← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 116

Sashe 25

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Daren daga Adnan har Ummi babu wanda ya yi bacci isashshe, gaba daya hankalinsu ya tafi ga Mami wacce basusan dalilin damuwarta ba. Hakanan ta yi abinda shi Adnan tun tasowarsa bai ta6a gani ba, wato ta baro sashen Abba aranar (duty) dinta, abu ne da bai ta6a faruwa ba saifa a yau. Itama Ummi abinda ya dauremata kai kenan, domin tunda take agidan tsawon wata daya da kwanaki bata ta6a ganin Mami ta kwana a sashenta ba alhalin Abba na garin kuma itace da aiki. 
    Inaga mai gayya mai aikin, wato Mami, wacce kwana ta yi tana kuka tana kai kukanta ga Mahaliccinta. Ta kasa zaune ta kasa tsaye, idan ta runtse ido babu abinda ke fad'omata a rai sai tsawan da Mijinnata ya dakamata a sadda ya nufeta da niyyar runguma ya rarrasheta ya nunamata dazun da gaske ya ji wari da baisan dalilin wanzuwarsa ba a tattare da ita. Yana jin warin kuwa ya tureta da k'arfi gami da jan tsaki. Ta matso da nufin tambayar ko lafiya, ya yi azamar matsawa gefe gami da dakamata uban tsawa akan kada ta kuskura ta k'araso inda ya ke. Haka ya kyaleta ya fice daga dakin, ta jima anan tana kuka, har ta ji maganarsa inda ya ke bata umarni kan ta fita zai kwanta. Haka ta tashi ta fito nan ma hancinsa a toshe har wani runtse ido.
  Haka ta k'araci zamanta a falo, ganin babu Sarki sai Allah yasa ta mik'e ta bar masa sashennasa.
   Mami ta numfasa ta kwanta lamo saman filo, a iyakar rayuwarta da Muhammad, matsala makamancin haka bai ta6a shiga tsakaninsu ba. Kullum cikin yabonta yakeyi musamman a 6angaren kwalliya da tsafta. Ayau ga wani sabon lamari ya 6ullomata.

  Washegari da safe Ihsan ta yi mamakin ganin Maminta a d'aki, koda ta gayamata, bata 6oyemata cewar ga abinda Abban yace tana yi ba. Ihsan har kuka ta yi ganin yanda Mamin ke hawaye. Ta girgiza kai.
"Allah kuwa Mami kawai wani abin ne na daman Abba ya 6ullo da shi, amma babu wani abu da na ji ajikinki, asalima wani bala'in kamshi kikeyi."
  Murmushi kawai Mamin ta yi, cikin dauriya ta dubi 'yarta.
  "Nagode, ki tashi ku je kada kuyi latti."
   Haka dai Ihsan suka fice duk jiki babu kwari. Daidai da yan uwansu sun lura yau yaran dakin Mami basu da walwala. Hassana d'iyar Anti Amarya, wacce basu fiye daukar kishi zazzafa ba akan yan uwansu, ta tambayi Ihsan ko lafiya. Ihsan ta nunamata babu komai hakan yasa dole suka dan saki jiki gudun wata tuhumar.
     Acan gidan kuwa, Ummi ta kammala komai na gyaranta a sashen yara sannan ta fad'a sashen Mami da sallama. Bata falon, ta hau gyara saida ta gama sannan ta lek'a d'akin. Duk a zatonta Mami na bandaki wannan yasa ta juya da zummar sai ta kammala zata dawo. Ji ta yi an kira sunanta, ta juya da sauri ta dubi gadon tana mai amsawa. Can ta hangeta ta dukunkune cikin bargo tana faman rawar d'ari. Ta karasa ta russuna ta gaisheta. Kai kawai ta gyada. Murya na rawa tace 
   "Kashemin fanka." 'To." Ta amsa gami da mik'ewa da sauri ta aiwatar, ta dawo ta durkusa.
  "Sannu, a kawomiki kari nan?"
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

37
  Dan yamutsa fuska ta yi ta cire yatsa ta yi mata nuni da dirowar gefen gadon. Cikin rawar muryar dai ta ce. "Duba ki daukomin Paracetamol."
   Koda batasan (spelling) din ba, tasan maganin, ta bude ta hau bincike cikin sa'a kuwa ta samu ta ciro. Ta taimakawa Mamin kamar yanda ta buk'ata ta mik'e zaune. Saida ta sha maganin sannan ta koma ta kwanta. 
     "Ki yi aikinki." Cewar Mami a sanyaye.  
   Ummi ta mik'e ta hau aikinta, tana yi tana kallon  Mami wacce itama tun tana dubanta m, jefi-jefi tana goge kwalla har bacci ya dauketa.

