← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 118

Sashe 70

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma'aikatan gidan suka baibayesu da sannu da zuwa Abie na basu hannu 'daya bayan 'daya suna musabaha.
“Baby kuje ciki ganinan shigowa.â€
Meerah ta janyo trolley suka nufi ciki Rahma hannu kawai take 'daga musu duk wanda ya gaisheta ko ta ce“Ngd.â€
Daman surutunta baki Abie ne da Jaddatu sai Abie 2 Anee Su Ummiterh, Meerah kwanan nan ne suke hira sosai.
“Meerah mu shiga wajan Abie 2 na gansa nayi missing 'dinsa.â€
Ta fa'da tana nufar 'kofar wanda yay daidai da fitowar Ibtisam wacce ta maidoma Tanko wayarsa sun gama hira da su Dadda.
Ibtisam gabanta taji ya fa'di ganin zuqeqiyar balarabiya agabanta, idan ba gizo idanunta suka mata ba ita ce ta jikin hoto rungume da Balarabe.
Ibtisam ta ha'diye wani yawu na baqin ciki tana qoqarin wucewa duk yadda taso tama Rahma mgna ta kasa.
Rahma har zata shareta sai ta tuna ai tayi ciwon ta'bin hankali qila bata warke duka ba. Ko ba komai Abienta ne sanadi dole ta kula duk abinda yake ajiyar Abienta idan ba haka ba wannan yarinyar tayi ka'dan ta fizge mata kai.
Hannun Ibtisam ta kamo ta ce“Ibtisam ko? Congratulation barka da samun lafiya.â€
Ibtisma ta kalli tattausan hannun Rahma mai wani irin laushi da ya riqe hannunta sai wani shegen fitinannan 'kamshi yake tashi ajikinta qamshin sak taji irin na Balarabe.
Yawu ta ha'diye a French Ibtisam ta ce“Bana jin turanci sai French. â€
Rahma ta saki hannunta tana murmushi da French ta maimaita mata abinda ta fa'di sbd tanajin French sosai.
Murya Abie ta daki dodon kunnen Rahma da Ibtisam.
“Baby me kike atsaye anan?â€
Rahma zatayi mgna idanunta suka sauka akan zoben diamond 'din Abie a yatsar hannun Ibtisam.
Cike da mugun kishin da bata san daliliba, ta damqe yatsar ta waiwayo ta tsare Abie da kyawawna 'kananun idanun ta ce“Abienah me ya kawo zobenka hannun yarinyar nan?â€
Ihun Ibtisam sukaji wacce ta dafe cikinta ta fashe da kuka ta sulale zata fa'di 'kasa sai lokacin Abie ya ankare da yarinya, tsaf ya karanceta.
Rahma ta tarota tana fa'din “Abie temaka mana wlh ta suma daman bata warke ba ku ka dawo?â€
Abie ya ce“ No! Matar wani zan kama? Meerah kamata, Baby wuce ciki ki huta umarni nake baki ban son musu oya zo mutafi.â€
Ya 'karashe mgnar yana wucewa ya fasa ma zuwa 'bangaransu Abien, dan dole sai ya ra'basu zai wuce.
Ibtisam jin abinda Abie ya ce ga Rahma na shirin sakinta ta bisa hakan ya saka ta..................

_Rahmerh ladingo😉_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/19/22, 18:59 - Buhainat: ```D A```

```69&70```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_

_Afuwa wlh yau na tashi da wata irin mura ta maqoshi, sam komai baya min da'di, but nayi typing ga dai shi nan so bansan ko bazai maku da'di ba dan kawai dai ina son ragewa ga azumi na gabatowane shiyasa nai maku Ngd_

Ta riqe Rahma sosai tana kuka tana fa'din“Wayyo cikina aunty zan mutu, kaina marata.â€
Ta 'karashe mgnar cikin kuka, tana dafe cikinta.
Rahma macace me tausayi sai kawai ta ru'de hankalinta amugun tashe, ta ri'ko Ibtisam tana mata sannu kamar zatayi kuka, ta ce“Meerah temaka mu shiga ciki inada magani sai na bata idan baiyi sauqi ba sai muje hospital. â€
Ibtisam da'di ya cikata ganin Rahma zata tsaya tare da ita ta sha magani, ko banza ai ba zata bi balarabe ba.
