← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 116

Sashe 26

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya tsaya gami da juyowa, ta tako har wajensa tana dubansa cike da tsananin tausayi.
  "Ka yi hakuri, bari naje ga mahaifinnaku."
  Ya girgiza mata kai da sauri, cikin tsananin fushi da daga murya ya soma magana.
  "Sai kiyita zuwa yana wulakanta mana ke Mami? For what reason?!! Idan har don ni za ki ki barshi, kudi da yace na dauka, ga wayata can da Laptop zan aiko a kar6a a siyar..."
  "Kasan abinda ka ke fad'a kuwa? To kada ka soma, na gayamaka ka tsaya bari na je ga Abbannaka."
  Mami ke maganar a fusace kafin a karshe ta sassauta, daga haka ta giftashi ta zura silifas dinta ta yi gaba, daman da mayafi jikinta, idar da sallar walha kenan ta zauna jin rediyo.
Mami ta isa har k'ofar sashen Abba cike da jin kwarin gwuiwa, hakanan ranta a tsananin 6ace, ayau ta gaji, saidai ayi wacce za'ayi kawai. 
  Ta murd'a k'ofar da sallama ta tura kai ciki. Rabonta da turakar maigidan nata wata daya da satittuka kenan, dariyar Abba da Umma ta katse sa'ilin da sallamar Mami ya ratsa dodon kunnuwansu. 
   Abba nan take ya daure fuska, ita kuwa Umma ta k'ara muskutawa jikinsa kai kace wata yarinya. A hankali ta tako, da sauri ya toshe hanci gami da dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.
  "Tsaya anan don Allah!" Ya yi maganar cikin tsananin fusata, ya d'ora da cewa.
"Wai Madina meyasa bakya ji ne? Inace na yi miki iyaka da sashena?!"
  Yana maganar ne kamar zai taso ya daketa ga hancinsa dake a toshe, itama Umman hancinta tosheshin ta yi. 
  "Alhaji agaskiya bazan iya zama ba, ku kammala maganarku tukunna."
Umma ta mik'e tana yamutsa fuska kamar gaske, ta shige d'aka, tana shiga ta la6e bayan ta gama kyakyata dariya tana sauraronsu.
   Mami ta sauke kanta k'asa tana mai fidda gwauron numfashi, DAN ADAM kenan mai saurin manta halacci, tamkar wani abu na kyautatawa a rayuwa bai ta6a wanzuwa tsakaninta da Mijinta ba. 
  Ba tare da ta dubeshi ba ta soma magana, domin kallonsa ma ayanzun kunci ya ke k'ara mata.
"Kayi hakuri, na sa6awa umarninka na shigo inda kayimin hani, saidai wannan karon ba zuwan kaina bane, zuwan 'ya'yana ne."
  Ga mamakinsa sai ya ga ta russuna k'asa.
"Domin Allah Abban Adnan, komai da zaka yimin kabar sanya yaranmu ciki, ka cigaba da kyautatamusu kamar yanda kakeyi a baya. Ni..."
  "Ke sauraramin don Allah!" Ya yi maganar cikin tsawa.
  Yana zaro ido ya jefamata tambaya.
"Wane abu makiran yaran naki suka ce miki nayi musu na wariyar launin fata?"
Ta daure ta ciji le66anta, dakyar ta cigaba da magana.
"Wani mugun zance naji, wai kana zargin Adnan da yi maka sata. A sanina kafi kowa sanin halayyar danka, bazai ta6a aikata hakan ba."
  "Toh, kenan kina nufin kice k'arya nayi mishi? Madina ba fa ko isa ki dunga koyawa yarana mugun hali har haka ba. Ki kiyayeni wallahil azim idan ba haka ba zan miki abinda ba ki ta6a zato ba ko a mafarki. Iskancin banza! Don kaza kazansa ni ban isa na hukuntashi ba? Da wannan mugun halin da ya koyo ne ya ke tsammanin zan turashi waje karatu ya lalata yaran mutane? To bazai ta6a yiwuwa ba wallahi, kuma ki amsomin dubu ashirin d'ina idan kuwa ba haka ba, karatun ma kwata-kwata ya jawa kansa bazai yishi ba."
   Daga haka ya mike yana cigaba da masifa kamar zai ari baki, a haka ya shige daki ya barta durkushe.
  Mami wacce tun ashar din da ya yi ta girgiza bata iya cewa uffan ba, ta jima anan ta kasa tashi don tsananin tashin hankali, dakyar ta iya mik'ewa ta zura silifas d'inta ta fita. Tana tafe zuwa sashenta tana juya maganganun mijinnata, zuwa yanzun ta k'ara tabbatarwa lallai akwai wani babban lamari. Watakil ko mijin ya soma hauka ne shiyasa abin ya kai har da zagi. 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

   39
  A falo ta tarar da Ummi da Ramma sunyi jugum, ta dubesu ta dauke kai tana waige.
"Ina Adnan?" 
Ramma suka dubeta.
"Ai kina fita ya wuce, inaga dakinsa ya shiga."
  Da sauri ta juya zuwa dakinnasa, babu kowa, ta lek'a bandaki nan ba bayanan, akan gadon ta ga takarda ta dauka ta warware ta soma karantawa. 
    "KIYI HAKURI MAMINA, WALLAHI BAZAN IYA ZAMA BA. KADA KI DAMU WAJEN YAYA FARUK NA NUFA WATO ABUJA, MAMI DON ALLAH AYI YANDA NACE, GA WAYOYINA DA LAPTOP A SIYAR A BAWA ABBA KUDINSA KADA KI BADA KWANDALARKI. IDAN NA ISA ZANYI KIRANKI."

