Sashe 39
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
55
KANO
Mami ta yi mamakin chanje-chanjen da ta gani wajen Mijinnata. Abin mamakin bai wuce yanda ya dage akan lallai su bata girkinta ba. A ranar kuwa suna isa ita ce ta shiga fadarsa. Saboda Fahad, Ramma ta kwana a gidan kasancewar yaranta suna kauye ziyarar dangin ubansu.
Ta sha rok'o a wajensa akan ta yafemishi har ta gaji domin duk da nunamishin da ta yi komai ya wuce, bai iya sakin jiki ba. Ranar kam komai ya yi lafiya, ya sanarmata haka kawai ya soma tsintar kansa cikin halin tunani da kuma tsananin kewarta.
Tsakanin mata da miji dai sai Allah, a wannan daren suka dinke har ma ya nemi kiran d'ansa don ya dawo ya soma shirin tafiya karatunsa.
'Babu abinda ya fi karfin Allah.' Shine abinda Mami ta fad'a a zuciyarta cikin murmushi lokacin da ta saci kallon fuskar mijinta ta ga annurinsa ya dawo ba kamar da ba.
*** *** ***
ABUJA
Misalin karfe shida a gaggauce ya kammala shirinsa ya fice zuwa aiki ko karyawa bai tsaya yi ba.
Ummi tun misalin takwas suka soma ayyukansu, ta yi gyararrakinta tsaf, Binta itama ta kama nata. Hajiya Babba ta yaba kwarai da gyaran Ummi. Koda ta shigo ta iske falon kyal-kyal tana(mopping) ta kalli wajen kafin ta amsa gaisuwarta da murmushi dauke saman fuskarta.
"Eh lallai, dole Madina ta so zamanki wajenta, ashe haka kika iya gyara? Lallai kam na yaba miki Ummi."
Wani murmushi ta yi har kumatunta saida suka lotsa, kwarai ta ji dadin wannan yabo da ta samu. Hajiya Babba ta yi dakinta, nan ma an kyalkyaleshi tamkar ba'a ta6a kwana cikinsa ba. Komai tsaf, hakanan ta ga bambancin aikinta da na Sa'a kwarai.
Ummi duk jikinta babu dadi, duk da cewar tana son gujewa Adnan, rashin had'uwarsu a kwana biyunnan yana damunta, batasan dalilin son sanyashi a kwayar idanunta da ta ke yi ba. Hankalinta ya kai ga tafkekan hoton matasan yaran Hajiya Babba. Dukkansu sanye suke da shadda ruwan k'asa tazarce, ta sha surfani mai tsada. Hularsu mai surkin ruwan k'asa mai duhu da marar duhu, a tsaye sukayi hoton a farfajiyar wani (hall), daga hotunan bayansu za ka tabbatar cewar a wajen wata walima ne.
Ta kauda idanunta gami da sauke ajiyar zuciya, duk cikinsu babu wanda yafi haskakawa a idanunta kamar Faruk, ko don shi zuciyarta ke so ne?
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
54
A wannan ranar dakyar ya jure suka kammala suka tashi, a hanya Magriba ta riskeshi haka ya karasa gidan ya yi fakin duk jiki a sanyaye. Bai zarce ko'ina ba sai sashensa. Saida ya yi sallah ya watsa ruwa ya sanya bak'ar jallabiya a saman gajeran wandonsa sannan ya yi niyyar shiga cikin gidan. Hankalinsa ya kai ga Adnan wanda ke kwance saman gado yana danne-dannen waya. Yatsun k'afarsa na hagu ya ja wanda ya tilastawa Adnan yin gefe da wayar yana mai sakin k'ara lokaci guda kuma da dariya.
"Kai my best."
Faruk ya murmusa kadan.
"Baka da aiki sai(chatting) kwanakin nan, ya dace na soma haramar kora ka makaranta naga ta (chatting)."
