Sashe 3
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Washegari dakyar ta iya mik'ewa saboda dad'in baccin da ta ji. Amina ta jima tana tashinta, har daga karshe ta hakura tayi sallah sannan ta k'ara dawowa ta tasheta. Sai lokacin ne kuma ta farka. Ummi harda su miyan bacci.
Bayan ta idar da sallah tana shirin komawa ta kwanta Amina ta dubeta tayi dariya kad'an.
"Lallai Ummi kinaso Hajiya ta bud'emiki wuta. Ai muddin yaranta zasu makaranta to bacci fa ya k'are mana. Sai an had'a musu shayi an dafawa Fahad indomi don kuwa kullum da shi yake tafiya. Sauran kuma wani sa'in shayin ma ba shansa sukeyi ba haka suke tafiya basu damu ba. Sannan akwai gyaran dakunan yara da Hajiya. Sauran ayyukan da ya shafi kicin da falo da tsakar gida, duk ba namu bane, yana cikin aikin Ramma, sai da daddare ne ma tattara falo da kicin yake dole a kanmu. A yanda nasani kenan yanzu, bansani ba ko kema haka zata d'oraki akai ko kuma zata chanja tsari."
Ummi dai tayi shiru kawai tana sauraronta. Suka fita falon. Amina ta kunna fitilu wanda ta tabbatar ita da ta kashe d'in, ita ta kunna don babu wanda zai fito. Adnan ko zai tafi masallaci, zagaye yakeyi ta k'ofar waje ta d'akinsa. Ummi 'yar mik'omin wannan da wancan ce, tana lura da abinda Amina keyi. Haka kuma tana biye da ita da fahimta.
Komai suka hada, Amina ta zuba Indomin a filas din Fahad na makaranta, ta had'a shayin sannan suka fito. A falon suka iskesu, kowannensu na shiri. Ihsan ta shirya Fahad tsaf cikin riga ruwan goro da bulun wando na makaranta. Itama ta shirya cikin riga fara da siket ruwan toka, sai farin hijabi da safa fara, ta saka bak'in takalmi. Shima Adnan irin kayan Ihsan ne saidai wando ne nashi dogo, da farar hula (Face cap) wanda aka buga tambarin makarantar daga gaba. Shima bak'in takalmin ne sai farar safa, wanda hakan ya kasance tsarin makarantar.
Ba karamin kyau da burge Ummi sukayi ba, gaba d'aya sai ta shagaltu a kallonsu tana murmushin inama itace ta samu wannan gatan na zuwa makaranta. Tana son karatu sosai saidai bata da mai mata gatan nan.
Adnan na kokarin zura (belt) na wando ya ankara da ita. Ya dubeta batare da ya cigaba da abinda yakeyi ba, bai kai ga magana ba, tayi sauri ta durkusa ta gaisheshi, ya amsa sannan ta juya ga Ihsan wacce take zura littafi cikin jakarta ta makaranta, itama gaisheta tayi. Ihsan ta amsa tana hura hanci cike da jin ita d'in ta isa ta kai. Adnan ya girgiza kai ya ja karamin tsaki. "Na gayamaki ki daina gaisheta ko? Kodayake don kanki zaki bari ai."
Ihsan ta turo baki. "Nidai wallahi broda kana ban kunya a gaban 'yan aiki. Kaga banason irin haka, wannan jawomin raini ne fa."
Harararta kawai yayi baice uffan ba. Ta dubi Amina. "Ki zubomin shayi."
Amina ta juya bayan ta ajiye na Fahad a gabansa da biredi da bota. Can sai gata ta fito da kofuna biyu a hannunta. Ta ajiyewa Ihsan d'aya, sai Adnan wanda take yace bazai sha ba. Ta ajiyewa Fahad filas d'in abincinsa sannan ta ja Ummi suka fad'a d'akin da Ihsan da Fahad ke kwana. Karamin daki ne sai gado mai hawa biyu na yara. Saman an saka zanin gado kalar ruwan hoda mai zanen (Barbie), na k'asan kuwa an saka bulun zanin gado mai zanen (spider-man). A gefe kuwa, kwabar kaya ne guda biyu, shima d'aya ruwan hoda da fari, dayan kuma bulu da fari. Sai kafet mai duka kaloli ukun da aka kawata tsakar dakin da shi, da kuma k'arami na takawa a daidai hanyar bandaki. Daga can kuwa, karamin madubi ne, sai kwaba da abu mafi yawa akansa, kayan kwalliyar Ihsan ne. Fanka ce kawai a d'akin, sai bada wadataccen iska take. Ba k'aramin burge Ummi dakin yayi ba. Ta saki baki tana kallo.
"Ummi ki dunga lura kina rike abubuwan da nakeyi fa, don kuwa gobe zai iya kasancewa ke d'aya zakiyi. Da zarar Hajiya Mama ta dawo zan tafi."
A sanyaye Ummi tayi magana. "Yaushe zasu dawo?"
Tana murmushinta na sabo ta amsa. "Hausa nayi miki, ni kaina bansan sadda zasu dawo ba amma na tabbatar ba zata kaisu da nisa ba tunda an koma makaranta, yara zasu je. Nufina yau idan ina nan gobe bana nan, kece zakiyi."
Ta jinjina kai. Tare sukayi aikin, har inda ake daukar sabon zanin gado idan na kai sunyi datti saida Amina ta nunamata. Suka fito, tuni yan makarantar sun tafi lokacin takwas ma ta wuce, saidai sam Hajiya bata lek'o ba. Saida suka shiga dakin Adnan nan ma suka gyarashi tas, shima madaidaicin daki ne, da katifa babba wacce bata da bukatar katakon gado. Komai na dakin adon fari da bulu ne, babu wani tarkace a dakin sosai. Amina ta barta da gyaran gado don taga yanda zatayi, sai kuma ta bata mamaki don tayi kokari ba laifi. Ta dan gyaggyara inda baiyi ba sannan Ummi ta share dakin, anan kam ko Amina ba zata nunamata iyawa ba. Bayan sun fito, shayin suka zuba suka sha da sauran biredin sannan suka maida komai kicin suka koma dakinsu. Suna daga kwance Amina ta soma magana.
"Zanso kafin na fad'amaki halayen mutanen da zakiyi zama tare dasu, na soma gayamaki tsarin gidansu don ya dace kisan da wadanda zaki zauna."
Ummi ta muskuta tana dubanta gaba daya ta tattara hankali da nutsuwarta ga Aminan. Ganin haka Amina ta soma.
DAN ADAM
@Rufaida Omar
(03)