Sashe 87
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Ba kai ake gaisarwa ba?" Cewar Hajiya.
Ya yamutse fuska kadan.
"Lafiya."
Ya mike.
"Hajiya bari na je na dawo."
"Aa, to ka tafi da ita mana kawai. Tunda duk hanya ne."
Ya runtse ido kadan sannan ya yi gaba, Hajiya ta dubeta.
"Tashi ku je."
Ummi wacce duk jikinta ya yi sanyi, ina laifin mai sonka? Ta ji haushin kanta na 6atawa Faruk rai, mutumin da ya so ta tun kafin ta zama 'yar gayu haka, tun tana matsayin 'yar aiki. Sam bata kyauta ba, Faruk bai cancanta ta dunga 6atamishi rai haka ba.
Ta iske tuni ya fiddo motar yana jiranta, ta karasa kanta a k'asa, ta bude gaban mota ta shiga, sanyi da kamshi ya doketa, garin ya yi sanyi hakanan babu rana kamar zaayi wani ruwan. Ta rufe kofar gami da satar kallonsa saidai ko inda take ba ya kallo, fuskarsa babu digon walwala, gaba daya haushin kanta ya kamata, suka soma tafiya nan ma babu alamun zai shiga harkarta, wannan ne dalilin da yasa ta daure ta soma magana dakyar.
"Yaya Faruk."
Bai amsa ba hakanan bai kalleta ba. Ta sunkuyar da kanta idanunta suka ciko da ruwan hawaye, ta dubeshi cikin rawar murya.
"Yaya Faruk don Allah ka yafemin."
Ya lumshe ido ya budesu yana mai duban gefen da zai yanka kwana, can cikin zuciyarsa babu dadi, ji ya ke tamkar ya janyota ya rarrasheta, ko kusa ya tsani kukanta.
Ita kuwa ganin ya yi shiru yasa ta kauda kanta ta maida dubanta ga gefenta tana sharar hawaye. Shiru ya biyo baya har dai suka isa.
Daidai Islamiyyar ya tsaya, dalibai har sun shiga wasu kusa na tsaitsaye a k'ofa, gaba daya suka zubawa motar ido don ganin wanda zai fito. Ya cire (Lock), bata dubeshi ba ta bude kofar ta fita bayan ta share fuskarta.
Haka ta shiga ciki, mintuna uku da shigarta suna tsaye wata Malama na tambayarta ko ita sabuwar daliba ce, ya shigo. Gaisawa ya yi da wani Malami sannan ya yi ciki zuwa ofishin headmaster bayan ya yi mata umarnin ta biyoshi. Nan ya bada hakurin rashin zuwanta na tsawon lokaci, ya nuna babu komai. Aka sallameta ta fito, da isarta kofar ajinsu suka hadu da Husna da wasu.
"Lah, ashe dagaske ki ke Fati, Hasiya ce."
Cewar Husna kenan, Ummi cikin rashin fahimta ta dubesu, saidai kafin ta ce wani abu, ta ji suna duban bayanta wata na fadin.
"Gashinan wallahi, wayyo Allah, very handsome, please Hasiya ki hadani da shi, wallahi yayanki ya min, kalar mijin da nake fata kenan."
Cewar wata Shukra Aminu.
Wani mugun kishi ya turnuk'e Ummi, ta juya ta dubi Faruk sa'ilin da ya ke kokarin sanya kansa a waje ya fice. Sanye ya ke da bak'ar t-shirt bodyhug wanda ya taimaka wajen fiddo da kyakkawar halittar da Allah Ya yiwa jikinsa na kirar karfi, sai farin wandon jeans da ya sanya, sumarsa kwance luf, bak'ak'irin kamar mai sanya (hair dye). Ta juyo ba ta ce uffan ba ta nufi ciki, tana jinsu suna kod'a mijinta saidai bata da bakin magana.
Gaba daya suka biyota ajin. Husna ke tambayarta game da Gombe, su kuwa tambaya suke akan Faruk, duk sun isheta, Allah Ya taimaketa Malam ya shigo ajin, wannan yasa duk aka nutsu.
