← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 116

Sashe 27

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  40
   Yana tsaye a wajen ajiye motoci a Bankinnasu, lokacin misalin biyar na yamma, dawowarsa kenan daga wani aike da manajansu ya yi mishi, yana kokarin barin wajen wayarsa ta dauki k'ara. Ya yi mamakin ganib lambar dw bai sani ba a kuma layin da mutane d'aid'aiku ya ta6a kira da shi. Jikinsa ya ba shi cewar kowanene wannan, wani na jikinsa ne, hakan yasa ya d'aga da sallama. 
  Daga can Adnan ya amsa, Faruk ya saki fuska.
"A'a, k'anina ashe kai ne."
  Adnan ya gyara zaman jakarsa yana duban cikin tashar gami da yin yak'e.
"Ni ne my best, ina Abuja."
Faruk ya ji wani dadi har cikin ransa domin yana kaunar yaron, duk kuwa da tazarar dake tsakaninsu na shekaru, yana daukarsa tamkar wani sa'ansa. 
   "A ina kake yanzu?"
Ya sanarmishi yana tasha, ya umarceshi da daukar taxi yazo banki ya sameshi. Ya mik'awa mai wayar wayarsa gami da godiya sannan ya kama hanya. Bayan zuwansa saida ya jira Faruk ya kammala sannan suka fito. Faruk ya lura da yanayin Adnan ba mai dad'i bane, ga wata rama da ya yi kamar ba ya cin abinci, har ya kasa hakuri bayan sun hau titi ya tambayeshi ko lafiya.
  Adnan daman kiris yake jira, kawai sai ya hau kuka, daman tun dazun ya ke cike da tunanin halin da Maminsu ke ciki ga wani dumbin tausayinta. Faruk na ganin haka ya cigaba da tafiya har ya samu wurin fakin ya tsaya. 
   "Ka tayarmin da hankali fa k'anina, meke faruwa ne?"
  Adnan ya yi shiru, to me kuma ya rage? Dole daman wataran yan uwan su ji abinda ke faruwa muddin Mami ta zo biki ko don yanda gaba daya suka fita hayyacinsu, ya 6oyemasa komai sai abinda Abba ya yi mishi a yau kawai ya sanarmishi.
  Faruk bai ji dadi ba sam, ya sauke ajiyar zuciya, baiyi zaton Abba zaiyi haka din ba koda a mafarki.  Ya dubi Adnan cikin muryarsa sassanya yace "Mami tasan ka taho?"

  "No, na barmata takarda dai."
  Faruk ya girgiza kai gami da daukar waya ya dannamata kira. 
  Mami na zaune saman darduma, idar da sallar magriba da gabatar da nafilarta kenan ko mik'ewa batayi ba ta ji wayarta na k'ara. Ta janyo da sauri, Faruk ta gani ta numfasa, daman tun dazun take jiran kira daga wani na Abujan don jin ko Adnan ya isa batason tayarmusu da hankali. 
   Bayan sun gaisa yake sanarmata da isowar Adnan. Farin ciki ya lullu6e zuciyarta. Fuska a sake ta yi hamdala a fili, ta cigaba da magana.
  "Don Allah Faruk kada ka barshi cikin damuwa, kayi iyakar kokarin ganin ya samu walwala. Nima ina nan zuwa nan da kwana uku da zarar yarannan sunyi hutu."
  Ya murmusa cikin ransa yana mai tausayinsu, ya gama fahimtar akwai wasu al'amura dake faruwa tare da su duk da suna 6oyewa. 
"Karki damu Mami, in sha Allah zan yi yanda kikace."
  Ta yi murna da jin hakan har ta sauke ajiyar zuciyar da hatta Faruk saida ya ji.
  "Nagode d'ana, Allah Ya k'ara muku albarka."
  "Amin."
Ya mik'awa Adnan. Adnan murya a raunane yace. "Maminaa."
  Mami ta lumshe ido hawayenta sukq zubo ta bud'e tana murmushin k'arfin hali.
"Na'am d'an Maminsa, ka gujemu ko?"
