← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 116

Sashe 84

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Har la'asar, Ummi na mak'ale wajen Abida ta kasa fitowa. Tana cikin sallah   ya shigo, tana ji suna magana k'asa-k'asa da Abida, sai kuma ta ji Abida ta soma bud'a wanda ya sa Ummi gabanta ya fadi adaidai lokacin da ta sallame. Furucin da Abida ta yi ne yasa ta durkuso a wajen tana salati....!
   "Alhamdulillah, Allah Shi ne abin godiya, amma ya akayi haka ta kasance?" Cewar Abida kenan.
"Wallahi abu na Alllah, da kansu suka buk'aci hakan sai kuma Malam bai musa ba don a farko sun bukaci komawarta Abujan saboda karatun da ta soma amman bamu amince ba, sai suka yanke shawarar kan a daure auren kawai, to shine fa aka daura, tarewa kuma aka barshi nan da wata daya."
   Duk wannan bayanin da Baffa ke yi a kunnen Ummi, ta ji jikinta ya yi mugun sanyi, take ta ji ruwan hawaye na kwaranyo mata, wai shikenan ta zama MATAR AURE? Ta zama mata wajen Umarul-Faruk Danzaki? Allah mai Iko, yanzu komai za ta yi saida izninsa? 
  Tana nan durkushe saman darduma tana hawaye, Abida ta shigo bayan fitar maigidanta. 
   Ta rik'ota.
"Haba Ummi, kukan menene? Godiya za ki yiwa Allah, wannan ikon naSa ne anzo da zummar a sanya rana aka daura aure gaba daya kinga kuwa babu mai yin hakan sai Allah."
  Haka ta ja ta har suka isa dakin Dada, nan sauran jama'ar gidan suka yi mata caa, ita kuwa jikin Dada ta shige tana kuka, kukan da batasan dalilinsa ba. Hakanan ba zata iya tantance yanayin da ta ke ciki ba, farin ciki ko akasinsa. 
   Kiran da Malam ya aiko ayimata ne yasa ta dan nutsu. 
   Har lokacin daman hijab dinne jikinta, tana tafe kanta a k'asa har ta shiga rumfar Malam inda anan su Daddy ke zaune, sun yi sallah sun ci abinci. 
  Bata iya kallon kowa ba ta durkusa ta gaishesu, suka amsa. Daddy ya ce.
"Ke kuma daga mun bawa Balarabe aronki shikenan sai ki mak'ale ki gujemana?"
Ya karashe da dariya, su dinma dariyar su ka yi ita dai murmushin yak'e ta yi don har lokacin jikin ba dadi. 
   Ta mike ta tafi bayan sun sallameta, a ranar su Daddy suka koma. Bayan tafiyarsu Malam ya kara kiranta. Zaune ta samesu su uku, da Baffanta Haruna sai Babanta da kuma Malam din. 
  Malam ne ya soma magana.
"To Hasiya, kinga dai yanda Allah Ya yi lamarinsa ko? To inaso ki yarda da hakan a matsayin kaddararSa, Allah Ya yi yau din ita ta kama ranar daurin aurenki ba baiko ba. Sadakinki dubu hamsin muka kar6a don neman albarka cikin aure. Yanda su ka ce, gobe litinin zasu turo direbansu idan yaso a wuce da ke can, sun buk'aci komawarki zuwa zuwa lokacin bikin ba don komai ba sai domin karatun da ki ka soma kada ayi miki nisa. Ina fatan ba za ki bamu kunua ba Hasiya?"
  Shiru ta yi cike da jin nauyi yayinda hawaye ya zubomata don babu abinda ya fado ranta sai matan su Babban Yaya da kuma Ikram da abokiyarta Ihsan wadanda a rayuwa basu kaunarta, a gefe kuma wane irin kallo Mami za ta yi gareta?
Malam ya cigaba da nasiharsa, a karshe shima Baffa Haruna ya tofa nasa sannan ta suka sallameta ta koma ciki. 
  Da Magriba tana kwance saman gadon Dada duk jiki babu kwari ta luluk'a cikin duniyar tunani wayarta ta yi k'ara wanda har saida ta firgita, salati ta yi sanya a hankali sannan ta janyo wayar, gabanta daman tuni ya ke bugu da sauri-sauri, ta sauke ajiyar zuciya ganin ba wanda ta zata bane. Ganin sunan Antinta Amina yasa ta dagawa da sallama. Dariya Amina ta yi bayan ta amsa tana mai rangad'a bud'a. Ummi ta runtse ido tana murmushi kawai. 
"Kai Ummi, wato maimakon ma ya kasance ni ce farkon ji shikenan saidai na ji a wajen su Hajiya Mama? Ba ki bugomin waya ba?"
Ita dai Ummi shiru kawai ta yi mata, dariya Amina ta yi, ai nasan daman babu abinda za ki ce. To Ummi, Allah Ya sanya alheri, hakika na tayaki farinciki sosai. Nima gobe za mu wuce Nijar yanzu haka ma ina tare da Inna.