Dariya Adnan ya cigaba da yi. Faruk ya zura silifas dinsa ya fice zuwa sashen Hajiyarsa.
Bayan saukowarsa daga bene saida ya tsaya cak yana k'arewa hanyar dakunan yan aikin kallo, yasan Ummi zuwa yanzu ta yi mishi nisa. Ya sauke ajiyar zuciya gami da juyawa ya cigaba da tafiyarsa.
A falo ya iske Ikram da Ihsan suna cin abinci suna hira. Ganinsa yasa duk suka dubeshi suna mai amsa sallamarshi. Yana duban Ihsan da mamaki ya jefamata tambaya.
"A'a, baku wuce ba?"
Ihsan cikin kashe murya ta ce "No sun wuce, ina nan sai bayan sati biyu zan koma."
Bai wani ji dadi sosai ba, zaman Ihsan takura rayuwarsa kawai ne, ba yau ba ya soma lura da take-takenta, shi din ya kasance mai saurin fahimtar masu nunamasa so haka. Yana sane da Iklima ma, sai yanzu ne ma ya fahimci ta dan kwana biyu bata mishi koda sallama ba a whatsapp ballantana kuma akai ga kira.
"Ok." Shine kawai abinda ya ce sannan ya k'ara gaba. Ihsan ta bi bayanshi da kallo har saida Ikram ta zungureta.
"Kin shiga uku wallahi kedai, nikam har na daina mamaki."
Ihsan ta yi murmushi.
"Me kike nufi?"
"Ina nufin ki sanarmasa kina sonsa."
Ihsan ta zaro ido.
"Zubda aji."
Ikram ta yi kwafa.
"Tsaya kallon ruwa kwado ya yi miki k'afa."
"Wai kina nufin akwai wacce ya ke so?"
Ikram ta yi dariya.
"Bani da tabbacin hakan. Amma kada ki sake ki tsaya wani jan aji wallahi. Yayanki ne, koda zai wulakanta kowa banda ke."
Ihsan dai ta yi shiru ta cigaba da kai loma, maganar Maminta kawai ta ke tunanowa inda ta yita bata shawara akan ta yi kokarin jawo hankalinsa ta kissa.
Ya dan jima wajen Hajiyarsa har akayi kiran salla tukunna ya fito. Daga masallaci dakinsu.
Ya dan jima wajen Hajiyarsa har akayi kiran salla tukunna ya fito. Daga masallaci dakinsu ya wuce, can su Ikram suka kai musu abincinsu, har lokacin sam ba shi da masaniya akan Ummi na Abuja. Koda ya shiga wajen Hajiyarsa, bata sanarmishi ba.
*** *** ***
KADUNA
Wasa-wasa karamar magana ta zama babba, domin kuwa Deen da Dija soyewarsu sukeyi son ransu, saidai hirarsu ta fi a waya ko kuma idan sun yi sa'ar rana Munira bata gida. Tun ita Munira bata ganewa har ta soma zargin akwai wani abun. Kamar yanda Deen ke damuwa da harkar Dija sosai, abin mamaki har zuwa ta ke ta zauna a hau wasa da dariya da ita har ma su dinga wareta cikin hirartasu saidai ta yi shiru tana sauraronsu.
Dija da kanta ta bawa Deen shawara akan lokacin komawarta gida ya yi idan har da gaske ya ke sai ya turo magabatansa. Alokacin ne kuma ya yi dumm, ya dubeta.
"Kina ganin hakan bazai janyomin matsala da Munira ba?"
Ta ji haushin furucinsa, ta fahimci koda asiri ya ci shi akanta, tofa baisa ya mance da matarsa ba. Ta nunamishi idan ba zai iya aurenta saboda matarsa ba, shikenan. Anan kuma ya hau bata hakuri suka ajiye maganar yanda za'a 6ullowa lamarin.
