Sashe 14
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
19
"Ki sanar da ita cewar tana iya tafiya, don banason had'a tafiyata da shirgi."
Ummi dai toh kawai ta furta sannan ta mike.
"Tsaya Ummi." Cewar Iklima wacce ta fito daga d'aki cikin shirin shadda ruwan k'asa mai turuwa, dankwalinta a hannu da ribuna. Gaba daya suka dubeta. Ta dubi Hajiyarta.
"Ni zan bisu yanzu mu tafi."
Hajiya Binta ta bita da mugun kallo, ta tabbatar wannan rawar kafar da takeyi bai wuce na son ganin Faruk ba, ita kuwa ta ci alwashin koda Iklima zata mutu, ba zata ta6a bari ta auri jinin Mami na kut da kut ba.
"Banyi miki iznin binsu ba, ke wuce ki isar da sak'ona. Tana iya tafiya."
Ummi jin haka yasa ta juya gami da dan ta6e baki, da sauri ta kara gaba batare da ta jira jin yanda zata kaya tsakanin 'ya da uwarta ba.
Kai tsaye dakin Anti Amarya wato Hajiya Lubna, ta nufa. Ita kam babu laifi tana da tsafta itama duk da cewa ko rabi-rabin kafar Mami bata kama ba, bata falon sai yaranta. Babu wanda ya yiwa Ummi kallon banza, saidai kuma basu bada muhimmanci akanta ba don hankalinsu ya tafi ga kallon wani film na yak'i da ake haskowa a (Mbc Max). Ganin haka yasa ta kara magana.
"Don Allah ina Anti Amarya? Mami ce ta aikoni wajenta."
Hassana ce ta dubeta.
"Me za'a ce mata?"
Ummi ta sanarmata, Hassana ta shiga dakin mahaifiyarsu. Ummi ta cigaba da nazarin falon, ta lura dai kusan duk girmansu daya da na Hajiya Binta, Mami ne komai nata ya fita daban mai yiwuwa kuma don itace farkon zama a gidan kafin zuwansu. Hakanan ta kasa bambance falon wanda yafi shan kaya acikinsu, don kowanne falo akwai nasa kyawun na musamman. Tunaninta ya katse bayan fitowar Hassana.
"Tace sai zuwa anjima yanzu kanta yana sarawa ta sha magani ne."
"To, Allah Ya bata lafiya." Daga haka ta mike ta fita.
Mami tuni sun shiga mota, itama shiga tayi sannan ta sanarwa Mami sakon data samu wajen kowannensu bayan ta yiwa sakon Hajiya Binta kwaskwarima inda tace kawai sai zuwa anjima zata taho. Danliti yasa hancin mota ya fita daga harabar gidan.
Sunci sa'a don kuwa ba'a kai ga daura aure ba an dai tafi. Motoci cike makil ne a kofar gidan har babu wajen fakin, dole daga nan waje Danliti ya saukesu sannan yayi gaba don neman wajen ajiye mota.
Gidan a cike yake da yan uwa da abokan arziki na jiki sosai, Ummi banda rarraba ido yanda zata ga Amina babu abinda takeyi, saidai ko kusa bata hangota ba. Ga waje da mutane ba kadan ba ballantana tace zata nemeta. Haka ta hakura ta nemi gefe guda saman tabarma anan tsakar gidan ta zauna tana kalle-kalle. Kwalliya iri-iri, da wadanda suka burgeta da wadanda ko kusa basu burgeta ba take gani, a haka Ihsan ta zo ta wuce, har ta gaji da haduwa sai daukar ido takeyi. Ummi ta bi takalminta da kallo wanda yake da tsini sosai, jinjina kai kawai tayi tunanowa da Tasleem ta 'Yar Bariki wacce ta tsinci Ihsan kwanaki tana labartawa Adnan yanda labarin yake, har take mishi batun takalman da Tasleem ke sanyawa. Toh ita kam bata ga marabar takalmin da Ihsan ta kwatanta da wannan dake kafarta ba. Da ace itace ai babu abinda zai hanata karyewa a kaita d'ori, sai ikon Allah.
