← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 116

Sashe 64

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jin haka Hajja ta rausaya kai.
"Ai shikenan na bari."
A karshe ma suka shiga wata maganar inda Modibbo ke fadin ya dace ma su kai ziyara Adamawa don sun jima basu je ba, ya ce idan anyi zaman taro zai fad'a. 
Sai bayan Azhar Hajiya Mama ta iso ita daya sai autarta Mufida. Bayan an gaggaisa suka zauna hira da zaman jiran Mami, ba ita ta zo gidan ba sai yamma. Nan din ma ta zo ne tana daure-dauren fuska, ko kallon inda ta ke Hajiya Mama bata yi ballantana wata gaisuwa ta shiga tsakaninsu. Sai lokacin Hajja ta fahimci akwai matsala. 
Bayan sun zauna har mahaifinnasu, Hajiya Babba ta zayyane batun auren Faruk da Ummi da kuma maganar Ihsan kaf ta fadawa iyayen, sai kuma Hajiya Mama ta dora da yanda suka yi da Madina a gidanta. 
  Shiru ya biyo bayan gama saurare, can kuma Modibbo ya yi maimaita Innalillahi wa inna ilaihir raajiun har sau uku.
  "Hakika shaidan ya so shiga tsakaninku, ina nema muku tsarin Allah daga sharrinsa."
Ya dan yi shiru kafin ya dora.
"Kin bani mamaki Auta, kinyi abinda ban ta6a zatonki da aikatawa ba, da ace wani bare ne ke sanarmin kin yi wannan gagarumin laifin da babu ta yadda zan amince da hakan. Karki manta cewar Aure shi kaddarar Ubangiji ne, idan Allah Ya kaddarowa shi Farukun da ita Ummi aure, to babu mahalukin da zai chanja yin Allah, hakazalika idan kaddararsa ce aurensu su biyu duka, nan ma duk wani tashin hankula da zaayi zai je ya dawo ne ba fa zaa fasa abinda Allah Ya shirya ba."
  Shiru ya dan biyo baya, Mami ji ta ke yi ranta na zafi, wato iyayensu ba su ga hadin da ake so ayi na diyarta da yar aiki ba? To wai ma Faruk kadai ne namiji da har zaayita takurawa akansa? 
  Modibbo ya cigaba da yi mata nasiha don ba shi da zafi sosai, ita kuwa Hajja shiru ta yi, wannan fadan da ake yiwa Madina yafi komai yi mata zafi, tana ji da yar autarta ta. Bayan Modibbo ya kai aya ta soma magana a fusace.
"Nifa banga laifin Madina ba yarinyar nan da gaskiyarta. Ke banda rashin wayo da girman kwabo ki rasa da wacce za ki had'a dangantaka saida yarinyar da bakisan komai game da ita ba, 'yar asali ce, shegiya ce, oho! Duk ba daya da ki ka sani,duka-duka ko wata uku bata cika ba inace tare da mu, kece kuma har da marin kanwarki saboda..."
  Tsawar da Modibbo ya dakamata ne yasa ta yin shiru tana kwafa, zuciyarta na tafarfasa kamar ta rufe Fatima da Sadiya da duka haka ta ke ji.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  82
"Ke meyasa baki da tunani ne? To ko fita idona tun ban sa6amiki ba wallahi! Kina ganin ana kokarin gyara lamari ke kuwa kina neman ki k'ara dagula shi? Ko an gayamaki shi Amadun ba shi da hankali da ba zai yi bincike ba kafin hada zuria da su? Haba!"
  Ya juya ga yarannasa kafin ya kai ga magana Mami ta soma.
"Ka yi hakuri Baffa, amma don Ihsan ita ta hakura, mahaifinta ma ya yi mata miji bata sani ba."
   Ta fadi hakan don ma kada ya ce lallai hakan zaayi, Modibbo ya so fahimtar kawai ta fada ne saidai ya yi tunanin barin mutum da halinsa, ya jinjina kai ransa baiyi mishi dadi game da wannan sa6ani da aka samu ba tsakanin yaransa wadanda ya ke alfahari da su wajen kokarin zumunci da hadin kai.
     Haka dai aka rabu ran kowa babu dadi. 
