Sashe 60
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
*** *** ***
. ABUJA
Hajiya Babba ce zaune a falonta tare da yaranta maza ana 'yar hira. Ta dubesu cike da farincikin ganin yanda Ridwan ya sakarwa Faruk fuska kamar yanda suka saba, fatanta Allah Ya cigaba da had'a kan yarannata haka. Suna zaune a saman kafet ga katuwar leda agabansu an shimfid'a sai kulolin abinci duk Ikram ta zuzzubamusu. Haidar ya sanyo batun auren Faruk da irin kyauta ta musamman da ya tanadar mishi.
"Mata biyu lokaci guda? Ai wannan ni kadai nasan tanadin da na yi ma."
Ya fada saitin kunnen Faruk , ya yi kamar bai ji ba ya cigaba da cin abincinsa. Babban Yaya na jin haka ya ajiye cokali gami da dan kora ruwa sakamakon kwarewar da ya so yi babu shiri.
"Wai wa zai auri mata biyu?"
"Oh, baka da labari fa ashe Dan uwa." Cewar Dakta.
"Abincin za ku ci ne ko hira zaayi?"
Suka tsinci muryar Daddy wanda ya katse hanzarin Haidar da Dakta masu zuci-zucin bawa Babban Yaya labari kamar wasu yara.
Ya karaso fuska a sake ya zauna.
"Ke kuma na lura duk ranar da 'ya'yanki ke gidannan kina mantawa da lamurana, ina ga dai na kusa hanaku irin wannan zuwan."
Ya karashe yana kallonsu, suka yi dariya har Faruk.
"Kai amma da na ji dadi Daddy." Ya fad'a yana kanne ido daya. Suka watsamishi hararar wasa banda Babban Yaya da ya ke dariya.
"Kwana nawa ne kaima?" Fadin Haidar kenan.
Daddy ya dakatar da su da hannu.
"Ya isa hakanan, a ci abinci a nutse. Idan kun kammala ina nemanku."
Daga haka ya tashi Hajiya ta bi bayansa.
Bayan sun kammala suka hadu sashen Daddy har Ikram. Ya soma da fadin.
"Ku amanar Allah ce awajena, ya kuma zama dole na dunga nusar da ku akan lamura na rayuwa." Ya cigaba da yi musu nasiha mai ratsa jiki kafin ya sanyo batun auren Faruk da Ummi.
"Idan Allah Ya shiryo hakan babu wanda zai hana, hakazalika kowa da kaddararsa a rayuwa."
A karshe dai ya kara nusar da su batu na hadin kai, akan ko bayan ransa yana fatan su rike zumunci.
Sun jima anan, Babban Yaya bai nuna wata alama ta k'in sha'anin ba, Ikram dai har lokacin zuciyar bata lafa ba, koda ta yi yunkurin hakan da zarar ta tuno da wacce zaa aurar sai ranta ya yi bak'i. Ko yar uwarta Baraka lamarin baiyi mata dadi ba, Intisar ma ta nuna rashin yardarta ga Hajiya Mama nan ta ci karo da fushinta, dole ta ja bakinta ta yi shiru ba don ranta naso ba, ga mijinta shima da ya goyi bayan dan uwansa.
Haka taro ya tashi zuciyar kowa a sake har Ikram don ta samu dama Faruk ya sakarmata fuska.
Bayan fitarsu Daddy ya sanarwa Hajiya cewar lokaci ya yi na dauke Ummi daga sashen yan aiki, itama daman ta yi tunanin hakan saidai tunanin da ya yi mata yawa akan k'in daga wayarta da Madina ta k'i yi duk kuwa da cewar ta samu magana da Hajiya Mama ta nunamata komai lafiya amma sam hankalinta bai kwanta ba. Sunyi waya da Adnan ya sanarmata gobe zai wuce, ta bishi da kyakkyawar addua da kuma nasiha.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
78
KADUNA
Amarya Dija an dirji amarci, Deen kamar ya haukacemata tsabar rud'ashin da ta yi, ita kanta tasan ta yi aure ta samu miji na nunawa sa'a.
Munira baiwar Allah, a wannan daren ta ci kuka har ta gode Allah, tana yiwa ranar kallon bak'ar rana agareta, wai mijinta da yar uwarta da ta dauketa tamkar wadda suka fito ciki daya, sune tare a makwanci guda. Dakyar ta iya saita kanta don a daren ba wani bacci da ta yi. Da safiyar litinin ta daure ta rigasu fitowa ta hada karin kumallo na gaba dayansu. Kamar ta je ta kwankwasa musu sai kuma ta tuno cewar ko sallama a daren jiya Deen fa baizo ya mata ba, koda a waya bai nemeta ba sai ita da ta mishi sakon taya murnar aure nan ma bai amsa ba. Anya yanzu ba bada kai bane ta je kwankwasa musu? Ai ta daure ma da ta yi girkin. Juyawa ta yi ta koma suka karya da yaranta ta shiryasu ta fice kaisu makaranta.
Su kuwa masoyan basu tashi ba sai bayan takwas, suka shiga wanka bayan sun gama suka shirya. Dija ta hade cikin wani leshi kore dinkin da ya kama jikinta, shi kuwa kananun kaya ya ci don ya samu hutu wajen aikinsu na amarci.
Koda Munira ta shigo, dariyarsu ce ta bata shaidar sun tashi, ta daure ta hadiye abinda ta ke jin ya tasomata a zuciya ta shige dakinta.