Kwanaki biyu da yin maganarsu ta tattara ta koma Ringim, Munira ta ji dadin tafiyarta don Allah shaida ta soma tunanin akwai wata alak'a tsakaninta da maigidanta wanda bata fatan zatonta ya kasance gaskiya. Ta rik'i Dija yar uwa haka kuma da zuciya daya ta ke zaune da ita. Koda zasu rabu, tayi mata kyauta ta sutura da abin hannu, idan kuma zaa hada da wanda Deen ya yi mata, to fa ba komai bane.
*** *** ***
RINGIM
"Lale da 'yan Kaduna. To, saukar yamma ce?" Baba Habiba ta fada tana mai dan tafa hannuwa kamar kawata Bingel a fagen nanaye (LOL). Dija ta sakarmata jakar kayanta ta kar6a da gaggawa tana mai k'arewa diyartata kallo da dumbin mamakin yanda akayi ta chanja, wani k'iba ta k'ara da kyau.
Sai da dare bayan sun zauna ne suna 'yar hirarrakinsu, wayar Dija ta k'ara daukar k'ara a karo na biyar tun shigowarta gidan. Baba baki bude ta ke dubanta, ta rasa inda zata tsoma ranta don tsananin murna, ga dukkan alamu dai diyarta ta samu saurayi dan birni, lallai ba zasu yi sake ba.
Bayan Dija ta ajiye wayar ne ta dubeta.
"Ya sunansa?" Dariya ma tambayar ta bawa Dija, bayan ta gama kyakyatawa ta ce "Wa kenan?"
Baba ta girgiza kai.
"Ke bafa za muyi sake ba, fadamin sunansa mu k'ara kamashi a hannu yanda bazai ta6a iya su6uce mana ba kafin zuwa lokacin da za'a tashi aurenku muyi shiri na musamman."
Wani murmushi Dija ta saki.
"Zahraddeen sunansa."
Baba ta zaro ido waje.
"Wanne kenan?"
Babu ko d'arr ta amsa.
"Zahraddeen dai da kika sani, mijin Munira, shi nake so kuma ya ke sona."
Baba ta yi tsit, Dija tiryan-tiryan ta labartamata ire-iren hidimar da yake mata har da kyautar kudi dubu talatin da ya yi mata da za ta taho ya kuma siyamata sabuwar waya tana nan cikin kayanta. Har ma da yanda suka ajiye magana da shi akan zai zo neman aure. Bayan ta kammala bayanin ta fiddo kudaden ta damk'a a hannun Babarta, ta zaro kwalin wayar shima daga jakarta tana mai nunamata. Baba Habiba ta zurawa kudin ido da wayar kafin ta washe baki.
"Ke Dije! Wadannan yanzu duk mallakinki ne? Shakka babu daman bokanya ta tabbatar min idan mijin aurenki ya zo za muyi mamaki gashinan tun ma ba'a je ko'ina ba na soma. Abun yi yanzu, gobe zan koma gidan bori na ji yanda zamuyi ayi komai cikin salama batare da ansamu matsala ba, don ta ubanki mai sauki ne, sai yanda nace."
Wani ihun dadi Dija ta saki gami da rungume mahaifiyarta.
"Shiyasa nake bala'in sonki wallahi Baba."
Suka yi dariya, nan suka soma shawara kan irin k'ulle-k'ullen da zasu sanya ayi bayan auren. Ko kusa Dija bata sanarmata komai akan Raihana ba gudun yanda zata yiwa kallon abin.
*** *** ***
KANO
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
56
Har Ummi ta yi kwana biyu a gidan, Faruk ba shi da masaniya don gaba daya aiyuka sun mishi ca a ofis. Ba shi ya samu kansa ba sai ranar Asabar. Ranar kam ya sha bacci, bai farka ba sai sha daya. Kai tsaye wanka ya fad'a, bayan fitowarsa ya shirya cikin t-shirt fara tas da wando na (Adidas), bak'i mai surkin fari kadan sannan ya zura silifas ya nufi sashen mahaifiyarsa.