Ranta a matukar 6ace ya ke, har aka fito sallah basu bar bibiyatar da son jin ko wanene ba, tana tsaye bakin famfo tana daure dankwalinta, jiran Husna ta ke yi ta idar su bar wajen, idanunta ya kai ga Ikram suna nufo famfon ita da tawagarta. Ba shiri ta ja hijabinta ta rufe fuskar gami da basu baya, saidai duk da hakan bata tsira ba Ikram ta ganta, saidai bata ko nuna tasan da itan ba bisa gargadin Haidar wanda ya gargadeta sosai akanta. Dogon tsaki ta ja kawai wanda Ummin ta ji, daidai lokacin ne kuma Husna ta kammala ta dubeta.
"Mu tafi."
Suka bar wajen zuwa masallaci. Zuciyar Ummi ko kadan babu dadi har aka tashesu, direba ya dauketa.
A farfajiyar gidan suan fakawa ta fito, idanunta ya kai ga baranda Gogannata. Yana makale da earpiece a kunne, hannunsa na hagu lemun gwangwani ne da ya ke kur6a, sai sketct-board a gabansa yana zane. Ta dubeshi sosai, ganin zai kallota ne yasa ta saurin k'asa da kanta gami da soma tafiya zuwa ciki, ta goge kwallar da ta tahomata. Wannan cutarwa ne, ba zata jure wannan fad'an nasu ba. Ba haka ya sabarmata ba a mu'amalarsu.
Bayan sun gaisa da Hajiya, ta shiga ciki ta watsa ruwa ta sauya kaya zuwa riga da siket na Atamfa mai fari da (orange), bata daure dankwalin ba saidai kawai rufashi da ta yi. Fita ta yi zuwa kicin wajen Binta. Anan ta zauna, Binta ta yi akan ta ci abinci saidai ta ce ita sam bata jin yunwa duk kuwa da irin yanda ta ke jin yunwa na addabarta saidai damuwarta na rashin ganin fuskar Faruk yafi komai damunta. Tana daga kujera yar tsugunno suna hira da Binta. Anan ta ke bata labarin yanda suka yi da Ikram. Dariya sosai Binta ta yi.
"Duk yanda akayi ba banza ta kyaleki bata tofa ba."
Murmushi kawai Ummi ta yi wanda bai kai zuci ba, da ta ji hirar babu abinda ta ragemata sai ma k'ara hargitsata da ta yi don kuwa Binta ta sanarmata da zuwan matasan gidan da iyalinsu gobe, anan zasu wuni, duk sai ta ji hankalinta ya k'ara tashi, hakan yasa ta mikewa.
"Bari dai na dan zagaya."
Kai tsaye (Garden) ta nufa, zama ta yi saman lilo ta kwantar da kanta jikin igiyar, a sannu ta ke lulata tana tunani, rayuwarta na tafiya daki-daki, daga matsayin yar aiki zuwa ta surukar gida, har ta gangaro ga irin kyautatawar da Faruk ya yi mata zuwa ga yanzu da ta 6ata mishi rai.
Bata ji motsin zuwansa ba, saidai ji ta yi yana share mata hawaye.
"Yaya Faruk!"
Ta fada da sauri tana dubansa, sai kuma kunya ta kamata ganin dagaske ba mafarki ta ke ba shi dinne zaune durkushe gabanta yana dubanta.
"I'm sorry. Ki yi hakuri kinji?"
Ya fada cike da damuwa a fuskarsa, ta girgiza kai.
"Ni zan baka hakuri, don Allah ka gafartamin kada Allah Ya yi fushi da ni."
Ta burgeshi har baisan sadda ya dora gwuiwoyin hannunsa ba akan kafafunta yana mai dubanta.
"Sai kin chanjamin suna."
Ta rufe fuska tana dariya. Ya riko hannunta gami da mik'ar da ita.
"Oya, muje mu ci abinci."
Ta mike ba musu suka shiga ciki yana rike da hannunta.
Kusan tare suka ci abincin a falon Hajiya, Hajiyar na sama ta yi bak'uwa mai zuwa sarar kaya.
Suna ci daga zai bata a baki sai ta yi saurin kaucewa, har ya gaji ya bari, abin kan ta6a zuciyarsa, shi sam ba ya kaunar rayuwa haka, Yana yawan hangowa kansa rayuwa ta wayewa, baya kaunar kunyar Ummi ta cucesu a zamantakewa, idan har hakane, zata tauye musu jin dadi....
'((Nagode da adduoinku.. Allah Yabar zumunci..ameen))
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
105