← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 118

Sashe 78

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jaddatu ta hango zaune tana waya sai washe baki take.
Kallo 'daya tama Rayyana ta kauda kanta, tsaf shirinta tana cikin blue shadda tayi kyau komai blue ne ajikinta har jaka.
Hanan ta ce“A'a kaga Autar Abienta yau fa kwalliya ta yi kyau.â€
Iman ta tarbeta da gudu Rahma ta 'dagata tana murmushi ta ce“Abbyn ummina na gaisheki keda Jaddatu da ammi Hanan.â€
Ta 'karaso falon ta, zauna tana ajiye Iman ta ce“Ammi Rayyana barka da safiya .
Ammi Hanan ina kwana?â€
Ta 'karashe mgnar tana kwantowa jikin Jaddatu ta sumbaci kumatunta ta ce“Masoyiya Jaddatu fatan kina tashi lafiya? Da wa kike waya?â€
Rayyana cikin sakin fuska ta amsa gaisuwar ta ce“Baby zaki rakani gida mu yini?â€
Kai ta langwa'bar ta ce“Kashhh! Ammi da Abienah na nan ne sai muje kinga kuwa ban ta'ba zuwaba wataran zanje.â€
Murmushi Rayyana tai ta ce“Ai kuwa zamuje wataran ummi qarama.â€
Rahma ta miqe tana amsa gaisuwar Meerah ta ce“Meerah pls a 'dan gyaramin 'daki wlh na gaji na Abie na gyara. Latifa! Pls zo kuje ki Kama mata.â€
Ta 'karashe mgnar ta nufi corridor 'din da zai sadata da dining area.
Rayyana baki da hanci ta saki tana kallon Rahma har ta 'bace mata, lamarin yarinyar na bata tsoro matuqa, sai ta dinga mata gani² kamar ba matar uabanta ba, tamkar kishiya haka take ganin abinda Rahma take mata.
Meerah da Latifa suka haye sama dan cika aikin uwar gidan tasu.
Jaddatu na gama waya Rayyana ta ce“Ummi zanje gida amman bazan kai dareba.â€
Jaddatu ta ce“Ikon Allah ashe dai har yanzu da saura toh agaida mutanen gidan.â€
Rayyana jiki asanyaye ta amsa sukayi sallama da Hanan ta fita.
Hanan ta ce“Iman jeki wajan Auntinki ta baki chocolate.â€
Cikin murna ta tafi.
Hanan ta ce“Kai Ummi don Allah ki daina mata hakan shi wanda ya ajiyeta idan yana bu'katar zama da ita fa!? haba!â€
Sandar hannunta ta d'aga zata kwa'da mata ta matsa nesa tana dariya.
“Ke! Jiddah bana son magnar banza wato kece munafukarta ko? Wlh zan sa'ba miki korar kare zan miki ki tattara ki koma Morocco kafin mijinki ya dawo munafuka na tsani matarnan wallahi idan ma zama zaiyi da ita ya rabamu ai yanada gidaje bana son ganinta Sam.â€
Hanan tai muqus taja bakinta ta tsuke sanin halin uwar tata.
Rahma tana gama breakfast ta dawo falon ta zube jikin Jaddatu tana nuna mata wayar da Abie ya siyamata sabuwa.
Jaddatu ta ce“Yauwa 'dan albarka ya kyauta, kuma ta yi kyau sosai.â€
Rahma na murmushi ta shiga camera suka fara salfie.
Sama ta koma ta nemo number Anee a cikin kundinta na ajiye numbobi, ta sanya ta Kira tana zubewa saman sofa a falonta, yayin da su Meerah Duke aikin goge-goge har sun gama.na bedroom.
Cikin sa'a kiran ya shiga.
Anee lokacin suna tare da Rafeek a compound 'din gidan Auntie ta, ya zo mata magiyar ta ha'dasa da Rahma har wata 'yar rama ya yi,duk ya susuce rashin samun layin Rahma.
