← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 116

Sashe 68

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washegari da misalin karfe sha biyu na rana, Hajiya Mama da iyalanta suka dira a gidan Modibbo. Ummi tun gaishesu da ta yi ta sauko. Ido hudu sukayi da Antinta Amina dake tsaye a kofar kicin suna gaisawa da Larai. Da sauri Amina ta juya ta fita, itama Ummi cikin saurin ta karasa sauka daga bene ta fita, tsaye ta ganta a baranda ta sunkuyar da kai. Cikin sanyin jiki ta karasa gareta ta dafa kafadarta fuskarta dauke da matsanancin farinciki.
"Anti."
Koda Amina ta dubeta ta razana da ganin hawayen dake saman fuskarta. 
  Hankalinta ya tashi.
"Anti ki yi hakuri don Allah, ban.."
  "Meyasa haka Ummi? Meyasa bakya tausayawa kanki da rayuwarki? Anya kuwa kinsan hatsarin da ki ka jefa kanki? Kina sane cewar a sanadinki zumuncin dake tsakanin Mami, Hajiya Babba da Hajiya Mama ya raunana?"
  Gabanta ya fadi, Amina ta koramata bayanin duk abinda ke faruwa ta dora da fadin.
"Ina jiyemiki tsoron abinda zai je ya zo. Karki dauki maganganu a baibai, ni mai kaunarki ce, ba kuma zan so wani abu ya sameki ba sanadin auren Yaya Faruk, saidai kishi tsakaninki da Ihsan?"
Ta yi shiru tana mai girgiza kai kafin ta share fuskarta. Bata kara komai akai ba ta yi gaba, Ummi hankalinta ya yi mugun tashi, duk wannan abun ya faru ne sanadinta? Ya akayi bata da masaniya? To wa zai fadamata, bata ji daga bakin kowa ba, ta tuno dai sadda Hajiya Babba ke kokarin yi mata magnar Faruk ya shigo wanda hakan yasa Hajiya katse maganar da ta yi niyya alokacin. 
   Durkushewa ta yi awajen sai kuma ta ji kuka mai karfi ya tahomata, da sauri ta zagaya dan lungun gidan ta durkushe ta soma shek'asa, duk a sanadinta hakan ya faru, anya bata zama mai son kai ba? Tana ina akayi hakan? Meyasa babu wanda ya sanarmata? Sai gaba daya ta ji kunyar kanta ya mamayeta, ya za ta yi da wannan abu? Da wane ido zata kalli Mami a yanzu?  Don ita sam Ihsan bata gabanta kamar Mami, Mami ta fi ji. Acan kasan zuciyarta kuwa tana ji kamar ba zata iya rabuwa da Faruk ba. 
   Ta jima anan har saida ta ji Amina na cigiyarta sannan ta taso ta zo tana mai amsawa. Ganin yanayinta ne yasa Amina jin wani mugun tausayinta, ta janyo hannunta suka zauna a baranda.
  "Anti wallahi ba ni da wannan labarin, bansan da shi ba da babu abinda zai kaini ga amincewa hakan."
  Amina ta yi murmushi cike da tausayawa Ummi, tana kaunar yarinyar ko don hakurinta. Ita kanta ta yi mamakin yanda aka ce Ummi ta yarda da batun auren Faruk batare da wani tunani ba. 
  "Karki damu kanki Ummi, Ubangiji Ya fi kowa sanin dalilin hakan, idan kuma Ya kaddaro aurenki da Yaya Faruk to babu makawa sai an yishi. Kawai dai ni na yi mamaki ne daman yanda akayi ki ka amince har haka."
  Ummi ta dubeta sai kuma ta shiga bata labarin dukkan abubuwan da suka faru bayan tafiyarta, Amina tana murmushi ta tsaida idanunta kawai tana duban Ummin. Har saida Ummin ta shiga damuwa, ga wani gumi da ta ke yi sakamakon iska mai zafin dake kadawa haka kuma garin hadari ne kwance. 
  "Ki godewa Allah da Ya hadaki da mutum mai matukar kaunarki irin Yaya Faruk, lallai kin yi sa'a."
  Kunya ta kama Ummi, ta sunkuyar da kanta don har lokacin hankalinta bai kwanta ba. 
  Kiran da Larai ta yi musu ne ya katse hirarsu, abinci ne. Ta dubi Ummi sadda ta mik'awa Amina filet din abinci.
"Sama za ki hau ai, kya ci a anan?" Cewar Larai.
  Ta ji babu dadi.
"Kai Larai, to ni wacece da ba zan ci da yar uwata ba? 
  Larai zata yi magana Amina ta rigata.
"Ai nasan halin kanwata ko wane matsayi ta taka ba zata wulakanta DAN ADAM ba."
  Larai ta jinjina kai tana mai kya6e baki.
'Inama ni na samu damarki.' Ta yi furucin a ranta, a fili kuwa hannu ta mik'awa Amina.
"To kawo na k'ara muku." Bayan ta k'ara Ummi ta kar6a suka koma falon dake k'asa suna ci suna 'yar hira anan ne Ummi ke jin batun saka ranar Amina wanda aka daga sai bayan azumi don lokacin watanni biyu ya rage azumin.  

   Misalin karfe uku kusan kowa ya iso har Mami. Ummi kasa zuwa ta yi gaida Mami, wajen Amina ta wuce har lokacin da aka bude taro da addua suka soma abinsu.
  Ummi da Amina na nan zaune suka ji sallama, suka dubi kofar suna mai amsawa. Wani saurayi ne dan dogo bak'i saidai kana kallon sumarsa Kaga bafulatanin mutum(lol) yana sanye da shadda fara k'al sai hula da ya dora a kansa. Shima idanunsa a kansu musamman ma Ummi wacce ya k'urawa ido har ta tsargu da hakan ta sunkuyar da kanta. Suka shiga gaisheshi, ya amsa, kafin su yi wani yunkurin Abba da amininsa Alhaji Kabir Jimeta sun shigo, kai a kasa Ummi ta gaishesu don kuwa tana tsoron kallon da zata samu daga Abban wanda bata mance irin rabuwar da ta yi da gidansa ba duk kuwa da ance komai ya wuce. Kafin su kai ga cewa komai sai ga Babban Yaya da Dakta sun sauko daga sama, su suka jagorancesu zuwa saman. Abubakar Kabir Jimeta har ya soma taka benen bai bar waigen Ummi ba shi fa kallon sani ya ke yiwa fuskarta saidai ya kasa tuna ko a ina yasan fuskar! Zai so Baffansa ya gani saidai kuma sam bata k'ara dago kanta ba. 
   Acan sama kuwa bayan an zauna aka gaggaisa, Modibbo cikin harshen fulatanci ya ke tambayar Alhaji Kabir Jimeta mutan gida. Bayan gama gaisuwa Abba ya gabatar da Abubakar matsayin wanda ke son Ihsan da aure. 
  Banda Hajiya Babba da ta riga tasan zancen da kuma Faruk da shima ya riga da ya sani a bakin Hajiyarsa, babu wanda bai girgiza da jin wannan batu ba sai ko Hajiya Mama dake murmushi kawai. 
  ((Ku yi hakuri da wannan, kaina ne ciwo...))
             ***   ***   ***
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Chapter 68 · 0% Book details