan Abienta. Kiran sallar la'asar ne ya saka ta tafi 'bangaranta.
Raiyana zaune saman bed 'dinta tana waya.
“Humm! Ai wlh iya gaskiyar nake fa'da miki, yau naga abinda na jima ban ganiba, kuma ruwa da iska sai nayi wannan ha'di, dan ubanta ko zata barmin mijina ya huta, badan tsabar kamar da suke ba, wlh sai nace wajan haihuwarta likitoci sun canza masa yarinyar da aka Haifa masa, shegiya mayya kamar ita 'daya ce 'diyar attajiri aduniya sam yarinyar bata barin wata qofa da mutum zai samu shiga zuciyar Abdul Majeed na ratse da Allah sai na tarwatsa rayuwarta, rubuta ki ajiye. Idan tana nan bazan samu Majeed ba har abadan. Ita aunty Saro 'kidahumace sam bata gaenwa sabida ta samu nama da juice tana ci tana qara jibgewa kamar kayan wanki shi kenan bu'kata ta biya, da kayi mgna ta ce kayi hkr ka nutsu mtswwww!â€
Wahida ta 'kyal'kyale da dariya, daga can ta ce“
Ai ba zata ganeba ita taci dai, yanzu dai ki shirya zuwa jibi kizo mu tafi can 'din muji ta inda za'a fara wlh zataci ubanta, 'diyar gida zata hana matar gida walawala.
Raiyana ta ce“Ba wannan ba ma wlh na ha'diya yawu jikin ba'kin yaron nan da ganinsa zaiyi fawa inason sai ya kashemin 'kishirwata kafin nasan yadda zan ha'da aurensu da shegiyar balarabar nan, ko ya kika gani.â€
Wahida ta ce“Kin fini tsiya sosai amman karki fara neman lalatada shi ki kawar da Rahmar, muje kawai wlh malamin hatsabibine, zai miki yadda kikeso, tinda kin saka agano mazauninsa abin da sauqi jinnu zasuyi aikin wlh duk abinda kikeso sai kin samu.â€
Raiyana tai dariya ta ce“
Ok Ngd zamuyi waya anjima da dare.â€
Ta katse kiran ta mi'ke ta gyra jikinta tana dariyar nasara dan ji take komai ya kankama da ikon Allah.

Bayan da ya dawo daga masallaci, sallar la'asar ya yi wanka ya shirya cikin wasu fararen kaya riga da wando masu taushi, ya na fesa turare, yaji ana knocking 'din 'kofar.
Cike da takunsa na qasaita tamkar wani yaro 'dan shekaru 30 yake jinsa.
Key ya nurza ya bu'de 'kofar.
Sanye take da riga da siket 'yan Saudiya masu masifar kyau, kalar golden sai wani irin 'kamshi take, ta raba dogon gashinta biyu ta 'daure ko 'dan kwali bata yafa ba.
Abie ya ware mata hannayensa, ya na fa'din.
“Oyoyo Babyna.â€
Shigewa tai cikin 'kirjinsa ta 'kan'kameshi, ashagwa'be ta ce.
“Abie Rabin Raina yau inajin nutsuwa fiye da kullun duk da Abie 2 ya hana nai kewarka. Abiena kayi kyau sosai kawo na fesama turaren.â€
Ta 'karashe mgnar tana 'dagowa ta shafi sajansa zuwa gemunsa, tana 'da'ddage ta Kira “Abie Rabin raina, um zanyi kuka fa!â€
Abie ya gane nufinta.
Yay saurin tallafota jikinsa sosai ya saddo yadda tsawonsu zaizo 'daya cike da rauni ya ce“No! Rayuwata karki min kuka kinji oya toh.â€
Rahma cikin farin ciki ta sumbaci gemun da sajan da hancinsa ta dawo da kallon labb'ansa tana marerece fuska tana kallon 'kananun la'bban nasa.
Bakinsa taji saman nata ya sakar mata sumba mai sauti yana dariya, ya janyeta jikinsa ya ce“Toh Baby shi kenan ko?â€
Kai ta 'daga ta amshi turaren ta fesa masa ta ce“Abie Rabin raina muje wajan Abie 2 ko.â€
Gira ya 'daga mata ya kama hanunta ya kaita har gaban dressing mirror ta ajiye turaren yajata suka fito.
Raiyana wacce ta fito daga bedroom 'din ta bisu da mugun kallo, sai wayance ta ce“Kaga 'yar Abienta muje Abienki yaci abinci ko.â€
Rahma ta janye hannun daga cikin na Abie cikin sanyi jiki ta ce“Kuje kawai ni na tafi wajan Abie 2.â€
Bata jira amsar suba ta tafi ta fara taka steps cikin sauri kamar zata fa'di.
Abie ya ce“Baby kiyi asannu karki fa'da pls.â€
Rahma ko kallonsu bata bai taci gaba gaba da sauka cikin saurinta.
Raiyana ta rungume Abie ta baya tana fa'din.
“Nayi kewarka mijina sannu da zuwa fatan ka dawo lafiya?â€
“Alhmdllh! Fatan na sameku lfy?â€
Rahma ta waigo karaf idanunsu ya sarqe da na Abie, tai saurin juyar da kanta qafarta sauran ka'dan ta goce tai saurin riqe 'karfen benin, taci gaba da saukowa.
Abie ya zame jikinsa ya ce“Bakida hankali kefa 'diyata na kallonki bakya jin ko kunya.â€
Yay maza ya bar mata wajan cike da haushinta.
Chapter 20 · 0% Book details