Sashe 34
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Adnan?" Ya furta a hankali, a iyakar saninsa Adnan baya nan sai Kb wanda ya bari yana shiryawa amma don tabbatarwa ya dauki waya ya dannawa Adnan kira, koda ya dauka ya tabbatar mishi yana farfajiyar wajen taron. Ya tsaya yana tunani, kada dai cutar Ummi zasuyi?
"Oh No!" Ya fad'a da karfi sannan ya fito daga motar cikin zafin nama.
Ita kuwa Ummi kai tsaye saman ta nufa ta hau kwankwasawa, aka budemata, ana budeww daga bayanta ta ji an hankadata cikin dakin sai jikin KB. Kafin ta kai ga duban wanda ya hankad'atan ta ji an rufe k'ofar har da sanya muk'ulli.
A gigice ta d'ago tana fadin.
"Adn..." Maganar ta makale a fatar bakinta ganin Kb daga shi sai gajeran wando. Fisge jikinta ta yi da karfi jikinta ya soma rawa.
Ya soma nufota da murmushi yana shafar gefen fuskarsa.
"Helloo bebi."
Ta nufi kofa da sauri zata bude, saidai ga mamakinta ta ji kofar gam! Ya kamo k'ugunta yana dariya.
"O'o, guduna kikeyi?"
Ta fisge jikinta, tuni ta soma kuka tana ja baya.
"Don Allah ka yi hakuri ka kyaleni."
Ya jinjina kai.
"Ki yarda da ni zan kyaleki."
Ya cigaba da nufota tana ja baya.
"Don ke na k'i tafiya wajen party fa Bebi."
Faruk na hayowa sukayi kici6us da Sa'a tana saukowa tana dariya, ganinsa yasa ta sakin ihu don tsoro, jikinta ya dauki rawa, tunda ta ke bata ta6a ganin Faruk a yanayin da ta ganshi yanzun ba, gaba daya idanunsa sun kad'a, fuskarsa tamkar bai ta6a dariya ba. Ya shak'o wuyanta, cikin kakkausar murya yace.
"Ina Ummi?"
Muguwar shak'ar da ya yi mata ne yasa muk'ullin dake rik'e a hannunta ya fadi don sunyi da Kb da zarar ya kammala zai nemeta a waya ta bud'esu, jin faduwar abu yasa shi kai dubansa k'asa. Da sauri ya dauka ya dago ya dauke fuskarta da lafiyayyun mari har biyu sannan ya nufi saman da gudu, tuni Sa'a ta gudu ta bar wajen.
Daidai lokacin da Kb ya rungumo Ummi da karfinsa na da namiji yana sumbatar wuyanta duk kuwa da irin turjiya da duka da cizo da ya ke sha, bai fasa abinda yakeyi ba, alokacin Faruk ya bude kofar ya hankadata ya shigo. Baiyi wata wata ba ya janyoshi ya wanke mishi fuska da mari.
"Are you out of your senses?!!"
Ya k'ara janyo ya kai mishi naushi a baki.
"Baka da hankali KB?!! Kazamin jikinka kake hadawa da na Ummina?!! Kayi kadan wallahi!!!"
Ya cigaba da bugunshi, Kb babu karfin haka ya yi ta jibguwa. Da dai Ummi ta ga yana shirin kisa a guje ta yi kansa ta shiga tsakani gami da rike kafadarsa a gigice tana kuka.
"Don Allah Yaya Faruk ka yi hakuri, ya isa ka rabu da shi."
Ya watsamata kallon da ya kad'a hanjin cikinta. Ya fisgi hannunta suka fita, bai tsaya ko'ina dq ita ba sai wajen(swimming pool) dinsu, wajen babu kowa. Ya saki hannunta ta fada gefe tana kuka sosai.
"Ga irinta! Ga irinta nan!! Yau da kina gaban iyayenki, wane shege ne zai shigo ya nemi 6ata rayuwarki..." Sai kuma ya yi shiru har lokacin cikin zafi ya ke, ya dauki kujera daya ya yi jifa da ita da karfi har ta 6alle. Ummi ta fahimci ya fusata, ko me za ta ce bazai ta6a fahimta ba, mutane nawa ne a gaban iyayennasu ake lalatasu, wasu ma ubannasu ne da kanshi? Ya zauna saman kujera ya dunk'ule hannu wuri daya gami da dafe goshinsa har lokacin bai huce ba, babu abinda ya ke hangowa sai Ummi a jikin KB. Maganarta ta katse tunaninsa.
"Wallahi bani da laifi, yaudarata sukayi." Daga nan ta labartamishi dukkan abinda ya faru, sai kuma lokacin ya dan samu nutsuwa duk da daman ya zargi hakan. Ta cigaba da kuka mai shiga zuciya. Ya kasa daurewa ya mik'e ya isa gareta gami da yin zaman durshen agabanta yana lankwashe kafafuwa. Ta dago idanunta jajaye ta zubamishi, shi dinma ita ya ke duba.
Sakonni kala-kala ta ke amsa daga gareshi duk da yanda idanunsa suka kad'a don 6acin rai, hakan bai hana ta ganin wasu abubuwa masu wuyar fassaruwa ba, masu kashe jiki ba. Shima awajensa ji yakeyi yau bazata wuce ba sai ya sanarwa Ummi abinda ya ke ji gami da ita, idan ta san amsoshin ta k'aramishi ilimi a kai.
Ta sauke idanunta tana tuna furucinsa na dazun. "Ummina."
Hannunsa ta ji a saman ha6anta ta razana don har lokacin fargaba bai barta ba na abinda Kb ya yi mata. Ya cire hannunsa da sauri don ya gani hakan. Ya fiddo hankicif ya mik'a mata.
"Share fuskarki, yau zan gayamaki abinda ban ta6a fad'awa wata diya mace a doron k'asa ba Ummi."
Ya yi magana tamkar mai rad'a, ta dubeshi, shima ya zubawa gashinta ido wanda ya tabbatar garin kwatar kai ta baroshi a can, ya maida kansa gareta yayinda ta ke bin umarninsa. Gabanta sai lugude ya ke yi, shiyasq bataso ta ra6eshi, don duk sadda suka hadu suka rabu, dakyar tunaninsa ke barinta ta sake. Ya soma magana.....!
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
48
"Ummi shekaruna ashirin da tara a duniya, amma bazan ce miki yau ga wata mace da nakejin irin abinda nake ji ba akanki ga ita ba."
Ta dubeshi a matukar kaduwa. Ji ta yi kamar ta shid'e don tsoro. Idanunsa sam babu wasa sai ma wani kankancewa da suka k'ara yi yana mai dubanta duba na saurayi a gaban budurwar da ya ke mutuwar so tamkar numfashi.
"Yes, ki kalleni sosai Ummi, ina a cikin hayyacina ba wani abu na sha. Amsa za ki bani please, idan har kin sani, idan ma ba ki sani ba ki tayani nemowa."
Hawayenta suka zubo tuni ta sunkuyar da kanta k'asa.