← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 116

Sashe 62

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yana kwance yasa filo tsakaninsa da mahaifiyartasa sannan ya dora kansa saman filon suna 'yar hira akan ginin gidansa wanda ya yanzun ya yi nisa sosai. A haka suka yi sallama suka shigo, ya lumshe ido jin muryar abar kaunarsa kafin ya bude ya kai idanunsa gareta. Bata ko kalleshi ba saboda idon Hajiya dake kansu, ya mike zaune gami da rungume filon kujerar a kirji. 
   "Wash! Sannunku da gida." Cewar Ikram, itama Ummi ta gaishesu. Sannan ta mike don zuwa gabatar da Magriba don a hanya ta yi musu. Kasancewar Ikram na fashin sallah, ta dakata gami da budewa Hajiya ledar kayayyakin kamar yanda ta buk'ata. 
  Tun ganin kayan Faruk ya daure fuska, ya yi shiru yana jiran abinda zai fito daga bakin Hajiya. Ita dinma fuska ba walwala ta dubi Ikram.
"Menene wannan ki ka kwaso kuma? Wannan cream din nasa haske fa?"
  Ta girgiza kai.
"Ita fa ta za6i abinta wallahi, bari na yi ta za6i abinda ranta ke so."
  Suna hada ido da Faruk ya watsamata wani mugun kallo da ya yi sanadin kadawar yan hanjin cikinta, ta daure ta kauda kai. Baice komai ba, yana ji Hajiya ta hauta da fad'a sosai akan wannan ba daidan ba da ta yi mata. 
"Haka na sanyaki? Bance ki za6omata ba? Ko don kinsani ita din bawani za6e zata yi ba?"
   Gogan waya ya hau dannawa abinsa yana mai nazari, amma kwarai Ikram ta rainashi, wannan ba Ummi ta raina ba, shi ta raina. 
  "Ai dole sai kin koma gobe..."
"Is ok Hajiyata, ki yi hakuri."
Ya katse Hajiya da ke faman sababi, ta mike ta wuce sashen Daddy daman yana nafilfilu shiyasa ta zauna nan.
   Bayan fitarta ya dubi Ikram.
"Tashi muje."
Ta kasa motsi ta hau ba shi hakuri, ya dakamata tsawa.
"Na ce ki tashi!" Ba shiri ta mike shima ya mike tsaye ya nufi dakin Ummi, tana zaune saman darduma mai taushi ta idar da salla tana addua, saida ya jira ta kammala sannan ya bata umarnin ta taso. Ba tambaya ta bi bayansa sanye da hijab ajikinta. 
  Tare suka fice bayan ya sanarwa Hajiya ta waya, gudu kawai ya ke shararawa a saman kwalta, har suka isa wani katafaren boutique wanda duk Abuja babu irinsa indai a fannin saida kayan amfanin mace ne. Haka ya shiga ya lodowa Ummi kayayyaki masu matukar kyau da tsada wanda Ikram zata iya rantsewa ita kam bata ta6a amfani da irinsu ba, saidai ta yi ta burin ta siya. Jikinta ya yi sanyi tana kallo takalma kala-kala da kananun kaya masu kyau da tsada amma babu halin ta ce ya siyamata. Ta k'ulu matuka, wato don ya ramawa Ummi ya yi mata haka kamar ba kanwarsa ba, saida ya gama jidar son ransa har da abaya kala uku da kayan shafe-shafe masu kyau da gyara fata sannan ya biya ta hanyar Atmcard dinsa. Haka aka loda kayan a boot wasu a gefen Ikram da ke zaune bayan mota sannan suka tafi, a hanya ma sai jan Ummi da hirar soyayya ya ke tana kakkaucewa, wani abin kuma ya sanyata dariya. Wannan ya k'ular da ikram matuka. 
  Hajiya ita kanta ta yi mamakin yawan kayan da Faruk ya siyo saidai tasan don an 6ata mishi ne, yasa Ikram ta shigar mata da su daki, kamar ta yi kukan wannan abu haka ta yita kwasa tana shigarwa. Ya shigo har dakin ya tsaya bayan komawar Hajiya sashen Daddy, ya umarceta da ta jeramata na shafar a gaban madubi, tana hawaye tana yi, Ummi na zaune bata so hakan ba saidai ya hanata motsi, asalima zama ya yi gefenta ya soma nunamata wasu hotunanta a wayarsa da ya dauka batare da saninta ba, soyayya dadi, nan ta mance da wata Ikram, saida ta juyo ta ganta ne yasa ta dan janye daga hirar. Bayan ta kammala yasa ta jera takalman harda su abayoyin da sauran kananun kayan na shigar mutunci a kwaba. Faruk bai bar dakinnan ba saida ta shirya komai tsaf sannan ya dubeta.
"Get out now."
   Ya fada gami da maida dubansa ga abar kaunarsa, ta dubesu suna hada ido da Ummi ta watsamata harara sannan ta fice tana goge fuskarta. 
  "Da ka barshi wallahi zanyi Yaya Faruk, ba ka gudun janyomin bak'in jini?"
  Ya daga kafada.
"Sun jima basu yi ba, karki damu kanki ai kin wuce haka a wajensu, kannenmu ne fa."
Ta yi murmushi kawai can kasan ranta damuwa ce fal, ta lura shi ko a jikinsa, dakyar ta korashi kada Hajiya ta ganshi. Ya fice yana dariya ta bishi da kallo tamkar ta hadiyeshi don so.
                    ***   ***   ***
                         KANO
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