Kafa'darta suka shiga suka nufi ciki da ita, tana kuka 'kasa² Rahma na mata sannu duk ta damu, dan tasan ciwon ciki ba da'di.
Abie kuwa bai tsaya jiran Rahma ba, ya wuce ciki.
Tsaye yake 'kofar falon doorbell ya danna sau biyu, Jaddatu tana zaune ta washe baki ta ce“Su takwara an iso, Latifa zo bu'de 'kofar.â€
Rayyana ta miqe cikin rawar jiki ta ce“Ummi bari na bu'de musu.“
Ta kalli Latifa wacce ta fito da saurinta zata nufi hanyar falon, ta ce“Latifa koma aikin ki zan bu'de.â€
Ta 'karasa mgnar ta nufi hanyar falon tana wani irin taku me cike da nutsuwa sai wani irin fitinannan 'kamshi yake tashi ajikinta.
Hanan ta kalli Jaddatu tana dariya ta ce.
“Dan Allah Ummi kiba Rayyana lafiya ki saka musu idanu ba ruwanki.â€
Jaddatu batace uffan ba.
Ahankaali ta 'dora hannunta saman handle 'din 'kofar, ta bu'de.
Idanu hu'du sukayi da Abie wanda shigarsa ta kusa gigita Rayyana, wai irin mahaukacin kyau ya mata ga wani irin kwarjini na musamman, duk da 'kamshin da yake tashi a ko ina bai hana Rayyana jin dadda'dan 'kamshin Abie na musamman ba!
Abie fuskar shi ba yabo ba fallasa yake kallonta, ya ra'bata zai wuce tai saurin fa'dawa jikinsa ta rungumeshi gam, cike da murnar ganinsa take fa'din.
â€Oyoyo Habiby sannu da zuwa ina Ummin mu ne?â€
Daidai lokacin su Rahma suka iso wajan.
Wani irin abu ne ya tokare 'kirjin Rahma ganin yadda Rayyana ta ru'kum'kume Abienta 'kam, tana zuba maza sannu da zuwa.
Zuciyarta wani irin mahaukacin bugu take wanda ada batajin hakan idan taga Rayyana da Abienta.
Dakyar ta iya 'ko'karin janye idanunta akansu daidai Abien na qoqarin 'ban'bareta daga jikinsa ta sadda kanta suna riqe da Ibtisam wacce baqin ciki da takaicin su Rayyana da zafin kishi ya sakata Sam ta manta 'karya ciwo take ta miqe tana hararansu afakaice ta ce“Aunty cikina ya lafa ma zan iya tafiya Ku sakeni.â€
Rahma daman sam bata cikin hayyacinta ta saki Ibtisam zata wuce Rayyana ta rungumota tana fa'din.
“Oyoyo ummina sannu da zuwa ya gajiya? Muje kiyi wanka kiyi sallah kizo kuci abinci.â€
Rahma ta dake ta qaqalo murmushi ta ce“ammi na sameku lafiya? Ya 'karfin jikin?â€
Ta 'karashe mgnar tana satar kallon gefen Abie taga wayam baya wajan.
Ajiyar zuciya ta sauke.
Meerah ta gaishe da Rayyana ta amsa cikin sakin fuska.
Suka nufi falon.
Ibtisam kuwa tuni ta shige 'bangaransu ranta amatu'kar 'bace.
Rungume da Jaddatu ta hango shi yayin da Hanan take kusansa zaune Iman na zaune acinyarsa sai 'kayataccan murmushi yake saki wanda ya bayyana fararen haqoransa dimples 'dinsa suka lo'ba.
Rahma ta lumshe kyawawan 'kananun idanunta tana jin bugun zuciyarta na tsananta.
Hanan ta taso aguji ta rungume Rahma tana fa'din.
“Oyoyo Ummina ta dawo.â€
'Yar dariya Rahma ta yi tana hugging 'dinta sosai cikin siririyar murya ta ce“Ammi na sameku lafiya?â€
“Alhmdllh! Baby Abienta.â€
Fuska ta yamutsa wanda daidai lokacin suka ha'da idanu da Abien ya 'daga mata gira ta kauda kanta tana ha'de face.