Ta jima sosai anan zaune, kafin ta soma jiyo gud'a sosai yana tashi daga hancin tsoffin dake a wajen.
"An d'aura." Shins furucin da ta ji a bakunansu. Nan kuma ta ga tawagar kawayen Amarya dake a tsakar gidan sun karasa falo suna faman ihu da gud'a. Haka aka cika mak'il a falon Innar su Mami. Ganin da tayi ba zata iya lek'e ba yasa dole ta hakura ta koma da baya ta raku6e jikin bango ta zubamusu ido. A haka tawagar angwaye kuma kusan yan uwan juna gaba dayansu, don da yawansu daga Adamawa suke, yan uwansu ne sai kuma Abokai suma babu laifi.
Bata ci wuyar hangen Ango Haidar ba, ya cakare cikin farar shadda wacce ta sha aiki mai tsada. Sai wani shek'i yakeyi. Hakanan kusan gaba daya tawagarsa fararen kaya ne jikknsu idan ka cire yayyun Ango da kaninsu Faruk, wadanda sukayi ankon shadda ruwan madara. Sunyi kyau har sun gaji da haduwa, Ummi ta karemusu kallo, tabbas 'ya'yan Hajiya Babba abin so ne ga dukkan wata diya macen da take ji da kanta ita din mai aji ce. Idanunta suka fi karkata ga Faruk wanda ta ga kamar an kara matso kyawunshi, a yau yafi koyaushe haduwa domin kuwa fuskarsa yau a sake take hakanan hakoransa a bayyane har gefen kuncinsa na dama ya lotsa. Ya sanya farin tabarau a idonsa, ta sauke ajiyar zuciya, koda ace batasan me ake kira da hadadden namiji ba, to shakka babu akan Faruk ta sani. Cikin sa'a kuwa shima idanunsa suka sauka akanta daidai lokacin da yake gyara zaman agogonsa. Haka kawai ta tsinci yanayinta ya sauya adalilin kallon da yayi mata wanda ta tabbatar haka kwayar idanunsa suke, ba wai da gayya ya yi ba. Ga mamakinta fuskarsa bata sauya daga murmushin da yakeyi ba duk kuwa da cewar sun hada ido da shi, ta numfasa ta kauda kanta har suka shige zuwa Falo wajen iyayensu.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
18
Babu jimawa sosai Amarya ta iso filin da Angonta. Baki bud'e Ummi ta dubi Amina, alokacin wuri ya hargitse, k'arar kid'a ya yawaita da ihun mutane da masu daukar hoto. Ta so ta tambayi Amina daman namijin na zuwa kamu? Saidai babu damar hakan sakamakon hayaniyar da tayi yawa awajen, sunyi kyau matuk'a. Gaba dayansu fararen kaya suka sanya, Haidar cikin farar shadda, yayinda itama Intisar ta had'e cikin shadda dinkin doguwar rigar da ta sha aiki. Su Ihsan da sauran kawayen Intisar suna take musu baya, hakanan shima ango, abokansa na Abuja da na nan Kano kalilan cikinsu sun samu halara, yayinda wasu suka barwa gobe daurin aure. Ba anko sukayi ba, saidai shadda brown kowannensu ya saka, na wani yafi na wani turuwa.
Sunyi kyau kwarai, sai kirari ake yiwa Ango da Amaryarsa har suka isa mazauninsu. Duk raba idanun Ummi bata ga yayyun Haidar ba da kuma Faruk. Har akayi nisa da sha'anin, mata ne kawai da daidaikun matasan wajen wadanda dukkansu yan uwansu ne na Adamawa sai kuma yan uwan mahaifin Haidar Danzaki da ma'aikata.
