← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 116

Sashe 32

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

45
  Yana saukowa daga bene, tana tahowa, ta ji numfashinta na barazanar daukewa tsabar had'uwar da ya yi. Ya gama hadewa cikin kufta bak'i wanda ya sha aiki dinkin riga da wando, ya sanya hula, sanyawa na musamman don kuwa ya zauna dabas a kansa. Takalminsa bak'i sai shek'i yakeyi. Bak'in gilas ne a idanunsa bazaka iya tantance inda ya ke kallo ba, saidai jikinta ya bata ita din ya ke kallo shima.
   Kamar kuwa tasan hakan, domin babu abinda Faruk ke kallo irin tsarin halittarta. Yarinya cikakkiya, da ace ta samu jin dadi fiye da wanda ta ke ciki da babu abinda zai hana tsantsar zubin halittarta fitowa fili. Ya kai kallonsa ga le66anta masu surkin bak'i da ja wanda hakan ba karamin k'awata siririyar fuskarta ya yi ba, ya lashi nasa le66an gami da kauda kai daga kallonta. Itama ta yi niyyar wuceshi sai kuma ta hango rashin dacewar hakan, wannan yasa ta tsayawa har ya karasa saukowa sannan ta durkusa ta gaisheshi. 
  Ya amsa yana mai kai hannu da niyyar kar6ar Tahir. Ba musu ta sakarmishi shi. Cillashi sama ya hau yi yana mishi wasa, nan yaro ya hau dariya. Ita kuwa batasan ya akayi ta tsinci kanta da sakin baki tana mai dubansa ba. Wani irin kyau ta ga ya yi mata musamman yanda fararen hakoransa suka fito yana dariya. 
  Ganin zai kallota ne yasa ta saurin sunkuyar da kanta. Babu kowa awajen domin gaba daya suna can wajen taro, ya durkusa kamar yanda itama ta ke a durkushen. Gabanta ya cigaba da lugude har da surfe(lol), wani kamshi na turaruka ke bugun hancinta wadanda suka kashemata jiki. 
  "Kinyi kyau." Kasa gaskata abinda kunnuwanta suka ji ta yi, hakan yasa ta dago ta dubeshi, ya cire gilas din idanunsa, ya zubamata ido da murmushi a saman fuskarsa. A rud'e ta ke waige-waige babu wanda ta gani domin dai ba'a fiye zuwa wajejan ba matukar ba wani abu babba ne ya taso ba, sai ko su din dake kwana a dakunan wuraren. Mikewa ta yi niyyar yi ba zato ta ji ya rik'e hannunta ya maidata durkuson sannan ya saki hannun yana jifanta da kallo fuskarsa dauke da mamaki.
"Wai ban hanaki wannan tsoron ba? Na lura ni kadai kike tsoron ma, ko bakyaso ina shiga harkarki? If yes ki sanarmin sai na daina."
  Ummi fa kiris ya yi saura ta saki fitsari, ta dubeshi da idanunta wadanda suka kawo ruwan kwalla amma basu kai ga zuba saman fuskarta ba, sai kuma ta kasa jure kallon kwayar idanunsa mai k'ara jefeta cikin tsaka mai wuya.
  Ya mike tsaye.
"Rik'eshi." Da sauri ta kar6i Tahir a hannunsa domin dai Allah-Allah ta ke kira a ranta don ya kyaleta ta wuce. Ta rasa sabon lamarin da ke shirin 6ullowa tsakaninsu. Ya maida gilashinsa, ya dubeta da murmushi saman fuskarsa.
"Ke kam ko ni saurayinki ne sai haka. Bansan sadda tsoro da kunya ya shiga tsakaninmu ba alhalin ba shiga harkarki nake yi ba. Yanzun ma dalili ne ya yi dalili."
Ta dubeshi cikin neman karin bayani, ya daga mata gira yana murmushi da gefen kumatu. Kamar mai rad'a, ya furta "Bye." Daga haka ya k'ara gaba.
   'Meyasa ya na jin kansa mai aji idan yana gabanta ne wai?' Wannan ne tambayar da ya cillawa zuciyarsa alokacin da ya ke nufar can bayan inda ake taron domin shiga motarsa ya bar gidan, duk iyakar tunaninsa, ya kasa tunano komai, sai lokacin ya ke jin haushin abinda ya ke yi, ya ja guntun tsaki ya bude motar ya shiga gami da barin gidan. 
   Acan kuwa Ummi ta shiga yanayi mai wuyar fassaruwa, wai yau itace Faruk ke yiwa haka? Kodai yana jin yanda ta ke ji ne? Tasan ba wani so bane, kawai dai jikkunansu da zuciyoyinsu na chanja yanayi duk sadda suka ga juna ba don wani abun ba, hakanan kawai dai. Shine abinda ta ayyana a ranta.