  Jin haka yasa ta zauna d'abas saman gadon tana numfarfashi kafin ta soma hawaye. Shikenan farin cikin gidanta ya rushe, ta dauki wannan matsayin jarrabawa daga Allah, ta kuma tabbatar komai yana nan zuwa k'arshe. Hankalinta ya kwanta da jin inda Adnan ya nufa, ko babu komai zai samu kulawa hakanan tasan inda ya ke. 
  Bikin Baraka duka-duka sati d'aya ya rage, itama tana tunanin tattarawa zatayi ta tafi ko zuciyarta ta dan samu nutsuwa idan ta shiga cikin 'yan uwanta. 
   Ta linke takardar ta ajiye gami da kashe komai da ya danganci kayan wuta ta rufe dakin da mukulli ta fito.  

  Ta sanarwa su Ramma cewar Abuja ya wuce su kwantar da hankalinsu. Daga haka ta wucesu zuwa daki. Ramma ta girgiza kai.
"Oh, akace zato zunubi amma ina tunanin anya matannan na Alhaji babu sa hannunsu?"
  Ummi ta yi shiru cike da tunani, kuma mai yiwuwa ne saidai kamar dai yanda Ramman ta fad'a ne, wato zato zunubi ne, hakan yasa ta ja bakinta ta yi shiru batare da ta tofa nata ba.
  Koda su Ihsan suka dawo sunyi mamakin jin wai Adnan ya wuce Kaduna, saidai Mami ta nunamusu akan abinda ya shafi karatunsa ne. Hakan yasa suka hau murna da tunanin ko Abba ya sakko. 
   A ranar Mami ta saka Ihsan zuwa Atm ta ciro mata dubu ashirin ta kaiwa Abba. Ihsan dai bata da masaniyar ko ta menene, ta ji dai Abba na kiran 6arayin banza da wofi har yana dokamata harara. Sai bayan ta zo da korafin gaban Mami sannan Mami ta rarrasheta gami da nunamata kawai fad'ansa yakeji.

                   ***  ***  ***
   Hajiya Binta zaune a falon Hajiya Lubna (Anti Amarya) wacce ita kanta ta dan ji mamakin shigowarta don a yan kwanakin nan ta dauke k'afarta da shigowar, a cewar Anti Amarya ba don komai ta yi hakan ba sai don ganin ta samu kan Alhajin yanamata yanda ta ke so. 
   "Bakya ji dadi ba, na yanda Alhaji ya juyawa 'yar gwal dinsa baya?"
  Cewar Hajiya Binta kenan tana mai duban Anti Amarya wacce ke danna wayarta. Mace ce gwanin shan kamshi da yanga, shiyasa sau da yawa ta ke k'ular da Hajiya Binta, har a ranta tana yawan fad'in 'Da ace Hajiya Lubna ce ta samu kan Alhajin ba Mami ba, to da gaba daya sun kad'e, domin ta iya daukewa mutum kai ga wulakanci.'

"Ke kike ganin haka Hajiya Binta, saidai ni ban gano komai ba."
  Hajiya Binta ta yi mata wani kallo.

"Bangane nufinki ba?"
  Sai lokacin ta ajiye wayar ta dubeta da murmushi saman fuskarta.
   "Ba nasara a gaba Hajiya Binta, duk abinda za'ayi idan ba na Allah ba, babu inda ya ke zuwa, da dai anyi hakuri an cigaba da yarda da kaddara tunda shi wanda ya ajiyemun yana nunamana kulawa tsantsa da kauna. Amma ina tabbatar miki wannan ba abun murna bane, abu ne na lokaci k'ank'ani."

  Ta danyi shiru ta dora bayan ta gama lura da irin k'uluwar da Hajiya Bintar ta yi da maganganunta.

"Ina jiyemana ganin abinda yafi na baya tsakanin Muhammad da Madina anan gaba."
  A fusace Hajiya Binta ta mik'e.
"Ya isheni Malama, na lura ke kin daina damuwa da kayan takaicin da muke kuntsa. Shikenan ai, fatan da kikeyi ba dai ni na ganshi ba, saidai ko ke din. Idan kin k'ara ganina a sashenki ki gasamin wanda yafi wannan."
Fuu! Ta fice tamkar akan iska, dariya Anti Amarya ta yi gami da girgiza kai.
  "Za ki gani ganin idanunki Binta."
Ta fad'a a bayyane.

  Inda Hajiya Lubna ta fi Hajiya Binta kenan, tana da kokarin 6oye sirrinta hakanan bata kauna bin malamai tafi yarda da shaye-shayen magungunan mata, a wannan 6angaren kuwa saidai su tafa da Mami don bazata gwada mata ba. Saidai tasan kaunar dake tsakanin Muhammad da Madina, dad'add'iya ce wacce ko mutum ya yi yunkurin rabasu, to fa a karshe zai ji kunya matuk'a. Ta numfasa, tana da tabbacin uwarmijinsu bata da masaniya akan wannan sauyin lamarin, da tasan yanda d'an nata ya maida 'yar gaban goshinta, da tuni ta yiwa abin tufka.

                   ***   ***   ***
                     ABUJA
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Chapter 26 · 0% Book details