Sashe 110
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
An soma bikin Amina lafiya, ana gobe daurin aure Malam Balarabe suka zo, sun sha hira da diyarsa har ya rasa inda zai sakata don tsabar farinciki. Ita ta yi musu jagora har wajen Inna don yi mata fatan alheri, wani abu ya darsu a zukatan tsoffin sadda suka yi arba da juna. Bayan an daura auren ne Malam Balarabe ya kasa jurewa har saida ya sanarwa Baffa kaninsa don daman ya samun labarin cewa yanzu Inna bata da aure, hakanan yana iya cewa tun bayan Hasiya babu wacce ya kara gani ya ji yana so ya karashe rayuwarsa da ita matsayin mata kamar Inna Bilkisu. Baffa ya ji dadi kwarai kuma zai so hakan. Abinka da batun manya nan suka tuntu6i babban Yayan Bilkisu, Mahmuda, nan ya nunamusu jin dadinsa a fili don kwarai ba ya son zaman kanwartasa haka babu aure duk da cewa ta aurar da yara biyu Fiddausi da Hauwa, sai Amina ta uku, ga kuma autanta Ahmad mai shekaru goma sha daya a yanzu, ya yi musu alk'awarin tuntu6ar Inna Bilkisu. A karshe sukayi musayar lambobin waya sannan a karshe sukayi sallama da kowa suka tafi, Ummi har hawaye ta yi don kewa, shi kuwa babanta dadin yanayin da ya ganta ya ji don ta yi k'iba ta kara kyau.
Inna ta ji lamarin banbarakwai duk kuwa da cewa a ganin farko da ta yiwa Malam Balarabe ya kwantamata, ba musu ta amince da hakan. Nan ya kira ya shaidamusu, basu yi wata wata ba suka sanarwa iyayensu, Malam ya ji dadi haka ma Dada wacce ke tausayawa dan nata. Aka tsaida magana nan da sati biyu za'a je a daura aure.
Su Anti Hauwa sun ji abin banbarakwai, wai Innarsu aure. Tun basu ji ko waye mijin ba suka nuna rashin goyon bayansu, acewarsu da shekarunta na arba'in da takwas me ya ragemata banda ibada? A bakin matar Kawunnasu suka ji waye manemin auren, hankalinsu ya kwanta suka ji dadi, kusan Amina ta fisu jin dadin lamarin don a take ta bugawa Ummi wacce ke shirin komawa Abuja.
"Albishirinki." Ummi ta ware ido.
"Goro fari k'al Antina."
"Inna zata zama matar Babanmu."
Cikin rashin fahimta ta ce.
"Anti inace kin cemin Baba ya rasu."
Ta ja tsaki.
"Dallah can, babanmu fa na Gombe."
Daskarewa ta yi a tsaye ta bar ninke kayan. Ita abin kamar mafarki haka ta jishi.
"Ke ya ki ka yi shiru, wallahi dagaske ne." Tiryan-tiryan ta labartamata abinda ta ji. Hawaye kawai Ummi ta shiga fitarwa tana kara jin kaunar Amina da yan uwanta. Banda hamdala babu abinda ta dunga nanatawa a fili.
Bayan komawarta Abuja ta sanarwa Faruk wanda shima ya ji dadi ainun, ya sanyawa lamarin albarka. Kowa ya ji sai ya sanya albarka ciki. Koda ta kira mahaifinta, dariya kawai ya yi ya ce.
"Lamarin Allah kenan Hasiya, a tayamu addua."
Farinciki fal cikin ranta haka suka sha hira suka yi sallama.
*** *** ***
BAYAN WATANNI BIYAR
Ayau ake bikin yaye su Ikram daga sakandire, acan Kano ma su Ihsan na nasu shagalin don lokaci guda aka yi bikin yayesu.
Duk yayyun Ikram sun je mata banda Baraka dake wankan jego ta haifi danta namiji wanda ya ci sunan mahaifin Mijinta suke kiransa da Abulkhair. Ummi ma da cikinta dan wata bakwai katon gaske haka ta zo. Fuskarta duk ta chanja, tana sanye da wata tsadaddiyar abaya Faruk na rike da hannunta.
Ikram duk bata tare da walwala sai lek'e-lek'en wuya ta ke faman yi.
"Wai me ki ke nema haka?" Cewar Fadila wacce ta kasa shiru. Ikram ta dubeta, kafin ta yi magana suka ji sallama a gefensu duk suka waiga, mamaki karara ya bayyana a fuskokinsu.
Yana sanye da doguwar riga da wando na shadda dark green wacce ta sha aiki, ya dora hula mai fari da koren din sak'a, ya yi kyau kuma ta haskakashi ainun. Sai murmushi ya ke faman dokawa.
"Yaya Gidado?" Ummi ta furta da tsantsar mamaki kafin kuma ta saki fara'a sosai.
Ya bita da murmushi kafin ya karasa ya soma mikawa Mazajen Hajiya Babba hannu suna gaisawa. Suma sun saki fuskokinsu, Fadila da Jidda suka yi turus suna kallon ikon Allah, sun kuwa gane waye shi amman idan ka ganshi saika rantse ba daga kauyen Jar Kwami ya fito ba tsabar iya daukar wanka.
Ikram ta kasa rufe baki, zuciyarta na kara nutsawa cikin kogin so da kaunarsa, babban abinda yasa ta ke kwadayi da mafarkin zuwan wannan ranar kenan don kuwa ya bata tabbacin zai zo mata da kyakkyawan albishir duk ranar da ta yi Candy. Toh yau ga ranar ta zo.