Da sassarfa ta isa wajan Jaddatu ta ra'ba gefenta har jikinsu da Abie na ha'duwa.
Sumbatar Jaddatu tai ta ce“I miss you Jaddati.â€
Jaddatu ta rungumeta tana buga bayanta, cike da 'kaunarta.
Abie ya miqe ya nufi saman bene cikin kuzari yake taka steps.
Rayyana ta miqe tabi bayansa.
Jaddatu ikon Allah take gani.
Rahma tana kallonsu sai ta rufe idanunta ta nutsa kanta 'kirjin Jaddatu.
Kayansu ne Ummi Adnan da Latifa suka shigo da manyan trolleys.
Jaddatu ta ce“Ku haura dasu sama.â€
Rahma ta bu'de idanunta wanda sukayi jajir ta miqe tana 'ka'kalo murmushi ta ce “Meerah muje sama.â€
Jaddatu ta ce“Toh Ku fito ba kuci abinci don Allah.â€
Kai Rahma ta 'daga zata wuce taji muryar Laraba wacce ta fito tana gaishesu da musu sannu da zuwa.
Rahma ta jinjina kanta ta ce“Ngd ina Ibtisam?â€
“Tana ciki wai kanta yake ciwo.â€
Rahma bata ce komai ba ta haura sama.
Dai dai 'kofar 'dakin Abie takejin mgnar Rayyana a falo dan wannan mgna ba bedroom bane.
'Kirjinta taji ya buga da 'karfi tai saurin wucewa.
Falonta ta shaqi wani irin 'kamshi me da'di ko ina fess ta zube saman sofa tana fa'din.
“Latifa iyayan gyara ko ina tsaf. Pls Meerah ha'damin ruwan wanka sai muje na nuna miki 'dakin da za ki zauna.â€
Meerah ta amsa da “Toh.â€
Ta nufi hanyar bedroom 'din Rahma.
Bayan ta cika mata bathtub da ruwan 'dumi ta zuba sabulu na ruwa da turarukan wanka masu 'kamshi, ta ciro sabon towel a ledarsa ta rataya saman abinda ake sarkafe kaya, ta fito.

Fitowa sukayi Rahma ta nuna mata 'dakin da yake face da nata ta ce“Shiga akwai komai na bu'kata bedroom ne da toilet ba falo ki duba idan kina bu'katar wani abun kimin mgna, idan kinyi wanka kin shirya kinyi sallah sai fita zuwa cin abinci.â€
Godiya Meerah ta ma Rahma ta shige ciki yayin da Rahma ta koma ciki.
Kwance tayi cikin ruwan tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe idanunta.

'Bangaran Abie Yana shigowa falonsa, wayarsa ta 'dauki ringing ya zube man sofa yana amsa wayan, Rayyana ta shigo. Kai tsaye ta shiga bedroom 'dinsa ta ha'da masa ruwan wanka, ta fito har lokacin yana amsa wayan.
Kusansa ta zauna ta zare masa takalmin sa ta cire safan, ta kwanto jikinsa tana kallon fuskarsa mai cike da kwarjini uwa uba haiba.
Face ya ha'de ya matsar da ita gefe yana ciga da amsa wayansa.
Yana idarwa ya miqe zai shige ciki ta riqo hannunsa cikin zubar hawaye ta ce“Dan Allah Habiby karka haramtamin kanka naji na yarda zan zauna dakai daga nan har lokacin da kayi niyar kusantata bazan sake maka rashin kunya ba ko roqon ka bani haqqina don Allah ka yafemin laifin da na maka karka sakeni wlh ina tsananin 'kaunarka Habiby.â€
Ta 'karashe tana sakin kuka ta rungumeshi.
Bayata ya buga ya ce“Ok naji amman pls kibar takurani ina buqatar hutawa zamuyi mgna idan na nutsu OK?â€
Kai ta jinjina ta ce“Toh Ngd Allah ya qara hucemin zuciyarka dan Allah idan ka fito kazo kaci abinci na girka maka duk irin launin Abincin da kakeso.â€
Kai ya jinnina mata ya nufi bedroom, ta zauna zaman jiransa ta rabka tagumi.
Chapter 70 · 0% Book details