Sun jima sosai a wajen, an ci an sha, har saida aka kusan tashi sannan ta hangi mota ta faka daga can gefen na amarya da ango. Su biyar ne suka fito daga motar, Yaya Ridwan ne sai wasu wadanda suka fi kama da abokansa, a hannunsa kuwa, wata kyakkyawar yarinya ce wacce bata fi shekaru uku ba tana bacci saman kafad'arsa. Har aka tashi daga wajen babu Faruk da Babban Yaya.
Duk da irin gajiyar da Ummi ta kwaso, wannan bai hanata watsawa jikinta ruwa ba kafin ta chanja sutura ta kwanta.
☆☆☆
Washegari ya kama ranar da za'a daura aure da kuma yini. Tun safe da mutanen dakin Mami suka farka, babu wanda ya koma bacci. Daga Maigidan har sauran yaransa maza, shirye-shiryen karyawa sukeyi su wuce d'aurin aure, yayinda Mami itama ke shirin tafiya gidan biki. Ummi kuwa, ayyukanta ta shiga yi cikin sauri-sauri bisa umarnin Mami, don kuwa a son Mami, tafiso tana can a daura aure maimakon ace bata isa ba. Itama Ramma sanin da tayi na cewar Mami da wuri zata fita ne, yasa ta shiryawa da wuri, bata da wani aiki a kanta mai yawa kasancewar yaranta sun je k'auye. Wannan karon dai Ummi ta ji maganar Amina, don kuwa ta shafe fuskarta da hoda sannan ta sanya jan baki kalar ja sai kwalli data zizara a idonta. Ita kanta tasan tayi kyau, irin kyawun da bata ta6a ganin ta yishi ba, ko don ba kwalliyar takeyi ba?
Ankon bikin da Mami tayi musu ne a jikinta, ya zauna d'abas kamar a jikinta aka d'inkashi, ya fito da kyakkyawar surarta wanda ita kanta batasan tana da diri mai kyau ba kamar haka. Har ta dauki mayafi ta yafa sai kuma ta ga sam ba zata iya ba, hakan yasa ta janyo farin hijabinta wanda ya hau sosai da atamfarta mai adon fari da koren fulawoyi. Kiran da Mami ta kwalamata ne yasa ta amsawa da sauri don bata da masaniyar cewa Mamin ta shigo falon domin itace a fadar Alhajinsu.
"Masha Allah." Shine furucin da Ummi tayi a ranta, duk iyakar yanda take ganin ta fito tayi kyau, sai ta raina shigarta ganin shigar Mami, ba irin ankonta bane a jikinta. Wani tsadadden leshi ne ruwan madara mai duwatsu dinkin doguwar riga da zani ta sanya, anyi aiki a gaban rigar leshin wajen kirji, banda kamshi babu abinda kakeji yana tashi a falon. Hannunta rike da jaka da mayafinta. Ta dubi Ummi duban tsaf kafin cikin sakin fuska tace. "Ashe dai kin iya kwalliya." Abin ya bawa Ummi mamaki, kodayake dai tasan yau Mami cikin farinciki take. Ramma dariya tayi kawai, itama tayi tsaf da ita tana rike da karamar jaka na kaya wacce ta tabbatar na Mami ne.
"Shiga ki cewa su Hajiya Binta idan sun shirya su fito mu wuce."
"Toh." Sannan ta kama hanya da mamakin wannan irin iko na iyayen gida irin Mami, wato bata damu da ta sanarmusu su shirya ba tun farko saida ta tashi tafiya. Sashen Hajiya Binta ta soma zuwa, a zaune ta sameta tana latse-latsen waya ko wanka batayi ba. Ciki-ciki ta amsa sallamar Ummi, gabanta na dukan tara-tara, ta durkusa ta shaida mata sak'on Mami. Kamar ba zata ce komai ba saidai ta dubeta a wulakance har saida ta ji ta muzanta.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
20