80
                         KANO
Ranar litinin ya kama na tafiyar Adnan, ranar ne su Rahila da Aisha suka zo gidan. 
  Suna zaune a dakin Mami su duka banda Adnan sai kuma Mamin dake labartamusu batun auren Ummi da Faruk. Salati su Rahila suka shiga yi.
"Tabdi! Ni narasa ma yanda zan fassara wannan lamarin? Wallahi karki sake ki yarda a had'a darajarki da wata can wacce ba komai ba. Anya haka Ummi ta barsu?" Rahila ke maganar cikin 6acin rai.
"Wallahi nima ina tunanin da walakin, goro a miya. Amma don Allah ku yi tunani, ta ya ya Yaya Faruk zai so Ummi har ma wai ace son aure ya ke mata? Na yarda yarinya ba laifi ta hadu saidai anya kuwa ba zaa bawa Hajiya Babba shawara akan dagewa da rok'on Allah ba? Nikam wallahi ina tantama idan bawan Allahn nan cikin hayyacinshi ya ke."
Ta k'arashe cikin jimami, Ihsan na jinsu saidai takaici ma ya sa ta kasa cewa komai. Mami ta ta6e baki.
"Su suka sani, idan aure ne suyi ta yi, munanan sai ta auri wanda yafi Faruk din kud'i in sha Allah."
  Haka sukayita tofa na bakinsu, ko kusa Mami bata sanarmusu da sa'insar da ta shiga tsakaninta da Hajiya Mama ba. Sai a ranar ma ta daure ta amsa wayar Hajiya Babba, ta kuma fadamata cewar Ihsan kam ta hakura da Faruk akwai wanda ke sonta.
  Hajiya Babba gaba daya ta fahimci Madina fushi ta yi, ta nunamata hakan ma karin dankon zumunci ne idan akayi.
  "Kenan za'a fasa da Ummi ya aureta ita kadai?"
Hajiya Babba daga can ta dan yi shiru, ina ita ina yiwa Sadaukinta wannan gangancin?
"A'a Madina, menene idan ya auresu duka? Ina ce shi ya ga zai iya?"
Mami ta yamutse fuska ta ji haushin maganar sosai. 
  "To Ihsan dai ta dawo kuma ta tabbatar min matukar ba ita kadai zai aura ba to bata son auren."
   Hajiya Babba ranta ya 6aci, wannan son kai ne kawai.
"Amma Madina kin ban mamaki, menene ciki..."
"Don Allah Hajiya ke babba ce, ina ganinki da girma, na gayamaki raayin 'yata tunda bazai samu ba hakan to don Allah ki samamin lafiya, aure kuma idan ana daurawa sau dari a daura na Faruk da Ummi."
Daga wannan ta kashemata waya.
     A daren Adnan ya tafi, koda suka hadu da su Rukayya a(airport) hankali kwance suka gaisa yanda suka saba don babu wanda yasan wani abun, sun yi hotuna har Adnan na hawaye suna tayashi, haka suka yi bankwana cike da jin kewar juna.
Chapter 62 · 0% Book details