← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 118

Sashe 1

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

7t: _*DATTIJON ARZIƘI*_

*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_

_*FITATTU HUD'U🔥*_

_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_

_ALHAMDULILLAHI! MASOYA GANI NA DAWO._
_GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAD'AUKAKIN SARKI, DA YA BANI IKON DAWOWA DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA DATTIJON ARZIK'I. YA ALLAH KAI DADIN TSIRA DA AMINCI GA SHUGABAN HALITTU ANNABI MUHAMMAD DA ALAYENSA DA SAHABBANSA BAKI D'AYA._

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

_*cнapтer 1&2*_

K'asar Tchad cikin garin
Ndjamena.
Lokacine na yanayin sanyi, amman na yau yafi na kullun.
Yau an ta shi da wani irin mugu-mugun sanyi mai shiga jiki dukkan sassan jikin 'dan adam,wanda garin yake d'auke da wani irin hazo sosai, dayawa daga cikin mazauna garin, wad'anda suke waje domin kasuwancin su na yau da kullun, su na sanye cikin kayan sanyi, sabida sanyi yau ya fita daban da ko yaushe.
Unguwar (Ambassadna)
Wani katafareran gidane wanda tin daga gate d'in gidan za ka gane gidan na kece raini ne, kallo d'aya zaka masa kasan eh mai shi ba k'aramin mutum bane.
Gidan tamfatsetesne an had'a komai na jin dad'in duniya acikinsa, babu ce kawai babu.
Ko ina ka bi acikinsa an k'awata shi da shukar flowers masu kyau da k'amshi, wani tafkeken lambune, mai d'auke da shuke-shuken 'ya'yan itatuwa daban², iccan dabino strawberry inabi mangwaro lemon zak'i iccan kwakwa gwaiba.
Gefe d'aya wajan kiwon tsintsaye ne, wasu manyan keji ne gudu 5 dana d'awisu talatalo jimina k'wak'wa tantabaru irin na turai, sai kejin aku (uban mgna).
kai! tsayawa fad'in tsaruwar gidan abubuwan burgewar da suke cikinsa zai jamu da nisa, amman tsarin gidan da komai ya ji ma Sha Allah.
Masu gadine mutum biyu sanye da uniform, k'arfafan gaske kallo d'aya zaka musu, kasan Tchadian ne.
Wata k'atuwar rumfar shan iska mai d'auke kyawawan kujero, gefenta, babbar rumfar ajiyar motoci, manyan motocine kala² na kece raina, ajere har gudu 10 cif acikin rumfar.
Wasu motocine gudu biyu jibga-jibga d'aya fara tass d'aya bak'a sud'ik, guda biyu, an fito dasu ana gogewa, security's nata zagaya wajan motocin rik'e da bindigogi ahannunsa, sai kai komo suke suna bubbud'e hanci.
Matashiyar budurwa ce sabon jini, 'yar kimanin shekaru 18 aduniya.
Tsaye jikin k'ofar bedroom d'inta wacce tsayawa baiyana kyawun d'akin nata da dukiyar da aka kashe mata wajan makwancinta da abubuwan more rayuwata, b'ata lokacine, duk da ta kasance ba k'asar take karatu ba.
Sanye take da abaya mai taushi blue colour, mai adon duwatsu masu matuk'ar tsad'a farare tass. Ta yane kanta da d'an kwalin abayar, wacce ta zauna jikinta cif Ma sha Allah.
Jelar gashinta mai tsayi ta zubo har gadon bayanta.
Sam ita ko sanyin da akeyi bata ji, sabida ta wadatu da na'urorin d'umama d'aki a bedroom d'inta, haka ita d'in mai son sanyi ce sosai, yanzu abin sanyi data sauka ta sha ta kasa bacci sabida yunwa.
Ahankali ta fara taka matattakalar banin cike da nutsuwa, domin saukowa beni na d'aya, (Kasancewar ita a hawa na 2 ta ke.)
Wata irin tafiya take wacce ta sanya dukkan jikinta motsawa, tamkar tarwad'a, sai k'ananun pinky labb'anta take motsawa tana d'an lasarsu, k'ananun fararen shanyayyun idanunta ta ke d'an lumshewa tana bud'ewa wayace *iPhone 13 pro max*.
