← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 116

Sashe 7

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

 Wani ajiyar zuciya Ummi ta saki ganin yanda aka k'awata farfajiyar gidan da shukoki, wurin motocin da ta hango acan wata 'yar rumfa ta ga sun nufa suma, saidai bai karasa ba ya faka.  Duk suka fito, sannan ya karasa ciki.
  Suna gaba tana binsu a baya hannunta rike da Fahad wanda zuwa yanzu ta saba da shi ba kad'an ba kasancewarshi yaro mai son mutane. Banda kalle-kalle babu abinda takeyi har suka iso wata kofa da kai tsaye ta sadasu da wani dan karamin tsakar gida wanda aka dan yi gewaye a tsakiyarsa aka dasa shukoki. Ihun da ta ji ne ya katseta, wasu yan mata ta gani sun rungume Ihsan yayinda shima Adnan ya hau cafkewa da wasu maza a karshe suka hau rungumar juna ana dariya. 
   'Wadannan kuma su wanene?' Ta wurgawa zuciyarta tambayar, bata kai ga gama tantancewa ba ta k'ara ganin wasu yanmata biyar suma sun fito  suna fadin oyoyo Anti Mami. Ukun dai ta sansu, da Intisar ne da Rukayya da kuma Maryam yaran Hajiya Mama, biyun ne dai bata sansu ba duk kuwa da cewar sun had'u a sunan Aisha. 
  Bayan sun kammala rungume-rungumensu ne suka dunguma zuwa ciki gaba daya. Ihsan ta juyo da sauri ta matso daidai gefen Ummi. Tana dubanta duba na raini tace.
  "Saura kiyi karambanin biyomu, ki nemi wuri ki zauna anan."
  Ta amsa da toh sannan ta ja baya ta fasa niyyarta na binsu. Bayan shigewarsu ta koma can gefe ta ja kujerar roba daya cikin hudun da ke zagaye da tebur ta zauna ta zabga uban tagumi. Ko kusa bata ganin laifin Ihsan, daman ai ita ba wata bace a wajensu face  yar aiki, dole ne kuma ta cigaba da amfani da nasihun Antinta gudun abinda zai jawo a dizgata gaban mutane. 
  'Dizgi?' Ta  tambayi zuciyarta, toh kuma dizgi ya wuce wanda ta gama sha awajen shakikanta wadanda su kadai ne zata iya bugun kirji ta kira a matsayin nata? Sun gujeta sun manta da ita, tunda suka kawota har gashinan ta kusa yin wata a garin da babu iya babu baba, a wajen mutanen da bata da had'i da su sai na Allah. Bata kara sanin tayi rashin uwa ba sai bayan ta soma zuwa makarantar islamiyya, yanda ake kara koyar dasu gami da nuna musu muhimmancin biyayya ga iyaye. Ita kam bata da wannan gatan, har fargabar ranar da Hajiya zata gaji da ita ta koreta daga gidanta takeyi, tana rantsuwa da Allah batasan hanyar da zata bi ta koma garinsu ba a karan kanta matukar ba Yaha ce zata zo ta maidata ba. 
  Daddad'an kamshi da kuma zazzakar muryar da ta tsinta awajen ne ya katse mata tunani, ta d'ago kanta tana duban mai ita. 
   Tsaye yake ya zura hannunsa na hagu acikin aljihun wandonsa, hannun damansa kuwa, waya ce wacce ya kafa a kunne. Farin bafulatani ne, kansa cike da suma, saje a kwance saman fuskarsa yayi luf-luf. Yana da matsakaicin tsawo,hakanan yana da fadin fuska kadan, idanuwansa daidai misali hakanan siririn karan hancinsa da tsukakken le66ansa ruwan hoda, ya kara taimakawa wajen fiddo da tsantsar kyawun halittar da Allah Ubangiji Ya mishi. Sanye yake cikin shadda ruwan k'asa, kansa babu hula, agogon daya d'ora a hannun hagunsa ya kara fiddo da kyawun hannunnsa wanda ke cike da gargasa.
  A tsanake yake fidda kalmomi, hausa da turanci kawai yake gwamutsawa, idan yayi hausa, can gaba kuma ya jefa turanci, abin sai ya burge Ummi. Tayi shiru ta zubamasa ido tana sauraron yanda yake hada yare biyu lokaci guda duk da cewa ta sha jin hakan daga Ihsan, saidai ko rabin kwarewarsa Ihsan batayi ba. Daidai lokacin da yayi sallama da wanda suke wayar da shi, suka had'a ido, babu shiri tayi gaggawar janye nata idanun daga gareshi. Koda ta k'ara d'agowa, bata ganshi a wajen ba don tuni ya koma ciki. 
   Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuno da 'yar ajinsu wata Khadija, wacce bata da aiki sai hirar samari a aji, burinta bai wuce ta samu namiji kyakkyawa kuma mai kudi ta aura ba. Har mamaki suke bata, duka-duka tasan da wuya idan suma zasu fi shekara goma sha biyar kamar ita(GYARA) amma har ace sun waye da batun samari har haka, sai kuma ta tuna da cewar da ace a kauyensu ne da tuni watakila itama an aurar da ita. Abin kuma sai ya sanyata murmushi, wa zai aurar da ita? Ai kenan ma  Saude ta nunamata gata, akan kunnenta ta sha jin tana fadin saidai ta karar da rayuwarta a bauta mata, aure ne saida ta ga ana yi ba dai ita tayi ba. Hawaye ta ji suna kokarin taho mata da takaici, gaskiyar Saude tunda yanzun ma gatanan acikin hali na aikatau wanda duk a sanadinta ne, kudin da ta riga tasan na amfaninsu ne banda ita. An barta dai da wahalar.
  "Kamota nan!"
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