    Hajiya Babba kuwa ji ta yi kamar ran lahadi ta bi mota ta bar garin Kano sakamakon Hajja da ke ta jifanta da bakaken maganganu marasa dadi, daman Hajja ta na da fada idan an ta6ota musamman idan aka ta6a autarta. Ranar litinin kuwa jirgin safe Hajiya Babba ta bi zuwa Abuja zuciyarta a cunkushe, saukinta ma ta samu goyon baya wajen mahaifinnasu inda ya ce kuma ta dage nemawa dannata za6in Allah, Allah ba Ya bacci, Shi Mai amsawa ne.
   Da wannan hankalinta ya dan kwanta, itama Hajiya Mama ta jaddadamata ta kwantar da hankalinta, karon kanta Mamin zata zo ta gano kuskurenta, wannan zamanin namiji mai rikon aure sai an auna, tana kyautata zato akan Faruk. Madina zata yi da na sani acewarta. 
                    ***  ***  ***
                       RINGIM
  Salati Habiba ta shiga yi tana kallon Saude wacce ta shigo a rude ta zubar da Mariya akan kujera tana rusa ihun kuka sakamakon maganar da wata makwafciyarsu ta kawomata akan ta sanya ido akan yarinyarta don ta ganta sun shiga wani lungu da Dauda fitinannen d'a ga Zinaru itama makwafciyarsu, wannan dalilin yasa ta duba diyar ta tabbatar ana amfani da ita.
  "Kingani ko? Daman na sha kwa6arki akan sakacin da ki ke na barin yarinyar nan tare da wannan yaron, itace har shagon Usi mai kanti, yanzu ga irin ABIN DA AKE GUDU!"
   Ita dai Saude ba bakin magana, don cuta an gama cutarta diyarta kenan daya a duniya, tana ji da ita ta kuma ci buri akan aurenta idan ta girma don yanzu duka-duka shekarunta bakwai a duniya. 
   "Ba kuka ya kamace ki ba, mu lalla6a mu kaita asibiti a aunata ko tana da cutar kanjamau, idan babu duk sauran mai sauki ne."
   Suka dunguma zuwa asibiti, anci sa'a bata da cutar saidai ciwon sanyi da ya yi mata yawa a jiki, likitan ya tabbata musu ana amfani da yarinyar, abu ne da suka riga suka sani, ya nemi yardarsu a yi mata dinki suka k'i acewarsu sunsan yanda zasuyi. 
  Daga asibiti suka wuce wajen bokanya nan ta hadamusu magunguna, anan kuma Habiba ta je da batun matsalar Dija da Raihana, Bokanya ta ce zata yi aiki akai.
  Haka suka wuce ran kowannensu ba dadi, Saude ta so zuwa gidan Zinaru ta zagesu tas saidai Habiba ta kwa6eta gami da nunamata wannan tonon silili ne don wanda bai sani ba ma zai iya sani. Basusan cewa ba, mutanen gari sunsha tarar Malam Balarabe akan ya saka ido akan diyarsa, anan kuma Saude idan ta ga ya hana diyar fita ta nunamishi bai isa ba.  Daman yasan shi din ba shi da wani kata6us a gidan, yan uwansa ma an rabashi da su, ba wanda ke takowa Ringim da zummar ganinsa tun bayan rasuwar Yayar Malam Balaraben da ta rik'eshi, itama har ta mutu bata ta6a haihuwa ba. Daman iyayen na Malam Balarabe sun rasu da jimawa. 
                 ***   ***   *** 
                    KADUNA...

Lamura sun ca6ewa Dija tun ranar da Raihana ta yi mata waya akan tana nan zuwa, ta fahimci dukkan wani abu da su ke yi don a rabasu ya ci tura hakan bai samu ba, ranar da Deen ya koma dakin Munira a ranar Raihana ta zo. Da shirinta ta zo wajenta don kuwa wani shegen kwalli ta sanya a idanunta da yasa Dija kasa yi mata musu a dukkan abinda ta ce, ga wani dan iskan turare mai saukar da shaawa. A wannan ranar Raihana bata bar gidan Dija ba sai dare, Dija kuwa saidai ace Allah Ya kwatota don kuwa tuni ta fada tarkon shaidaniya Raihana. Tun daga ranar suka kara shak'uwa ta waya, har Raihana ta yi zuwa biyu gida, mutan gidan ba wanda ya ta6a kawo munin abu irin wannan a kansu saidai sun shaida Raihana ba ta yi kalar nutsastsun mata ba.
                   ***   ***   ***
                        KANO
Chapter 64 · 0% Book details