← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 116

Sashe 61

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Su kuwa karya kumallo sukeyi hankali kwance, Deen na so ya je ganin Munira saidai yana gudun 6acin ran Dija. Bayan sun kammala suka koma daki, wayarta ta dauki k'ara, ganin mai kiran yasa duk ta dan diririce ta wayance da katsewa gami da saurin sanya wayar a(silent), ta jefa wayar k'asan filo tana murmshin yak'e.
"Mutane ayita takura mutum."
Ya yi murmushi yana mai janyota jikinsa.
"Madam ko za kimin rakiya mu gaisa da yarana?"
  Ta daure fuska.
"Kodai kace za ka ga matarka?" 
Ya ja karan hancinta.
"Ta ci albarkacin yaranki mana."
Zata k'i sai kuma ta tunano da kiran da Raihana ke mata, ta yamutse fuska.
"Jeka kai daya, ni babu inda zanje."
Ya yi murmushi.
"Shikenan." Ya mike ya fita saida ta tabbatar ya tafi din sannan ta ciro wayarta a k'asan filo. Mayyar lokacin m wayar kiranta ne ke kara shigowa. Takaici ya isheta, ita fa yanzu duk ta ficemata aka, idan ma abinda ya shafi bukatarta ne to yanzun ta samu mai daukemata, duk wannan haukan ya fice daga kwanyarta daman ba ta6a aikatawar ta yi ba a fili. Ta daure ta kai zuciyarta nesa ta daga wayar. Daga can kuwa Raihana har wani gwauron numfashi ta saki wanda Dija ta ji shi har ta ji kamar ta shiga wayar ta mak"urota. Ta daure "Kin kira ban kusa."
  "Eh kina can kina amarci ai, ni na dauka ma ko wani laifin nayi miki."
  Ta cije le66anta.
'Laifin uwaki.' Ta fad'a a ranta, a fili kuwa ta dan yi murmushi mai sauti.
"Haba ni ina na yi wannan isar da za ta ce haka gareki? Ko kusa."
"To ya ango? Dijat kada fa ki k'i cika alkawarin da ki ka dauka, ki yi hankali, idan har ki ka ce za ki juyamin baya zan iya daukar kowane mataki."
  Hankalin Dija ya tashi, yau ta shiga uku, hankalinta ina ya tafi da ta mance da batun bokanyar uwarta har ta amince da Raihana akan ta sama mata mafita? Kodayake lokacin ji ta ke ko menene ma zata iya aikatawa matukar zata samu ta auri Deen.
  "Kinyi shiru."
Ta dan gyara murya.
"Ina na isa na mance da hakan? Karki damu ina sane."
Raihana ta yi dariya.
"Ina Kaduna, da zarar kin gama satin amarci, zamu soma namu."
  Ai saita mike tsaye tsabar kaduwa. Kasa magana ta yi ta kashe wayar gaba daya, ta koma ta zauna gefen gado. Babu wata mafita face na kiran Babarta, dole ta bar yin rufa-rufa gareta yanzu, idan yaso ta je mata wajen Bokanya ta gayamata duk halin da ake ciki. 
      Acan kuwa, Deen ya shiga dakin Munira, tana zaune gaban madubi daga ita sau daurin kirji ta yi wanka. Ganinsa ba sai ta juyo ba, sallamar ma a ciki ta amsa. 
   Zama ya yi gefen gadon yana dan satar kallonta tana shiryawa, tunaninsa bai wuce tsakanin matannasa biyu ba wace ta fi k'ira? Yana lura da abubuwa da dama wanda Munira ta mallaka, Dija bata mallakesu ba saidai ya dan lura da ramarta, ya kasa jurewa ya mike ya isa gareta gami da rungumota ta baya.
  "Wai ba gaisuwa?"
Ta tureshi kadan sannan ta gaisheshi, ya amsa. Cikin gatse ta tambayi amarya, ya shafi kansa ya amsa a dan kunyace.
"Idan na kammala abinda nake na je mu gaisa."
  "Am ina yaran nan?"
Ya fada cikin basar da wancan maganar, ta watsamishi wani kallon da bata shirya ba.
"Ka manta yau litinin?"
Ya jinjina kai yana dan kame-kame.
"Oh hakane fa."
Daga haka bata k'ara ce mishi uffan ba, har ta kammala shirinta ta hau gyara, ganin haka yasa shi ficewa sum-sum. Ta bishi da kallon tausayawa kanta. Kamar ba Deen din da ta sani ba, gabadaya ya chanja, ta soma tunano kyakkyawar rayuwar da suke gudanarwa kafin zuwan Dija, yanzu kam babu shi. Hawaye ya zubomata, ta kasa cigaba da aikin don daman kanta ciwo ya ke, kwanciya kawai ta yi bayan ta sha magani, cikin taimakon Ubangiji kuwa bacci ya yi awon gaba da ita.
                    ***   ***   ***  
                        ABUJA
  Ta rude iyakar rudewa jin da ta yi wai yau zata koma gefen dakin da Ikram ta ke wato dakin Baraka harma da batun da Binta ta zo mata da shi na cewar ayau dinne sabbin yan aiki biyu zasu zo. 
   Binta ta zunguri kafadarta.
"Wai kina daukar hakan wasa? Wallahi dagaske nake, Hajiya na ji tana sanarwa Ikram kar kiso kiga yanda yarinyar nan ta hada fuska, karshe ta kwalamin kira ina daga kicin akan na zo na kiraki."
   Ummi ta jinjina kai, wato shikenan ta tashi daga matsayin 'yar aiki? Allah kenan mai yanda ya so.
   Jiki a sa6ule ta bi bayan Binta, ai kuwa kamar yanda Binta ta fad'i haka dinne ya tabbata wato dai za'a chanja mata muhalli, ita kuwa Binta ta samu k'arin albashi wanda yafi ba baya tsoka. Wannan abu ba karamin dadi ya yi mata ba.  
  Ita ta taimakawa Ummi suka gyare dakin tsaf, dakin sak irin na Ikram ne, saidai bambanci and kala, na Baraka komai adon ruwan hoda akayi, ita kuwa Ikram (sky blue)da fari. 
   Binta cewa ta ke..
"Ki godewa Allah Ummi, Allah Ya daukaka ki lokaci guda ke kam alherin Allah ne ya kiraki Kano ki ka hadu da Yalla6ai har ga shi sanadinsa kin samu matsayin dab an ta6a ganin wata 'yar aiki ta samu ba. 
  Ummi kam murmushi kawai ta ke, gaskiyar maganar kenan da Binta ta fad'a. A ranta godiya kawai ta ke ga Allah, saidai a gefe guda tana jimamin haduwarsu da Antinta Amina, anya lamarinnan zaiyimata dadi?
    Bayan sun kammala ta zauna bakin gado ta zuba tagumi tana kallon Binta wacce ta dage sai an jera kaya a sif, ita kuwa sam bata so hakan ba, gani ta ke kamar za'a maidata sashenta. Ta daga kai ta dubi(Ac) da Binta ta kunna sai aiki ya ke yi, acewarta gwara ta dinga shan ra6a itama ta murje. 
   Aka banko kofar aka shigo babu ko sallama Ikram ce, ta rike k"ugu tana bin dakin da kallo kafin ta yi musu duba na raini. Sai kuma ta kyalkyale da dariya.
"Abinka da wanda bai saba ba kenan."
   Ta dauki(remote) ta kashe Ac, sannan ta dubi Ummi tana yamutsa fuska.
"To sarauniya dangin matsafa ki zo Hajiya na kiranki."
   Daga haka ta fice bayan ta yi wurgi da remote din har yana dukan k'afar Ummi. Ummi murmushi kawai ta yi ba tare da nuna damuwa ba ta dubi Binta.
"Ina zuwa."
Binta ta yi kwafa.
"Wallahi da ni ce ke Ummi sai na gayawa yar banza bak'ar magana, bansan sadda Ikram ta 6aci haka ba. Wallahi ki daina ragamata, ya dace ki dunga kwatarwa kanki 'yanci, ko babu komai yayanta za ki aura."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