11

Firgigit ta dubi wanda ya tsoratatan don gaba daya ta zurfafa cikin tunani. Ganin Amina yasa ta mikewa tsaye da mamaki, sai kuma suka hau dariya.
"Kai Ummi, tunanin me kikeyi haka wai?"
Ummi wacce ta kasa rufe bakinta don tsabar murnar ganin Amina ta amsa da fad'in.
"Bakomai, kikacemin ba zaki zo ba?"
Amina dauke da murmushinta na sabo tace.
"Wallahi ban saka ran zanzo ba, Hajiya Mama ta matsamin akan na biyosu kawai."
Abin ya bawa Ummi mamaki, ta kara gaskata cewa Hajiya Mama ba ruwanta.
Amina ta dubi ledar hannunta.
"Ina zuwa bari na mikawa Anti Rahila famfas nazo."
Daga haka ta shiga ciki da sauri ta nufi ciki. Ummi ta koma ta zauna ranta yayi fes cike da murnar sake haduwa da Amina wacce ta dauki matsayin Anti kacokam ta bata ba don komai ba sai don yanda ta nuna kauna gareta a farkon haduwarsu da kuma yanda take da kokarin yi mata gyara aduk lamuranta na rayuwa. Bata jima da shiga ba sai gata kuma ta fito, tana kokarin jan kujera ta zauna ne ta dubeta.
"Meyasa baki shiga ciki ba?"
Ummi ta zaro ido kadan.
"Ciki kuma? Um um, Ihsan tace kada na sake na shigo."
Amina ta ja guntun tsaki.
"Bansan sadda yarinyar nan zata dawo saiti ta gane cewa shima dan aiki mutum ne ba. Ki dai kara hakuri."
Murmushi kawai Ummi tayi.
"Anti 'yan Abuja ma sunzo ne?"
"Su ai tun jiya suna garinnan, basu je gidan Mami ba kenan? "
Ta girgiza kai.
"A'a."
"Sunzo, Ikram, Baraka, Yaya Usman, Yaya Ridwan, Yaya Haidar da kuma Yaya Faruk."
Jinjina kai kawai Ummi tayi batare da tace uffan ba.
Sai kuma suka fad'a hirar da ta shafesu, sun jima sosai anan kafin kuma wata dattijuwar mace ta leko.
"Ke Amina, kuzo ku taimaka mu kaiwa bak'i abinci."
"Toh Larai."
Ta dubi Ummi.
"Muje."
Ummi ta mike gaba daya sai ta ji wani nauyi, kamar kada ta je haka take ji, fatanta kada Ihsan ta ci zarafinta a bainar jama'a. Takalma baja-baja a dan koridon shiga falon, suka shiga da sallama. Saidai abin mamaki bata ga kowa anan ba sai ta dunga jiyo muryoyi da dariyarsu daga can sama, hakan ya tabbatar mata suna can. Zugui-zugui tayita bin Amina har zuwa wani kicin mai girma. Nan taga kuloli manya guda hudu sai tarkacen filettoci da cokula da kofina a saman teburin dake tsakiyar kicin din.
"Yauwa ku soma kaiwa, Amina ga ledar nan ki soma da shinfid'ata."
"Toh" kawai Amina tace sannan ta ja linkakkiyar ledar ta hada da filas guda d'aya, itama Ummi ta dauki filas d'aya don girma ne da su, ta bi bayanta suka soma taka bene.
★★★★★

Wani sanyi da daddadan kamshin (roomfreshner) ne ya soma yi musu marhabin kafin dariya da hirar jama'ar falon ta doki kunnawansu. Suka shiga da sallama, Ummi gabanta banda bugu babu abinda yakeyi. Ga wadanda kunnensu ya ji suka amsa musu sallamar, wadanda basu ji ba kuwa, sai hira suke.
Babban falo ne wanda ba'a cikashi da kayan ado sosai ba, saidai iyakar wadanda aka dan kawatashi da su masu kyau da tsada ne. Kujeru masu jikin leda farare tas ne zagaye a tsakiyar falon, iyayen na zaune saman kujera harda dattijon kwarai, wato maigidan Alhaji Atiku Modibbo, tare da uwargida ran gidansa, mahaifiya ga Hajiya Fatima, Hajiya Madina da karamarsu gaba daya wato Hajiya Sadiya(Hajiya Mama).
Sune a zaune saman kujera, su kuwa jikokin suna a kasan tattausan kafet din dake shimfid'e a tsakar falon. Kallo d'aya Ummi tayiwa 6angaren da suke tayi gaba ta bi bayan Amina zuwa inda ta nufa. Tsakiyarsu ne Amina ta shimfid'a katuwar leda ta cin abinci, suka ajiye komai anan. Anan ne ta ji Amina ta shiga gaishesu, itama ba shiri ta gaishesu. Ba zata iya tantance wadanda suka amsa ba da kuma wadanda basu amsa ba don kuwa sauri takeyi su bar wajen, haka kawai ta kara jin ta raina kanta, ji take kamar wari takeyi ma tsabar kamshin wajen. Cikin yaren fulatanci ta ji wata cikin yanmatan tayi magana da bata fahimci ko menene ba. Gaba daya matasan suka dara, tana ganin sadda wani a samarin ya jefamata filo.
"Baki da kirki."
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

10
Chapter 7 · 0% Book details