← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 116

Sashe 35

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Ban ta6a runtsuwa batare da na tunaki ba tun farkon ganin da nayi miki a gidan Grandpa (Alhaji Atiku Modibbo), ban kuma ta6a jin faduwar gaba aduk sadda na tuna wata diya mace ba sai a kanki, ban kuma ta6a gajiya da kallonki ba Ummi. Kin ga nan."
Ya yi nuni da kirjinsa, ta d'ago ido ta bi hannunsa wanda ya d'aurawa agogo na bak'in fata da zobunansa na azurfa biyu. Ta maida kanta ta sunkuyar har lokacin tsoro da firgici bai saketa ba. Faruk ya cigaba da magana tamkar ba muryarsa ba.
  "Koyaushe kina cikinsa, bansan kuma dalilin da yasa har abada bana fatan fitarki a ciki ba. Na rasa amsar abinda nakeji akanki, na baki yau zuwa gobe, ki taimaka ki nemomin amsa, zan nemeki."
  Ya yi shiru yana cigaba da kallonta ita kuwa ta kasa koda kallonshi. Har ta gaji da shirun ta dago ta dubeshi. Murmushi tattausa ya sakarmata wanda saida ta ambaci 'Subhanallah' a ranta adalilin kyawun da ya yi, bata ta6a ganin murmushi irin haka a wajensa ba, kallon ma na musamman ne Faruk ke jifanta da shi. Ta maida kanta kasa, ya daure fuska shima.
"Ki k'ara kula sosai Ummi, KB dan uwana ne don d'a ne ga cousin din Hajiyata amma ban aminta da ki kara shiga huldarsa ba duk da nasan cewa wannan karon tilasta ki aka so yi, ita kuma Sa'a barin gidan nan ya zamto mata wajibi, yanzun ma ba don dare ya yi ba, da a yau sai ta bar gidannan."
  Daga haka ya yi shiru, can kuma ya mik'e tsaye yana kakka6e jiki.
  "Kinga kin janyomin chanja kaya, fatin ma ba zan iya zuwa ba zan yi tsaronki."
Ita dai mamaki ya hanata cewa uffan duk da kalamansa sunyi mata dadi matuka saidai iyakar tunaninta ta kasa gano amsoshin tambayoyinsa. Hannun da ta ga ya mik'o mata ne yasa ta dubansa da sauri, murmushi ya sakarmata, wani yadi bak'i sidik yasa mai ratsin yellow, sai hula. Farar fatarsa ta fito ainun, ta mik'e batare da ta kama hannunnasa ba.
  "Saida safe. Ki kara kula please."
Bai kara sauraranta ba don yasan ba abinda zata ce ya juya ya fice domin zuwa kashe mota da kwaso wayoyinsa don dagaske ya ke jin tafiyar ta fice aransa. Ta bishi da kallo har ya 6acewa ganinta. Ta numfasa, sai kuma ta tuno abinda ya faru da ita yanzu, kai tabbas koda ta ji hirar su Sa'a bata ta6a tsammanin zata ci amanarta har haka ba ta yaudareta. Sai kuma ta tuno Antinta, ko me zata zarga akan dadewarta? Da gudu-gudu ta fito ta nufi dakinsu. Murdawa ta yi ta shiga, saidai kuma ta yi mamakin ganin Aminar na kwasar bacci, ta sauke ajiyar zuciya, watakil ta yi jiranta bata zo ba. Ta shigo gami da sanyawa kofar mukulli don gudun abinda zai kara faruwa da ita. Saida ta dauro alwala sannan ta rufe kanta ta kwanta lamo tana tunane-tunane.  A hankali kuma ta cigaba da kuka, ba don Allah Ya jefomata Faruk ba, da a yau kashinta ya bushe, da ta rasa mutuncinta na 'ya mace. Ji ta yi nan duniya ta tsani Kabir tsana tsantsa, shi kadai ne ya ta6a yin wannan yunk'urin a kanta, ta tuna sadda ya tsotsi wuyanta da sauri ta mike ta cire kaya ta je ta wanke jikinta don bai bar kamshin turarensa ba. Saida ta tabbatar kamshin ya bar jikinta sannan ta k'ara dauro alwala ta fito, saida ta yi nafila ta nunawa Allah godiyarta da Ya tserar da ita sannan ta yi addu'o'inta ta kwanta. Sai kuma sabon tunanin Faruk ya namayeta. Gani takeyi kamar a mafarki ba gaske ba, kamar kuma tana karanta litattafan hausa na soyayya da ake yawan yi na yan aiki da soyayya da dan masu gida. Ta runtse ido ta budesu, tabbas komai a zahiri ne, ya faru kuma a yau din, ga Faruk wai yana gayamata kalamai dad'ad''a har ya ke sanarmata yanda ya ke ji akanta bai ta6a ji akan kowace mace a doron k'asa ba. 