79
  Ummi da har lokacin bata bar murmushi ba ta ce.
"Meye duniya? Wataran don kanta za ta gaji ta bari."
  Binta ta ja tsaki.
"Ai ke daman hakurinki kusan ma ince ya yi yawa, ba fa komai za ki zuba ido ayimiki ba wannan raini ne."
  Ummi ta yi hanyar fita tana fadin.
"Gwara dai na tafi kada na yi laifi."
"Je ki dawo ranki ya dade!"
Ta karashe cikin zolaya, itama Ummin tana jinta bata tanka ba bayan dariya da ta danyi.
  A falon sama ta tarar da Hajiya, agefenta wasu atamfofi ne da leshi. Sai wata mace wacce daga gani ba bahaushiya bace zaune a can gefe. Bayan ta gaishesu ne, Hajiya ta bata umarnin zuwa ga matarnan.
  "Hafsa aunata."
Wacce aka kira Hafsa ta amsa da gur6atacciyar hausarta sannan ta shiga auna Ummi bayan tasa ta cire hijabin jikinta. 
   Saida ta gama sannan Hajiya ta bata umarnin tafiya, haka ta koma daki jiki duk a sanyaye, wato har dinkuna zaayi mata.
   A kwanaki uku kuwa sai ga Hafsa da dinkuna kala goma kala-kala. Atanfa biyar leshi biyu sai wasu yadi guda biyu. Ta rasa bakin godiya tsabar murna, Hajiya kam ta sha addua har saida ta dakatar da ita da fadin"Yiwa Kai ne." A ranar kuma ta hadata da Ikram don ta zuwa siyo kayan undies da na shafa. Jin da Ikram ne Faruk ya kira wayar Ikram ya yi mata gargadi da babbar murya don tun a daren da Hajiya ta sanarmata ta ke faman cika da batsewa, ya tabbatar mata ya lura da hakan. Hakan da ya yi sai ya samawa Ummi lafiya, Ikram na dawowa daga makaranta suka wuce. Har gaba ta ke yi wai don kada su jera da Ummin don ta lura sai wani d'ar-d'ar Ummin ta ke na rashin sabo da shiga ire-iren wajen da sai dan wane ko wance. Don mugunta babu abinda ta za6ar mata saita barta da za6in wannan yasa Ummi ta d'ibi undies kala bibbiyu, a 6angaren shafa ma ta rasa kalar da ya dace kawai sai ta dauki wani(Cream) da batasan ko na menene ba, hoda ma ta dauki daya sai janbaki da jagira, daganan Ikram ta fiddo kudi masu yawa ta ciri adadin abinda Ummin ta dauka ta biya suka tafi babu mai yiwa wani magana. Ummi gaba daya sai ta ji tausayin kanta, wane irin rayuwa ne haka za ta yi cikin mutanen da suka fi ta? 
'Allah Ka dafamini." Ta fad'i a ranta.
Chapter 61 · 0% Book details