  Adnan ya yi shiru baice komai ba sai  huci yake. 
"Karka damu, Allah Yana tare da mu. Kayi kokarin 6oyemin sirrin gida, idan ma ka gayamishi wani abu, to don Allah karka k'ara daga abinda ka fad'a. Kayi kokarin sakin jikinka kada tambaya ta yi maka yawa."
  Adnan ya gyada kai. Haka sukayi sallama bayan tace ya gaishemata da Hajiya Babba. 
  Faruk ya dubeshi da murmushi. 
  "To ya? Domino's Pizza ko kuma Jabi Lake Mall?"
  Adnan ya dubeshi sukayi dariya, ya kanne mishi ido.
"Kaima kasan inda nafi kauri."
  Faruk ma dariyar ya yi kafin ya tashi motar ya harba titi. Bai zarce ko'ina ba sai da suka samu masallaci sukayi sallah sannan suka karasa ya siyamusu Pizza da ice cream sukayi gida. A hanya Hajiya Babba ta kira Faruk a waya jin ya dad'e, ya tabbatar mata suna tafe da Adnan shima yazo. Ta ji dadi kwarai don Adnan yaro ne dan shafta, yanzun sai ya k'ullar da cikinta, sam baya mata bak'unta. 
  Saida suka isa dakin Faruk, Adnan ya yi wanka shima Faruk ya yi suka chanja kaya daga nan suka nufi cikin gidan. Hajiya na falon tare da Ikram da Baraka suna hira. Ganin Adnan yasa yaran soma ihun murna. Shima a take ya ji ya mance da komai ya washe hakora. Ya karasa ya gaida Hajiya har tana mishi fadan dalilin da bai zarto gidan ba ya soma zuwa ga Faruk. Ya daga ledojin hannunsa yana dariya.
"Saboda wannan ne."
  Sukayi dariya gaba daya. 
"An kammala karatu kuma sai tafiya ko?"
Ya dan yi murmushi bai ce uffan ba. 
"Ai nima ji nake kamar na bishi wallahi."
  Cewar Baraka. Ya harareta.
"Ki barwa mijinnaki wa?"
Ta yi dariya. Nan suka shiga hira, Hajiya ta tambayi dalilin ramarsa ya sanarmata ya danyi rashin lafiya ne. Tare suka ci suka sha kayan makulashen sannan Faruk da Adnan suka shiga wajen Daddy suka gaisheshi ya tambayi yaushe ya iso ya ke sanarmishi daga karshe suka koma sashen Faruk.
   Faruk kwance saman gado yana danne-dannen waya, yayinda Adnan ke sarrafa Laptop din Faruk yana duba shafin sada zumuntarsa na Facebook, hankalinsa ya kai ga zanen da Faruk ya yi a jikin sketch board. Ya k'urawa hoton ido yana son tuno inda yasan yarinyar. Zaro ido ya yi gami da ajiye Laptop din da sauri ya nufi wajen. Wannan ya ja hankalin Faruk ga dubansa, gabansa ya fad'i. Shaf ya mance bai cire takardar zanen daga jiki ba. Ya kauda kai sa'ilin da Adnan ya dubeshi.
"My best, wannan ta yimin kama da Ummi sosai. Ya akayi ka zanata?"
  Faruk ya daure ya k'ak'alo murmushin yak'e.
"Hobby na kenan, kasan zane babu inda baya zuwa, haka kawai na tsinci kaina da zanata."
  Adnan ya yi shiru, zarginsa yana bashi kamar akwai wani abu game da Ummin a zuciyar Faruk. Ya numfasa, idan ta yi wari watakil shine wanda zai soma ji. A fili kuwa murmusawa ya yi.
  "Wallahi ta yi kyau, kamar wacce aka dauka a hoto. Gaskiya Allah Ya baka."
  Faruk ya share maganar ta hanyar jefomishi tambaya.
  "Wace k'asa ka za6i zuwa ne?"
Adnan ya baro wajen zanen ya dawo, ransa ya sosu don ya tuno abin haushi. Ya dan daga kafada.
"Bar wannan zancen my best, ni nafasa anan zanyi."