    Ta lumshe ido ta budesu don dadi, ya tabbata dai abu daya su ke ji.  A haka har bacci ya dauketa bata ankara ba.
     Washegari har ta farka ta yi sallah Amina bata motsa ba, abin har ya soma bata tsoro, karshe dai itama baccin ta koma. Amina dai bata farka ba har sai da gari ya yi haske, kanta ya yi nauyi, lokacin Ummi tana bandaki tana wanka, a ranar ne zaa kai Amarya gidanta misalin karfe hud'u. 
  Ta yi shiru da son tuna abinda ya faru can kuma ta tuno yanda Sa'a ta shigo kiran Ummi, da kuma hodar da ta shak'a mata bacci ya yi awon gaba da ita. Ai da sauri ta mike ta fita kan babu ko kallabi.
  "Ummi! Ummi!"
Yan aikin basu nan sun tafi ciki don kama ayyukansu, Ummi na jin muryar Amina ta fito tana gyara mazaunin daura kirjinta don ta kammala dama. 
  "Anti kin tashi?"
Amina ta waigo, ganinta yasa ta karasa a guje cikin tsoro tsantsa.
"Ummi, na farka, gayamin ina Sa'a ta kaiki jiya?"
  Ummi ta dubi hanya sannan ta kama hannun Amina.
"Ki kwantar da hankalinki, ki yi sallah zan ba ki labari."
  Ta tuna ko sallar asubahi bata samu damar yi ba, ta matsa Ummi ta wuce, sannan ta fada zuciyarta ta dan sanyaya ganin Ummin lafiya, amma tana son tarar Sa'a don ta ji nufinta.  
  Bayan ta idar ta dubi Ummi wacce ta ke sanya riga doguwa'yar kanti sabuwar da suka sayo, baki da orange ne adonta, ta yi kyau daidai gwargwado duk da ba wani kwalliya ta yi ba. Ta cigaba da addu'ointa sai bayan ta kammala ta shafa sannan ta juya ga Ummin.
  "Ki sanarmin, meyafaru jiya?"
Ummi ta soma bata labarin har tana zubda hawaye, itama Amina har hawayen saida ta zubar tana mai yin salati. 
  "Innalillahi... Wannan masifa da me ya yi kama? Ashe ba'a banza ba ta shak'amin hodar da ta fiddani a hayyacina."
Ummi ta zaro ido.
"Hoda kuma?"
Amina ta ja majina ta share hawayenta.
"Tabbas, hoda ta shak'amin duk don kada na yi wani yunk'urin, saidai batasan cewa ba Amina ke karewa ba, Allah Shi ke kare bayinSa kodayaushe. Wallahi tun farkon ganina da Yaya Faruk ya ke burgeni don alamu sun nuna yasan mutuncin DAN ADAM. Ba shi kadai ba, dukkan yaran Hajiya Babba haka suke. Ki k'ara yi mishi godiya Ummi don ba karamin taimako ya yi miki ba. Ita kuma Sa'a na tabbatar tunda har Yaya Faruk yace zai hukuntata, to babu makawa. Kb kuma ki k'ara nisantarshi, biki kuma ai ya k'are, nasan ba za mu k'ara kwana biyu ba za mu tattara mu tafi."
  Ummi ta jinjina kai, tana son gayawa Amina yanda sukayi da Faruk saidai tana tsoron abinda zata ce, a karshe dai bayan fitowar Amina daga wanka ta daure ta soma labartamata abinda Faruk yace. Amina na shafar mai bata ko katseta ba, haka kuma fuskarta bata nuna wata alama ta razana ba. Bayan kammala bayanin Ummi ta saki murmushi.
  "Ai daman nasan za'a rina!"
  Shine abinda ta fada wanda ya yi matukar razana Ummi har ta kasa daurewa ta kalleta, Amina ta jinjina mata kai alamar tabbas dagaske ta ke.
  "Eh, nasan ke da Faruk kuna SON JUNA, ganewa ne kawai bakuyi ba."
  Ummi ta dafe kirji ta zaro ido.
"So kuma?"
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Chapter 35 · 0% Book details