Anee ganin number kamar ta Chad ta 'daga tana “Hello! Waye?â€
Rahma ta 'kyal'kyale da dariya ta ce“Habibiyarki ce dallah can yau Rabin raina Abie ya siyamin sabuwar waya, ya amshe waccan har layin, kinsan My Abie akwai rigima, ni *Baby Abie rigimata* ma zan dinga cemasa wollah.â€
Ta 'karashe mgnar tana 'kyal'kyala dariya.
Anee ta ce“Innalillahi! Wallahi Rahma bakida mutunci Allah ganinan inata nemanki kamar nayi hauka bana samunki kuma banda number Abienki bare na kirasa hope kina lafiya? Wai yaushe kika zama 'yar iska baban namu zakina cema Baby rigima? Yau kam Habibyta a farin ciki kike, meye sirrin Rahmatah?â€
Anee ta tambayeta itama tana sakin dariyar farin cikin samun 'kawar tata.
Rafeek jin Anee ta ambaci Rahma ya warce wayar cikin zafin nama ya kai kunnensa cike da 'dauki da farin cikin samunta.......!
_😩Duk yadda naso naje Inda nakeson zuwa banzo ba yau, dole na hkr, wai nagaji wlh Tabb rubutu masifa ne.🤣_

_Rahmerh ladingo😉_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/29/22, 16:56 - Buhainat: ```D A```

```79&80```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_

Cikin 'daukin samunta da son jin muryata, Rafeek ya bud'e baki zaiyi mgna,yaji zazzaqar murya Rahma tana siririyar dariya.
Dan bata san meke faruwa ba, ta sake sakin siriryar dariya, ta ce“Wlh Anee Abie ne ya bani irin wani farin ciki yau, inajin nisha'di sosai billahi.â€
Rafeek wani suman da'din jin sautin murya Rahma ya kusa yi, cikin zumu'di ya ce“Baby cute shi ne kika tafi kika barni da kewarki ko? Kinsan irin halin da na shiga? Yanzu ma nazo gidansu Anee ne, naji ko tanada labarin ki, sai ga shi nazo a sa'a Alhmdllh! Ykk baby cute nah?â€
Rahma daga can ta zazzaro kyawawan 'kananun idanunta, ta ce“Rafeek! Ykk? Wlh tafiyar kai tsaye ta sameni shiyasa.â€
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce“Na azabtu wlh baby cute, pls ki ban dama na fito neman aurenki bazan hanaki karatu ba.â€
Rahma ta ce“Kayi hkr zan nemeka idan buqatar hakan ta taso, amatsayin yanzu matar wani ce ni mahaifina ya 'dauramin aure kuma bazan bijire masa ba, pls karka kirani muyi hkr kawai.â€
Tana gama mgnar ta katse kiran ha'di da kashe wayar baki 'daya.

Rafeek jin Rahma ta katse kiran ya sake kiranta hankalinsa a tashe, amman switch of.
Anee ta amashi wayarta tana fa'din.
“Abinda nakeson kwatanta maka kenan, kayi hkr Rahma tanama mahaifinta biyayya sosai ba lallai ta saurareka ba.â€
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zarya akan fuskarshi.
Ya ce“Me yasa zatayi min haka? Ban wayarki na 'dauki number tata.â€
Anee ta girgiza kanta ta ce“'kilama sbd kai aka canza mata layi, sbd Rahma bata tsayawa da maza kai ka'dai naga tana kulawa.â€
Haka ya tafi ransa a 'bace gani yake kamar taci amanarsa ne. Anee ta shiga gida tana sake gwada number Rahma bata shiga.

A can kuwa Chad Rahma wayan ta ajiye saman center table, ta sanya hijab har 'kasa ta sauka 'kasa ta nufi 'bangaran Abie 2.
Auntie Saro zaune a falo tana ma Umaima 'yarta gyaran gashi ta shigo da sallama.
Auntie Saro ta amsa tana kallon Rayyana, cike da mamaki ganinta ba akwai, Umaima ta miqe ta rungumeta tana mata sannu da zuwa.
Rayyana ta zauna kusan Saro tana murmushi ta gaisheta.
Auntie Saro ta amsa ba yabo ba fallasa.
Rayyana ta ce“Kai Auntie wai meye kike ciccin magani?â€
Saro ta ce“Umaima jeki waje ki qarasa aikinmu.â€
Fita tai ta fuskanci Rayyana ta ce.
