← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 116

Sashe 113

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

sosai babu damar gane hakan. Takalmin yana da tudu, ya isheta, hakan yasa ta zuwa daidai motar Haidar ta tsaya gamicireshi sannan ta soma kokarin dauka, saidai durkuso ya yi wuya agareta, ta kara kokarin durkusawa ta ji an rike kafadarta, a razane ta dubeshi, Faruk ne, ya durkusa ya dauki takalmin ya rike mata, kai tsaye ya wuce ya bude motarsa ya tayar, ya yo ribas ya saita kafin ya budemata gidan gaba. Sauke gilashin motar ya yi yana dubanta batare da ya ce uffan ba. Hawayenta suka zubo ta soma tafiya, ya kuramata idanu cike da tausayi, tabbas ya kula a gajiye ta ke, abinda ya gujemata kenan shine babban dalilinsa na dagewa kan ba zata zo ganin anyi kamu anyi yini duk tana faman zirga-zirga. Ta shigo ta zauna ta rufe kofar, ya soma ja a sannu-sannu har suka fita, saida ya hau titi kafin ya dan k'ara gudu. Ta dubeshi saidai ta kasa magana, a hankali ta soma kuka sosai harda sheshsheka, duk yanda yaso ya basar, ya kasa, dole ya sauka daga saman titi ya yi fakin a gefe. Dubanta ya yi na yan mintoci kafin ya soma magana cikin sanyin murya. "Meyafaru kuma?" Ta dan matso kadan ta dora kanta saman kafadarsa gami da rungume hannun gam. "Don Allah FAR HAS ka yafemin, na fito bada izninka ba kuma na yi abinda kishinka ya motsa, don Allah ka yi hakuri." Wani so da tsantsar tausayinta ya cikashi, shima yana cikin dakin taron ya dawo daga lik'i ya ga batanan hakan yasa shi fitowa a rude, karshe ya hangeta jikin mota. Ta ya ya zai iya fushi mai tsawo da Umminsa? Ya sanya hannunsa na hagu ya dafa kanta. "Kinmin laifi Ummina, saidai duk iyakar laifin da za kimin bazan iya rabuwa da ke ba saidai wata kaddarar da bana fatan ta rabamu idan har ba mutuwa dayanmu ya yi ba, ina kishinki Ummi musamman da Kb wanda ya kusan cin rabona." Ta dago kanta cikin marairaicewa ta ce. "To ka yi hakuri bazan k'ara ba." Murmushi ya yi ya ka karan hancinta. "Haka ake bada hakuri?" Ta yi murmushi. "A hanya muke fa." Ya share mata fuskar. "Muje ki huta, daman nasan bebina bazai jure wannan Dinner ba shiyasa na hana ki zo amman Abubakar ya nunamin ke yar uwarsa ce." Ya karashe da dariya, ta tayashi kawai. Haka ya cigaba da tafiya, ta koma kujerarta ya kwantar mata da kujerar kadan ta yi filo da hannunta tana dubansa yana tuk'i, a haka bacci ya yi awon gaba da ita don sosai ta ke jinsa. A waya Faruk ya sanarwa Abubakar sun taho Ummi ta gaji don ba wanda ya sani. Koda ya yi fakin, saida ya karemata kallo don ba don baccin ta ke ji ba da bai ci ace ta yi ba don tafiyar ba wata tafiya ce sosai ba. Ya shafi gefen fuskarta, hakan ya sanyata bude idanunta. Kyakkyawan murmushi ya jefeta da shi. "Mun iso." Ta mike, ya zagayo ya budemata, da taimakonsa ta zura takalmi ya rike fos dinta suka shiga ciki. A falon Mami duk an ragu babu kowa, wasu sun yi bacci, har daki ya kaita, nan ma yaran su Jidda ne duk sun yi bacci, ya dubeta. "Ko za ki dakin Fahad? Kinga nan ma a cike." Ta dubeshi ta girgiza kai. "Aa zan kwanta gefensu karka damu." Bai bar dakin ba saida ya tabbatar ta rage kayan jikinta ta chanja zuwa na bacci ta kwanta, ya sumbaci goshinta. "Goodnight." Ta lumshe idanu tana murmushi. "Kaima ka kwanta fa." "Aa, zan koma wajen budurwata." Ya fada a wasance, ta kai mishi bugu a kirji sukayi dariya. "Bakasan na ji haushin yanmatan nan masu yi maka lik'i ba ko?" Ya ja karan hancinta. "Na fiki kishi Madam, karki damu ke kadai zuciyata ke so da kauna. Oya kwanta." Ta muskutawa ya rufeta, sannan ya kashe musu fitila ya fice, Allah Ya taimakeshi babu wanda ya ganshi balle tsoffin su ce ya yi rashin ta ido....! Washegari da safe ya koma bakin aikinsa Abuja, a ranar aka kai Amaren biyu, Iklima da Hassana, ita kuwa Ihsan Adamawa zasu wuce washegari. Bayan Magriba Mami ta yi kiran Ihsan da Ummi zuwa sashen Abba ta rufe don samun damar yin maganar da ta ke so....! DAN ADAM @RUFAIDA OMAR
Chapter 113 · 0% Book details