← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 116

Sashe 111

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

   Kamar wasa, aka tsayar da maganar auren Ikram da Gidado wanda takanas iyayensa suka zo Abuja nema mishi bayan an samu an shawo kan Hafsa dakyar wacce ta dage akan saita bar gidan Gidado ta ya ya zai hadata kishi da wayayyiya kamar Ikram? Acewarta wannan cutarwa ce, da dai ya auri Ikram gwara ya auromata yar kauyen Jar Kwami irinta sun zauna. 
   Wasu cikin yan uwa suka goyi bayanta wasu kuwa ba su goya ba, hakanan a cikin dangin Gen. Ahmad Danzaki, wasu da yawa basu amince ba, acewarsu Ikram ba zata iya rayuwa a kauye ba da kuma dan kauye, ita kuwa ta dage lallai sai Gidado, to Daddy shima ya goyamaya baya ko babu komai autarsa ce yana ji da ita. Haka aka tsaida auren Ikram da Gidado wata uku ba da son ran wasu ba. 
     Aka shiga shirye-shiryen bikin Abubakar da Ihsan, sai Iklima da Musaddik, mijin da Abba ya za6ar mata akayi sa'a sun hada kansu, da kuma kanwarsu Hassana da Abdullatif. 
   Biki ya yi biki, dukkan yan uwa sun iso Kano, ciki harda KB wanda ya zo hutu daga Ghana, gaba daya ya chanja ya zamo na kirki kamar ba shi ba. Ummi ce ta samu dakyar Faruk ya amince da zuwanta, acewarsa cikinta ya tsufa babu yawo....!
    Ansha shagalin biki su Abida da sauran yan uwan Gombe na Jar Kwami duk sun hallara. Sai nan nan Hajiya Salma ke yi da Ummi, hakanan duk motsi da zata yi sai an tambayi ko akwai wata matsala. 
   Tana zaune ta sanya kayan ankon Party a gaba tana kumbure-kumburen fuska, Ikram ta dubeta.
"Allah Sarki Antina, yanzu shikenan ba za ki je ba?"
  Dariya su ka sanya gaba daya wanda ya kara k'ular da ita. 
  "Tana gani zamu wuce amma ba inda za ta je tunda Oga ya hana."
Cewar Baraka kenan. 
"Ke banda abinki, kina fama da wannan katon ciki haihuwar yau ko gobe ina ke ina wani dinner party?"
  Ta yi narai-narai da fuska.
"Nasan da wanda zan hadashi ai, bari na kira Yayana."
Sukayi dariya, ta kira Abubakar.
"Innota ya akayi na ji muryarki na rawa?"
  Daman kiris ta ke jira kawai ta soma kuka. 
"Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun, me akayi? Kinga kina ina yanzu?"
"Dakin Ihsan."
"Ok ina zuwa."
Ya katse kiran Faruk dake zaune gefensa a benci ya dubeshi.
"Me ya samu Innontaka?"
"Bari na je na gani."
Ya bi bayansa da kallo kafin ya ta6e baki don yasan zancen bai wuce na party ba.
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

128
Chapter 111 · 0% Book details