Sashe 98
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ihsan kwance saman gadon Ikram tana waya da Abubakar, Ikram na gefe tana duba mahadin kayan da zasu sanya na dinner party wani leshi ne ruwan hoda saik uwa sauran yan mata sa'anninsu, Intisar ta shigo, ta dubesu kaf sannan ta tsaida idanunta kan Ikram.
"Kanwata zo." Ta dubeta kafin ta mike ta maida kayanta sif ta bi bayanta.
Kai tsaye yar barandar Hajiya Babba suka isa wacce kana iya hangen harabar gidan ta nan. Ta dubeta da kulawa.
"Ki fadamin damuwarki don Allah Ikram, ke ba ki lura da sauyin da ki ka yi ba tun kafin soma bikin Yaya Faruk? Menene ya ke damunki haka da har ki ke ramewa? Kin koma wata shiru-shiru kamar ba Ikram din da na sani ba mai yawan hira da dariya."
Ikram ta ji gabanta ya fad'i, wato har an fahimci damuwarta? Ta k'ak'alo murmushi.
"Kai in-law, nifa babu abinda ke damuna..."
"Karya ki ke wallahi, ko yanzu kin fuskarki ta kara tona miki asiri, lallai kina cikin damuwa saidai kuma idan ba ki yarda da ni ba ne shiyasa bakyason sanarmin. Barin kashi a ciki fa ba ya maganin yunwa. Yanzu gayamin, me ya hadaki da hoton wannan Gidadon a jakarki, dan uwan Ummi?"
Idanuwa a waje ta ke duban Intisar, ga wasu ruwan hawaye da suka ciko mata. Daidai lokacin Gidado da Abubakar da kuma Haidar suka shigo harabar gidan suna hira da dariya kamar dama can sun saba, daman suna kofar gidan, hankalinsu ya kai garesu, suka dubesu, Gidado ya saje da yan birni, sanye ya ke cikin farar shadda marar nauyi mai tsada cikin wanda Abubakar ya dinka mishi don Abubakar mutum ne mai yiwa yan uwa sosai, sam abin hannunsa bai rufemishi idanu ba, barshi dai da son ta6a mace idan yana sonta wanda ya ke fatan ya daina.
Su kuwa basu ko lura da su ba har suka wuce, Ikram hawayenta ya zubo wani irin wutar so tana kara ruruwa cikin zuciyarta har batasan lokacin da ta dubi Intisar ba ta soma magana bayan ta rike hannunta.
"Ina sonshi tun sadda na soma ganinsa a hoto."
Ta kwashe labarin komai ta sanarmata har zuwa sadda ta fahimci yana da mata.
Ta karashe tana kuka, kasancewar wajen gilas ne yasa na falo ma yana kallonsu, Hajiya Mama ta kwala kiran sunan Intisar. Ikram ta juya baya da sauri tana share fuska, Hajiya Mama ta karaso.
"Ku kuma lafiya? Me ya sami Ikram din?"
Ta fada tana duban Ikram mai share fuska, Intisar ta wayance.
"Um wai kanta ke ciwo shine abu bai kai ya kawo ba ya bata haushi wai ana damunta da hayaninya a daki."
Hajiya Mama ta hau ta da fada.
"To shine za ki zauna kina faman kuka, jimin aikin banza, ke kuma ki ka biyemata? Zo ki je ki bata magani mana, kuma ku soma shiri ga Magriba ta yi yanzu za'a wuce."
Suka amsa da toh. Intisar ta dubi Ikram cike da tausayi.
"Shakka babu wannan lamari ya bani mamaki matuka wallahi, amman ki bari za mu yi maganar daga baya, mubar nan kafin Hajiya Mama ta dawo."
Suka fice.
Wajen biyar da rabi Ummi ta amsa kiran Daddy don yi mata nashi nasihar. Kanta a rufe da mayafi, ga mamaki nan ta tarar da Faruk, ta zauna ta gaisheshi ya amsa fuska a sake.
Nan ya shiga yi musu nasiha mai ratsa jiki da jini har ta kai Ummi ita mace mai rauni soma hawaye, shi kuwa gogan gaba daya jikinsa ya yi sanyi matuk'a, can kuma ya sallami Ummi, ta yi mishi godiya bisa karamcin da ya yi mata, ta nuna ta daukeshi matsayin uba gareta, ya ji dadin kalamanta da addu'o'inta gareshi. Ya yi mata fatan alheri gami da sanyamata albarka.
Haka ta koma dakinta jiki babu kwari, yan uwanta yan Gombe da yawansu sun wuce ganin gidanta da kuma kai ragowar kayan da suka zo da shi da na gudunmuwa da ta samu.
Karfe bakwai na dare aka soma shirin tafiya Party, alokacin sun dawo gida kowannensu na yaba tsarin gidan Faruk da Ummi. Har hotunan suka nunamata banda murmushi ba abinda ta yi, kwarai ya tsaru duk da cewa flathouse ne. Ana wannan shirye-shiryen ne wata arniyar mota jeep ta shigo harabar gidan, inda wasu mata su bakwai suka sauko. Da gudu Husna ta isa garesu ta rungume, Fati ta nemi sanin ko su waye musamman ganinsu da anko wanda yafi na mutan gidan kyau da tsada, kafin ta amsa mata wata motar bus ta k'ara shigowa, nan kuwa ta ga matan rututu duk cikin ankon suma, wani arnen leshi suka sanya saidai suma kalar ruwan hodar ne, sun yi kyau har sun gaji da haduwa. Dariya Jidda ta yi tana duban Fadila.
"Wannan (ta nuna wata 'yar fara-fara doguwa cikinsu) Farha sunanta, schoolmate dita ce, ina yawan basu labarin kawata Ummi shine fa suka ce sai sun zo bikinta, kinga ango saida ya bani katin kowaccensu ya ce na bawa duk wasu masoyansu, nan da ki ke gani har da yan groups dinmu na whatsapp. Su Sally, Bingel, sophie, Fatima Aminiya, Ummu abdool, shamsiyar katsina, Ab kura, shukra, Dg da sauransu wallahi suna da yawa ne."
Fati ta dubesu, tabbas kuwa harda wadanda suka girmewa Ummi. Suka shiga ciki don gaisawa da mutanen gidan kafin su wuce wajen fatin.
Husna zata bisu Fati ta janyota ta dawo baya.
"Wai wane group da wanne ki ke fad'a?"
Dariya Husna ta yi, akwai yar Taskira, su Neena su sholingaye su Aisha da Sadiya, akwai yan Rof gaba dayansu wasu ta gidajensu zasu je, da yan Classic Ladies ga Matan Aljanna da Matan Aure Only, da Matan Aure na antinmu Amina Mamser, ban rageki ba, kaf yan Dm masoya labarun soyayya mazansu da matansu kalilan ne bazasu ba wato tsoffin haka ma yan group din khalisat da..."
"Ke ya isa, wallahi kinsa na kara jin son halartar fatin nan, Angon ma nafi dokin gani, kai Ummi ta godewa Allah wallahi, mutane ai rahma ne."
Dariya Husna ta yi.
"Muje mu karasa shirinmu Madam."
Suka rankaya ciki.
Wajen takwas aka soma tafiya, saida aka ragu sosai Ango ya iso daukar Amaryarsa....!
[2/5, 3:45 PM] +234 703 962 5239: DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
118