"Ashe kana tafe ba ka sanarmana ba mu yi maka kyakkawan tarba?"
Cewar Faruk cikin sakin fuska. Gidado ya danyi dariya.
"A yi hakuri surukina, ai gani yanzu ma bata 6aci ba."
"Lallai kam, saidai kamar zuwan ba namu bane na kanwarmu ne ko?." Cewar Haidar wanda ya riga yasan dawan garin daga Intisar., ya fada yana duban Ikram.
Suka yi dariya, kunya ta kama Ikram.
"Eh to, kusan hakan."
Cewar Gidado, shi kuwa babban Yaya da Ridwan mamaki sukayi don basu zata ba , hakanan Faruk shi kansa bai ji daga matarsa ba. Ya dan matse hannunta ta yi karamin kara.
"Shine ko ki gayamin?"
Ta waro ido.
"Babu wani abu fa tsakaninsu."
Murmushi kawai ya yi.
Har aka tashi taron Gidado bai samu ke6ewa da Ikram ba sai bayan sun koma gida, bayan ya gaisa da su Hajiya suka ke6e da ita a dakin bak'i.
Ya fiddo wani akwati daga aljihunsa ya mik'amata.
"Ga kyautar da na zo miki da ita, ki yi hakuri babu yawa.". Ta kar6a tana washe baki.
"A wajenka ne babu yawa."
Sukayi dariya.
"Ba za ki bini bashin zance ba Ikram, yau zan sanarmiki abinda ban ta6a sanarmiki ba. Haka kuma zan cika alkawarin da na daukar miki."
Ta lumshe idanu ta budesu.
"Ina jinka Yayana."
Shiru ya dan biyo baya kafin ya cigaba da magana.
"Karambanin so ke neman kaini inda aka fi karfina, duk iya kokarin da na yi na dannewa da kaucewa faruwar hakan, saidai ya gagara, bazan iya hana Allah zartar da hukuncinSa, ban isa ba ban kuma kai ba. Wallahi na kamu da sonki Ikram, so na gaskiya, a rayuwa ban ta6a zaton zan kara son wata diya nace ba bayan Hafsa, amma cikin ikon Allah da sannu-sannu kyawawan d'abi'unki da kuma hakurinki suka rinjayi zuciyata na afka cikin kogin son wacce ta fi karfin dan kauyen Jar Kwami."
Ta kasa motsi, ta kasa gaskatawa, ta kuma kasa tantance hakikanin yanayin da zuciyarta ta fada. Kallonsa kawai ta ke tamkar wata doluwa. Ya kai yatsa kamar zai tsone idonnata ta yi saurin lumshewa, sai kuma ta yi kasa da kai tana murmushi.
"Wannan kallon fa ya tsoratani, ko ba'a sona?" Ya fada don jin ta bakinta kawai bawai don baisan cewar tana sonsa ba.
"Bance ba, saidai na yi mamaki ne kawai ace kamar ka kana sona?"
"Kina neman ki ce kinfi karfina ko?"
Ya fada a raunane. Ta yi saurin girgiza kai kamar mai shirin kuka ta ce.
"Wallahi aa, ni don Allah ka daina bambanta kanka da ni, kaima cikakken DAN ADAM ne mai daraja, ina girmamaka hakanan ina sonka tsakani da Allah."
Ya murmusa gami da sunkuyowa saitin fuskarta cikin muryar rada.
"Za ki iya zaman aure da ni a Jar Kwami?"
Ta lumshe idanu gabanta na bugu da sauri-sauri.
"Yayana ba Jar Kwami ba, koda cikin daji ka ke rayuwa wallahi zan iya binka muyi zaman aure, ina sonka fa." Ta karashe kamar za ta yi kuka, ai kuwa hawayen da ta ke makalewa suka kwaranyo.
"Komai na Allah ne." Ta tuna furucin Ummi gareta a watarana da ta je gidanta da korafin yanda ta ke kara jin son Gidado a ranta kamar ta mutu.
"Idan Allah Ya kaddaro mijinki ne, za ku yi aure." Fadin Intisar a watarana suna hira ta ke kokawa bisa yanda Gidado kan share kwanaki ba ya nemanta koda ta waya sai idan ta nemeshi.
"Na gaji da jin maganar Gidadon nan, don Allah ki hakura ki fiddashi cikin ranki, idan mijinki ne fa sai kunyi aurennan ko ba ya so." Cewar Hajiya a wataran da ta risketa tana kukan yanda ya ke yawan yi mata hirar matarsa wanda batasani ba wani zubin da gayya ya ke yi don kawai ya gwada ko tana kishinsa.
Ta share hawayenta. Gidado zaune ya cigaba da fayyacemata irin son da ya ke mata ya kuma tabbatarmata ba da wasa ya zo ba, sonta ya ke yi tsakaninsa da Allah. Koda ta yi mishi batun Hafsa, ya nunamata wannan ba matsala bace, matarsa nada saukin kai tana son abinda ya ke so.
Ranar saida ta yi nafilfilu don nuna godiyarta ga Ubangiji. Daidai da Hajiya ta taya diyarta murna hakanan duk wani masoyinta da yasan tana son Gidado, ko Ihsan ma ta dan ji sanyi ganewar ba yar uwarta kadai ke wahala ba, ashe shima yana so.
"Allah Ya ba ki sa'a." Shine kawai abinda Jidda ta fadi.
Ita kuwa bata biyemusu ba don ta gane yan adawa ne.