Sai lokacin ta yi magana.
"Allah Ya kaiku lafiya Anti, ban ita mu gaisa."
Amina ta mik'awa Inna. Bayan sun gaisa Inna ta yi mata fatan alheri, murmushi kawai ta yi a kunyace ba tare da ta amsa ba, Inna ta dan yi mata nasiha kadan sannan ta mik'awa Amina wayar suka yi sallama. 
   Ta ajiye wayar tana shirin komawa ta kwanta Dada ta shigo.
"Wai ke ba zaki tashi haka ba ki sanya wani abu a cikinki?"
Ta dan tur6une fuska.
"Dada bana jin yunwa fa."
Dada ta zauna gefenta tana murmushi.
"Ina fa za ki ji? Farinciki ya cika miki ciki kinmin kwacen miji kin ji dadi ko?"
Batasan sadda ta 6oye kanta a saman cinyar Dadan ba, kamar za ta yi kuka ta ce.
"Kai don Allah Dada."
Murmushi Dada ta yi gami da dafa kanta.
"Allah Ya yi miki albarka Hasiya, Yasa ki gado mahaifiyarki wajen hakuri a zamantakewar aure duk kuwa a hakan ma na fahimci kema mao hakurin ce. Wannan aure, auren gata ne, bazan 6oyemiki ba, a dan zaman da yaronnan ya yi tare da mu na fahimci da yawa cikin kyawawan halayensa, kwarai yana sonki don banajin ko Abdullahi mahaifinki yana miki son da Umar ke yi miki. Ki yi biyayya ga dukkanin umarninsa, ki dage ainun ki bawa marar d'a kunya wajen neman ilimi Hasiya, wannan shine babban gatan da ki ka rasa a baya, kada ki sake ki yi wasa da ita. A kulkum ina k'ara ganin daraja da k'imar Hajiya Madina, wacce a labarin da ki ka bani itace farkon wacce ta soma yi miki gatan sanyaki neman ilimin addininki. Allah Ya sakamata da alheri, Ya jik'an Hasiya."
Kuka ciki-ciki Ummi ke yi, da gaskiyar Dada, Mami ta taimaketa a rayuwa, babu abinda za ta iya yi ta biyata ita da Abba face addua. 
   Haka Dada ta yi ta rarrashinta sannan ta mike ta shiga hadamata kaya bayan ta lalla6ata ta zubamata abinci. Anan Ummin ke jin ashe ba ita kadai za ta wuce ba, har da rakiyar Abida da mijinta Baffa wadanda zasu kawai don ganin waje bisa umarnin Malam. Ta ji dadin hakan.
  Karfe tara na dare, Anti Halima da Anti Abida suka sanyata tsakiya sunata yi mata nasiha. Ita dai ta kumbura ta yi fum don bata ga amfanin nasihar ba tunda ba tarewa za ta yi ba.
"Yauwa, kuma karki sake ki zubda ajinki, karki ba shi fuskar da wani abu zai shiga tsakaninku, zai fi d'okin ki, wallahi ki kiyaye. Duk abinda zai je ya zo karki bari wannan kunuar taki ta yi saurin tafiya kinji ko? Idan ku ka yi hakuri wata daya kamar yau ne." Cewar Anti Halima kenan.
'Wayyo Allah.' Cewar Ummi a zuciyarta kafin ta yi soma kwalla, wadannan me su ka maidata ne? Ganin hakan yasa suka yi dariya don su ganin Ummi suke yi kamar kanwarsu ba diyarsu ba. Ta mike a guje ta bar musu saman tabarmar ta koma cikin daki wajen Dada.
"Au ki ka gudu ko? Ai yanzu aka soma." Cewar Abida kenan cikin daga murya. Dada wacce har ta kwanta ta dubeta saidai ba ta ce komai ba.
  Kamar jira akeyi ta shigo dakin, wayarta ta soma k'ara, ita kam yanzu duk sadda ta ji k'arar wayar ma sai gabanta ya fadi. Adnan ne, ta ji kamar kada ta daga, shikenan fa labari ya zagaya ga kowa. Ta dan dubi Dada wacce idanunta ke rufe kafin ta d'aga da sallama. Bud'ar da ta ji ya yi ne, yasa ta dariyar da bata shiryamata ba ga kuma kunya da ta ji, yau kuma namiji ne da bud'a? Wannan abu lallai ya bata dariya.
  "Kai Yaya Adnan."
Ta fada tana dan marairaice murya. Ya yi dariya.
"Da girman kujerarki Antina Matar Best, tuba nake ranki ya dade nasan na yi lattin tayaki murna, abubuwan ne sai a hankali, sannan don Allah ki daina kirana da Yayan nan, yanzun ma kina fad'a kamar na nutse don kunya."