     Koda ta koma Amina ta nemi sanin dalilin jimawarta, fakewa ta yi da fadin dakyar ya yi shiru. Har taron nan ya watse, babu wani chanji daga yanayinta na sanyin jiki da yawan tunanin abinda ya kere ta, yafi karfinta gaba daya ma. 
                    ***   ***   ***
                     KADUNA
  Zaune suke tare da Munira suna faman hira, a haka Deen ya sanyo kai ya iskesu, kamar yanda Munira ta saba, mik'ewa ta yi ta isa gareshi ta taroshi, ya bata kyakkyawar runguma da sumba a kunci. Wani abu ya tokarewa Dija wuya, abin kuma kamar da gayya Deen keyi don ta tabbatar koda bata furta ba, to fa ya fahimci manufarta akansa. Ganin basu ko kula da ita ba, yasa ta amfani da hannu ta tunkude kofin tangaran din dake saman tebur, ji kake taratsatsa. Hankalinsu ya yi saurin zuwa gareta, ita kuwa ta hau salati tana fadin "Wayyo, ina shirin mik'ewa ne bansan na ta6ashi ba."
Munira da sauri ta karasa gareta.
"Sannu yar uwa, ba ki ji ciwo ba? Lanto! Lanto!"
Ta juya ta soma kiran yar aikinta domin ta tattara wajen, Deen kuwa wani kallo na kina sani ya hau watsawa Dija, wani murmushi ta sakarmishi, ya hade girar sama da ta k'asa ya bar wajen zuwa dakinsa.
   Tun daga wannan ranar ta ke faman tsiro da sirfa kala-kala musamman ma idan dare ya yi ta ce bata da lafiya Munira ta yita zirga-zirga kenan zuwa wajenta itama da bata gajiya. 
   A gefe kuwa, ga Raihana wacce ta matsamata da waya da kuma ta whatsapp akan zata iya rasa rayuwarta muddin bata amince da bukatarta ba. Akwai sadda ta budemata wuta ta nunamata ita yanzu haka akwai namijin da take mutuwar so amma ta kasa shawo kansa ya kaunaceta. Raihana ta aikomata audio tana dariya. Ta tabatar mata ko waye shi muddin ta amince da ita to ita mai yi mata komai ce don ta mallakeshi kuma ya aureta a sauk'ak'e. 
  Jin haka yasa Dija kiranta kai tsaye bayan ta rufe dakin gam.
"Me kike nufi?"
Acan Raihana dariya ta yi.
"Wallahi muryarki dadi."
  Banzan tsaki Dija ta ja, batasan ya akayi ta bawa yar uwarta mace wannan damar ba, fatanta dai a yanzu ta samu Deen don gaba daya idanunta a rufe suke.
"Kinga don Allah ki sanarmin idan da gaske kike."
Ganin haka yasa itama ta nutsu.
"Wallahi muddin za ki amincemin babu abinda za ki rasa a duniya Dijat. Kedai ki yarda na zo inda kike kigani."
Dija ta girgiza kai.
"Ki soma yimin aiki akan Deen idan na aureshi na rantse miki da Allah komai kikeso kin samu." Ta karashe a tsorace. 
   Wani ihun dadi Raihana ta saki gami da mannawa kan wayar kiss.
"Angama wallahi, Zahraddeen sunansa ko? Karki damu, yau dinnan zan kira Malamina na ji yanda za'ayi."
"Dakata (please), ki san sunan da za ki kai, kada ki cutar da ni ta hanyar asiri."
  Raihana ta marairaice murya tamkar da wani saurayi ta ke maganar.
"Ba cuta tsakanina da ke don ina sonki. Ki rike wannan." (Wa'iyazubillah)

  Dija ta murmusa ji ta ke yi inama Deen ke gayamata hakan ba jinsinta ba. 
  "Nagode sai na ji ki."
Daga haka suka rabu.
     A sati daya kuwa komai ya kammala, Raihana ta aikomata sak'o ta hanyar wata abokiyar ashararancinta da ke a Kadunan. Itama ta so ta latsa Dija ta ga ba fuska sannan Raihana ta gargadeta akanta kafin ta zo. Koda Munira ta tambayi Dija wacece, cewa ta yi kawarta a yanar gizo. Munira sam hankalinta bai kwanta ba da budurwar don da gani kasan yar duniya ce, haka ta yita yiwa Dija nasiha akan ta kula da wadanda zata dunga kulawa a yanar gizo, wasu da yawa 6ata gari ne. Ta amsa da to kawai. Ta kudurta a ranta sai ranar weekend zata soma amfani da turaren, na wanka kuwa a daren ta yisu. Na zubawa a abinci shima sai ranar da ba aiki. 
Chapter 32 · 0% Book details