   Kamar wasa, karamar magana ta zama babba. Tun Mami na ganin lamarin a kanta ita d'aya, har ya soma shafar yaranta. Abba ya chanja musu, ko gaisheshi suka je to ba fa kamar da ba, a yanzun ko yana cikin fara'a suka shiga to fa zai tamkemusu fuska, ya zamana Hajiya Madina bata da girki, abin kuma mamakin bai wuce ganin matan sun had'emata kai ba kamar ma sunyi farinciki da hakan. Idan yaran suka tafi makaranta, Mami haka zata zauna da Ramma da Ummi tana nuna damuwarta a fili don tun tana 6oyuwa har zuciyar ta kasa d'auka. 

           BAYAN WATA D'AYA
  Rayuwa ta yi musu kunci, ayau Ummi suna zaune da Mami a falo suna sauraron rediyo, Adnan ya shigo rai babu dad'i ya zauna d'abas saman kujera yana kunkuni. Mami bata saurareshi ba sai bayan da ta kammala sauraro, ganin an kammala Ummi ta kyalesu su zanta. Ta dubeshi, gaba daya ya bata tausayi ganin yanda ya rame, wannan wasa da dariyar tasa duk ta ragu.
  "Ya akayi d'an Abba?" Ji ya yi kamar ta watsamasa garwashi a zuciyarsa, a yanzu babu wanda ya ke tsananin jin haushi kamar mahaifinsa, ko hanya ya k'i jinin su had'u.  Ya k'ara tamke fuska.
  "Please Mami ki bari."
  Mami ta yi murmushi, ita kanta ta rame matuk'a, a baya Mami ba dai ta zauna ta yi hira da su Ummi ba, halin rayuwa yasa duk ta yi sanyi don har Ummi tana bawa ta yi mata sadaka a kofar gida. Hakanan gaba daya sun dage da addu'a, ko ta ji kamar ta sanarwa iyayenta sai wata zuciyar ta hanata, gani takeyi kamar ba jimawa komai zai yanke.
    "Shikenan, gayamin, meyafaru na ga ranka a 6ace?"
  Ya numfasa gami da cizan le66ansa na k'asa. Dakyar ya k'ok'arta ya yi magana.
  "Zan bar gidannan Mami."
Gabanta ya fad'i ta zaro ido tana ambaton Innalillahi a ranta.
  "Kamar ya za ka bar gidannan Adnan? Meya faru kuma?"
  Ga mamakinta, hawaye kawai ta ga ya soma. Hankalin Mami ya tashi yaronnata akwai hakuri da dakiya, sai ta iya k'irga sau nawa ta ga kukan Adnan tun tasowarsa. Ta yi shiru lokacin da ya katse tunaninta inda ya soma magana.
  "Wai yau ni Abba ya kira da zargin nayi mishi sata, wai jiya da dare bayan na fito ya yimin fad'an ya fasa turani k'asar waje karatu shine da safe ya laluba bai ga wasu kudadensa da ya bari a falonsa ba, shine yau ya kirani akan wallahi sai na fito mai da kudinsa har Umma na fadin tabbas ta ga sadda na fita wai ina gyaran aljihu. Ni bazan iya rayuwa a gidannan ana tafiya haka ba, na gaji Mami, zan yi nesa da ku."
   Yana kaiwa nan kawai sai ya cigaba zubar kwalla har yana sheshshek'a. Idan hankalin uwar ya yi dubu to ya tashi, duk a lamarinnan, bata ta6a kuka gabansu ba sai a yanzun. Kuka sosai ta shiga yi, yau Mijinta Modibbo ne ke kiran d'anta da sunan 6arawo, wane irin tashin hankali kenan ya ke faruwa dasu?
   Jin kukanta ne yasa Ramma da sauri ta fito daga kicin harma da Ummi wacce itama ta ji hankalinta ya yi tsananin tashi.
  "Hajiya lafiya?"
Cewar Ramma. Adnan ma kukan yakeyi babu mai bawa wani hakuri, karshe a fusace ya mik'e ya fita daga falon. 
  Ummi tuni ta soma kukan itama, Ramma da jiki ya gama sanyi ta karasa ga abinda uwardakinta ta russuna.
  "Haba Hajiya, haba, idan kina haka agaban yarannan sai ki karyamusu zuciya, komai na rayuwa idan ya samu bawa hakanan ya ke hakuri ya dangana. Addu'a kadai ce mafita, duk wannan fa bazai sanya abubuwa su chanja ba sai addu'a."
  Mami ta jinjina kai idanu a kod'e ta dubi Ramma.
"Yanzu har yakai Alhaji da soma zargin d'ansa da sata?"
  Abinda ta fad'a ya yi mugun kad'a hanjinsu. Ramma ta hau salati, ita kuwa Ummi daskarewa ta yi kukanma ya kasa fitowa. Basu kai ga samun abin fad'a ba suka ga Adnan ya shigo goye da k'atuwar jaka fuskarsa duk ta kumbura. 
  "Zan wuce Mami."
  Daga haka ya yi gaba, Mami ta mik'e tsaye da azama gami da dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa.
  "Adnan." 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

38
Chapter 25 · 0% Book details