  Faruk ya lura da wani abu, kawai sai ya share. 
                  ***   ***   ***
                     KADUNA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
   41
                     KADUNA
   Dija gaba daya ta sauya, daga mai surutu da zafi zuwa marar son hayaniya da kuma sanyi. Komai takeyi muddin Deen zai shigo, to fa zata mance komai ta shagaltu a kallon dukkan wani motsinsa. Tun Deen bai lura ba har dai ya soma tsarguwa da yawan bibiyarsa da takeyi da kallo. 
    A yau juma'a, Munira batanan ta wuce gidan wata aminiyarta da ta haihu, saida ta dauko yaranta daga makaranta suka wuce tare, gidan babu kowa sai Dija wacce ganin Denn a gida yasa fir ta k'i binsu ta fake da ciwon jiki. Misalin karfe uku da mintuna, Deen yana kwance a falonsa yana duban talabijin, ya ji sallamar Dija. Da mamaki ya dubi hanyar falon, yana mai amsawa. Ganin da ya yi mata cikin shigar mutunci marar mishkila sosai yasa ya dan ji nutsuwa a ransa. Ya mike zaune yana murmushin yak'e.
  "A'a Dija, k'araso mana." Ta dubeshi ta sauke ajiyar zuciya, komai nashi burgeta yakeyi. Ita kuwa ko zata mutu sai ta sace zuciyarsa, shekarunta sun kai munzalin da ya dace ace tana gidan miji ba yawon gidajen yan uwa ba. Itama fa mutum ce ba dutse ba, tana da sha'awa, koda dai takan biyewa k'awarta wacce waya ta hadasu, mai yawan yi mata hudubar banza akan ta amince ta je Kano su had'u don d'ebewa juna kewa, ta k'i yarda amman takan ta6a hirar banza da ita a waya(Wa'iyazubillah). 
     Ta samu wuri ta durkusa gami da gaisheshi. Ya amsa batare da ya kalleta ba yana mai wayancewa da chanja tasha.
  "Ashe sai kai kad'ai, ga abinci can an jera tun dazu."
  Ya dan dara.
"Eh yanzu zan taso na ci."
Ta narkar da fuska.
"Haba Deen, don Allah ka zo muje, ni kaina sai yanzu zan ci. Na riga na saba da ci da ku ana yi ana hira, yanzu da basunan bazan ji dadi ba."
  Ya jefeta da wani irin kallo har saida ta ji gabanta ya fad'i, tsoro ya cikata, sai kuma ya numfasa gami da maida dubansa ga talabijin.
  "Jeki ina zuwa."
Ya bata amsa a gajarce ta mike jiki babu kwari ta fita. Har ta cire ran zai zo sai kuma gashinan, wani sanyi ta ji a ranta ta mike zata zubamishi. Ya dakatar da ita.
"No barshi, zan yi da kaina."
Ta girgiza kai.
"Ban ta6a ganin kunyi haka da Munira ba, nima bazan bari ka zuba da kanka ba kada nayi laifi awajenta."
Jin haka ya kauda kai, ta zuba tana murmushi ta tura gabansa sannan ta zauna saitinsa tana cin nata. Idanunta a kansa, da zarar ta ga zai kallota sai ta yi sauri dauke idanun. 
  A ransa ya ji yana mai jin haushinta, da ace yar uwarsa ce da tuni ya korata gidansu, saidai ba yanda ya iya, baya son ran Munira ya 6aci ya lura sosai take kaunar Dija hakanan tana tausayinta wai adalilin har yau bata samu mashinshini ba.
  Ya rigata mik'ewa ya bar wajen, ta bishi da zazzafan kallo gami da k'ara cin alwashin ba fa zata barshi ba sai ta cika burinta na aurensa. Babu wacce ta fad'omata a rai sai Baba Habiba, ta tabbatar ita daya ce zata iya yi mata kokarin shawo kan Deen ko ta wane hali. Idan ma da hali ya saki Munira ya aureta. (Kun ji butulcin DAN ADAM)
Chapter 27 · 0% Book details