“Wai ya na ganki haka ziqau? Ko ya hkr ne?â€
Rayyana ta 'kyal'kyale da dariya ta ce“Lah! Wlh ya yafemin baiyi fushi ba, jiya 'dakina ya raba dare.â€
Auntie Saro ta ce“Ikon Allah! Shi kuwa wane irin mutum ne kina nufin ya sauke miki nauyin da yake kansa?â€
Rayyana akayi fari da idanu, ta ce“A'a amman ya kusa.â€
Saro ta ce“Humm! Raiyanatu kenan toh Allah ya jishemu alkhairi.â€
“Ameen Auntie wlh ba wata matsala, yanzu ma shiyasa aka kawoni ya ce kar nayi driving da kaina, ga sakonki ya ce na siyo muku tsaraba ni kuma na kawo miki ku'din.â€
Auntie Saro ta amsa tana jinjina kai tabbas akwai abinda yake jira kafin ya sallameta sam bata yardaba, wai ya hkr.
Saro ta ce“Masha Allah mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi.â€
Rayyana ta amsa da “Ameen.â€
Nan suka fara hira duniya.

Abie zaune yana kallon Tv casbi a hannunsa, Rahmatoubulie ta bu'de 'kofar ta shigo da sallama.
Abie2 ya amsa yana fa'din.
“Diyar albarka kece yanzu da Rana?â€
Murmushi Rahma tai ta zauna kusansa tana gaishesa ta ce“Abie inata kewarka mun jima bamuyi hira ba sosai azahiri sai a waya.â€
Dariya yay ya ce“Aikuwa dai 'diyar albarka, Abienki ya yi tafiya ko?â€
“Eh Abie2 amman yau Latifa bata zo ta gyarama falo ba? Bari idan naje zan turota, ko Meerah.â€
'Yar dariya yay ya ce“Yanzu nan ina wata dau'da?â€
Rahma ta ce“Abie2 bakaga wayana ba me kyau irin waccan Abienah ya siya min bari na 'dauko kagani.â€
Ta miqe kafin ya yi mgna ta fice.
Abie2 ya girgiza kansa yana murmushi.

Acan Niger
Da yamma su innah Hansatu suka tafi ganin Ibtisam.
Zaune suke a tsakiyar gidan, Taslim ta 'dora girkin yamma, Ibtisam zaune kusan Laraba, su Aydah na sabgogin gabansu.
Ramadan ya kalli Ibtisam ya ce“Wai aunty meke damunki kalli yadda kika zuge?â€
Laraba ta ce“Kaikuwa Ramadan dukama yaushe ta warke.
Ibtisam ta ce“Ni kaga ba abinda yake damuna kawai yanayin rayuwane...â€
Sallamar su innah hansatu ya katse mata mgna.
Laraba ta amsa tana fa'din.
Marabanku da zuwa, Ibtisam 'dauko babbar tabarma.â€
Ibtisam ta miqe tana Jan tsuki aranta taje ta kawo tabarmar da shimfi'da suka zauna ta duqa ta gaishesu.
Deluwa ta ce“Sannu ya jikin? Allah ya qara sauqi.â€
Ibtisam ta amsa da“Ameen.â€
Ta miqe ta nufi 'daki, innah ta bita kallo ganin yarinyar fuska ba walwala.
Yaran dukansu suka gaishesu.
Laraba ta zubo musu ruwan sabuwar Randa me sanyi, ta zauna suka gaggaisa, innah batayi tunanin Laraba zata tarbesu haka ba.
Ibtisam kuwa haushinsu takeji shiyasa ta shige 'daki sai da zasu tafi ta fito ta rakasu har bakin titi suka samu abin hawa.

Da dare bayan sallar isha Map Adamu yazo har nan gidansu Ibtisam shi da Tanko suka tsayar da ranan biki sati uku masu zuwa.
Yana zuwa gida ya gayama Ja'afar akan ya fara ha'da kayan lefe biki sati uku masu zuwa. Da toh ya amsa dan bai Iya jayayya da mahaifinsa.
Chapter 78 · 0% Book details