Dariya ta k'ara yi tana mai sa hannu ta rufe fuskarta, ba zata iya rike dariyar ba, shi dai Adnan ba dai iya tsokana ba. Shima cikin dariyar ya ce.
"Atoh, ai gaskiyane, yanzu idan My Best ya ji ai sai ya dauki fushi da ni. To Allah Ya sanya alheri, Ya nunamana ranar aurenku, abin dai zai min takaici don inaga watan zamu soma jarrabawa kinga ba lallai na zo ba."
Ta gyada kai tamkar yana ganinta.
"Allah Ya baku sa'a."
"Amin, ina Amarena? Kakanninmu."
Ba ta yi mamakin Adnan ba, daman ai Shi Allah babu ruwansa, idan Yaso sai ya yi daya mai kyakkyawan zuciya acikin dubu, to ballantana kuma suma su Ihsan din rashin fahimta ne yasa suke mata hakan.
  Tana dariya ta amsa da duk lafiya. Sun dan ta6a hira yana jifanta da tambayoyi akan Gombe tana amsawa a karshe suka yi sallama.
  Babu jimawa kuma ta ji wani kiran alokacin da ta ke kokarin kwanciya, shi ne dai wanda ta ke gujewa kirannasa. BABBAN GORO, UBAN GAYYA...!!!
   Ta zubawa wayar ido kamar ba zata amsa ba, sai faman safa da marwa numfashinta ke yi, har dai ta kusa yankewa sannan ta yi bismillah ta amsa. Shiru ba ta ce komai ba shima baice ba, can kuma ta ji ya sauke ajiyar zuciya ya yi sallama cikin sanyin murya.
   Ta amsa itama kamar wacce aka shak'ewa wuya don dakyar muryar ta fita.
   "Kema hawayen ki ke yi kamar ni?"
Ya fada a shagwa6ance, ta rufe bakinta da hannu don dariyar da ta so su6uce mata. Ya cigaba da magana.
"Dagaske nake fa, wannan idan zan rabu da Hajiyata sai yaya? Kawai kina shirin rabani da gidanmu ko? Dazunnan Haidar ya gama yimin dariyar mugunta ya tafi."
  Ta hadiye dariyarta ta maidashi murmushi mai bayyana hakora.
"Um." Shine kawai abinda ta ce sa'ilin da ta saci kallon Dada, minsharin da ta ji ne ya tabbatar mata cewar yanzun ta yi nisa da bacci.
  "Tashi Ummi, tashi mu yi salla mu mik'a godiyarmu ga Allah, zan k'ara kira karki kashe wayar kinji?"
  Ta gyada kai kawai, saida ya kara maimatawa.
"Kinji?" Alokacin ta amsa da to, bai jira cewarta ba ya katse kiran.
Ta bi wayar da kallo tana murmushi, soyayarsa na k'ara ratsa dukkan sassan jikinta, fita ta yi, babu kowa a tsakar gidan duk an shiga makwanci, alwala ta dora bayan ta kama ruwa sannan ta koma dakin ta tada sallah, ta jima tana adduo'i har da hawayenta kafin ta shafa ta mike. Mintuna biyar bayan haka, har ta fidda ran zai kira don lokacin sha daya ta kusa sai ga kirannasa. Ta daga da sallama, ya amsa kafin ya tambaya ko ta yi? Ta amsa da eh.
"Alhamdulillah." Ya maimaita sau uku sannan ya cigaba da fadin.
"Matata."
Ta ji sunan har cikin jini da jikinta, ta lumshe ido tana murmushi ga kirjintata dake lugude da sauri-sauri, saidai ta kasa amsawa, ganin abin ta ke yi tamkar a mafarki.
  "Matata Hasiya, ko ba ita bace? Kina jin mijinki na kira ki ka yi shiru ko?" Ya karashe a shagwa6ance, ai daman tasan ko wata macen ba fa zata nunawa Faruk shagwa6a ba, don ko ita ba zata iya yanda ya ke yi ba.
  "Um." Ta fada kanta na k'asa tana wasa da kasan t-shirt din dake jikinta na bacci.
  "Kin zama matata yau, shikenan na girma, haka Hajiya ta ce."
Har lokacin murmushin ne dai ta yi.
"Gobe za ki zo gareni Hasiya, ina fatan kin shirya tarbata?"
Ta zaro ido a tsorace.
"Kamar ya?"
"Au ba ki sani ba? Shikenan sai kinzo din."
Ta tsorata, ta tunano maganganun su Anti Halima, ya zama dole ta yi takatsantsan don kuwa dagaske ba fa za ta bari ajinnata ya zube ba.
   Ya cigaba da janta da hira, hirar da ba zata iya dauka ba, ganin dai dagaske ba zata bude baki ta ce wani abin ba yasa shi yi mata sallamar dole ba don yaso ba. Daga nan suka kwanta kowanne zuciyarsa cike da begen dan uwansa....!
  Washegari...!!!
Chapter 84 · 0% Book details