Kallo d'aya zaka mata kasan ruwa biyu ce, sai dai akallon farko zaka san ita d'in jinin larabawace, sabida yawan tulin gashinta, ga dogon siririn hancinta zuwat amik'e, bakinta d'an k'arami mai taushi kalar pinky, tana da gashin ido gazar² masu tsayi da gashin gira mai kyau idanunta 'yan k'ananu ne tamkar tana jin bacci farare tass, tana da gashi har tsakiyar bayanta, fatarta kwance luwai ga taushi kyakkayawace, amman ba irin mugun kyau can-can ba, sai dai fa itad'in cikakkar macace duk da kuwa k'arancin shekarunta, Allah ya k'erata Masha Allah, ita d'in ma'abuciyar son k'amshi ce, yanayin fatarta irin ta ruwa biyu ce, ita bata cika fararen mata tass ba, haka ita kuma ta fi chocolate hasken fata.
Doguwace amman ba can ba, sabida d'an kaurinta kad'an ya b'oye asalin tsawonta, tanada matsagai cin jiki, mai d'aukar hankalin duk wani namiji mai lafiya. K'irjinta cike yake da dukiyar fulani tsayayyu masu kyau.
Tana da hips mai d'aukar hankali haka Masha Allah bom-bom d'inta tamkar na manyan mata suke masu 'dan girma ba can-can ba, batada dimples haka batada wushirya, amman hak'oranta k'ananu farare tass ajere cases.
tana da sanyin hali bata fiye mgna ba sam bata shiga abinda bai dameta ba, miskilace sosai, amman tanada kirki da tausayi, ga kyauta.
Halinta dai na rashin son mgna ko hayaniya, sai ku wuni da ita bata ce maka k'alaba, hirata Abie d'inta ne, dan ko da Raiyana matar Abie, basu fiye mgna ba, duk da kuwa yadda take sonta amman sam ta kasa sakin jiki da ita. Dan ko Jaddatu Rahamu bata fiye mata surutu ba, sai idan ta yi abin dariya kasancewar Jaddatu Rahamu mafad'aciya ce ta k'arshe.
Dab da zata k'arasa saukowa beni na d'aya jikin k'ofar Abienta, ta taji muryan Ammi Raiyana tana ruwan masifa.
Da sassarfa ta k'araso jikin k'ofar bedroom d'in ta tsaya, da niyar bud'ewa ta shiga dan zaton ko Latifa ta saka aiki gyara b'angaran Abie ta mata shirme.
Wata irin tsinkewa taji zuciyarta tayi, sakammakon tsinto mgnar Raiyana da tai tana fad'a masa bak'ak'en maganganun da taji karaf akunnenta, ta fad'awa mahaifin nata mafi soyuwa azuciyarta.
Jikinta rawa ya soma, zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu uku².
Ta dafe setin zuciyar tata, da sauri ta runtse k'ananun kyawawan idanunta wanda suka fara rikid'ewa sukayi jajir, sabida mummunan b'acin ran da ya ziyarci zuciyarta.
Wani irin wahalallan numfashi taja da k'arfin gaske, kafin ta shiga sauke shi da sauri² ajere² kamar tayi gudun tsere, yayin da dukkan jikinta yake tsuma.
Wani irin abu taji na yawo adukkan sansan ajikinta kamar tsutsotsi.
Yayin da take wani irin fitinannan sanyi ya kawoma jikinta farmaki, wanda ta soma game jikinta waje d'aya, sabida k'ark'ashin tafukan k'afafunta da tafukan hannunta suka d'auki wani irin mugu-mugun sanyi, take ji wanda yake ratsa dukkan k'ofufun mahudar gashin jikinta baki d'aya, har ya kai tana had'e hak'oranta waje d'aya.
Wahalalliyar ajiyar zuciya ta sauke yayin da take ciza k'ananun pinky lips d'inta masu taushin gaske.
Ta runtse k'ananun shanyayyun idanunta, ta sanya dukkan tafukan hannunta ta toshe kunnuwanta, tana fizgo numfashinta da ya ke kai komo, ta bud'e idanun nata taja k'afafunta dakyar ta koma sama, tana mai jin mugun tsanar Ammi Raiyana.
Chapter 1 · 0% Book details