← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 116

Sashe 51

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ji takeyi kamar ta gudu tsabar rud'ani. Binta na sambatu tana feshe mata jiki dq turare, hakanan mayafinta shima ta bi ta fesheshi sannan ta yafamata akanta. Takalmin ta mik'omata ta sanya, banda Masha Allah babu abinda Binta ke kira don iyakar haduwa ta hadu, kai ka rantse dinkin aunata akayi. 
  "Ni ganinki nakeyi kin saje da mutan gidan, babu wani bambanci."
  Anan ne Ummi ta murmusa don gani takeyi kawai zolaya ce don Binta ba laifi akwai barkwanci. Suna nan zaune Binta ta bata baki wayarta ta dauki k'ara. Ta yi sakato tana dubanta, ganin zata katse yasa Binta mik'amata.
  "Ki d'aga mana."
Ta kar6a hannunta har rawa yakeyi ta d'auka. A kunnenta ta kara, bai bari ta ce komai ba sai cewa da ya yi.
  "Fito."
Ji ta yi cikinta ya bada wani sautin k'ululu. Tuni ya katse kiran, ta mik'awa Binta wayar sannan ta dubeta idanunta har sun ciko da kwalla.
"Don Allah ki tayani addu'a."
Tausayinta ya kama Binta, Binta ta rik'e hannunta.
"Allah Yana tare da ke, na tabbatar zai taimakeki, ki saki ranki. Komai na Allah ne."
  Ummi ta mike jikinta a sanyaye ta fita. Ido hud'u sukayi da shi yana tsaye a bakin matattakala ya sanya kafarsa daya jikin bango yana danne-dannensa a waya. Ya yi mata kyau kwarai dagaske haka kuma ya bata mamaki, sai kace wasu Amarya da Ango duk yasa su yin shigar kaya masu kyau, shi dinma wani boyel fari k'al yaa sanya da hula wacce ta dace da kayan.  Tunda idanunsa suka sauka akanta, ya kasa daukesu, daskarewa ya yi a wajen kawai don  ya yi kamar zuciyartasa ma tsayuwar ta yi. Haka har ta k'araso wajenshi ta tsaya gefe tana wasa da jelar mayafin. Yasa hannu ya dago ha6anta, idanunsu cikin juna sannan ya kauda hannunsa.
  "Kinyi kyau matuk'a."
  Ta lumshe ido gami da kauda kanta cikin bugun zuciya mai sauri. To Faruk ina wani kyau a wajenta idan aka had'asu? Gaba daya ganinta ta keyi wani tsami akansa, ta k'ara raina ajinta kwata-kwata, har ta hangowa kanta irin kyamar da za'a nunamata yau. Watakil ma su Ihsan su yi mata dariya. Idanunta ya yi kwal-kwal. Hannu ta ji yasa ya janyo mayafinta ya dan rufe kusan rabin fuskarta da shi.
  "Muje." Ya yi maganar cikin dusashshiyar murya. A hankali suka soma takawa, Faruk shi kansa dakewa yakeyi don ba shi da yak'inin samun goyon baya, yana dai ji a jikinsa kawai zai yi nasara idan Allah Ya so.
  Haka har suka shigo falon Hajiya, babu kowa, daman hakan yafi buk'ata, yasan a wannan lokacin Hajiya na sashen Daddy, kai tsaye kofar zuwa sashen Daddy ya shige. Anan kofar falon ya dakata gami da umartar Ummi da tsayawa anan. Ba musu ta tsaya, ta bishi da kallo har ya shiga da sallamarsa, kirjinta ta dafe jin irin yanda ya ke bugu fiye da baya, addu'o'i kawai ta ke karantowa. 
  Daddy da Hajija suka amsa sallamar dan nasu fuska a sake. 
    Ya karasa yana taku a kasaitance ya zauna a gefen kafafun Daddy ya gaishesu. Suka amsa suna k'are mishi kallo. Daddy ya kasa hak'uri ya tofa.
  "Wai ni kodai wajen surukartawa za ka tafi ne? Wannan ado haka?"
  Ya shafi k'eyarsa da murmushi saman fuskarsa, Hajiya na dariya.
  "Daddy na je na dawo, kuma tare muke da ita ma yau za ku ganta."
  Sai Hajiya ta hau salati.
"Kai Sadaukina, haka kuma akeyi babu sanarwa? Maimakon ka fad'amin a shirya?"
  "To yanzu dai ai magana ta k'are tunda daman ya sanarmana a satinnan zai kawota, kinsan halin d'annaki komai nashi daban ne."
  Cewar Daddy yana duban matarsa kafin ya maida dubansa ga Faruk.
  "Tana ina ne?"
Faruk ya dubesu, su dinma shi suke kallo fuskokinsu a sake. Hakan ya k'ara mishi wani k'arfin gwuiwa, ya mik'e tsaye ya nufi hanyar waje. 
  Ya dubi Ummi wacce ya tabbata a rud'e ta ke. 
  "Addu'a zakiyi, Allah na tare da mu."
Ya fada cikin muryar rad'a. Ta gyada mishi kyau kafin ya bata hanya.
"Bismillah."
  Dagowa ta yi ta dan bude fuskarta ta dubeshi kamar zata yi kuka, ya jefeta da kallo mai sanyaya jiki, dole ta maida ta rufe fuskarta sannan ta saka k'afa da sallama, shima ya biyo bayanta. Iyayen suka amsa fuskarnan a sake, suka zuba mata ido har ta k'araso ta zauna, Hajiya dai gani ta ke kamar muryar da kuma tafiyar ba yau ta soma ganin irinta ba. Ta dai danne, ta amsa gaisuwar surukarta ta wacce ke ta bad'ad'a k'amshi. Kafin su kai ga tambayar wani abu, Dakta Ridwan ya yi sallama ya zo gaida iyayensa. 
  Ya dubi Ummi sannan ya dubi Faruk yana 'yar dariya.
  "Ikon Allah, ashe na zo a daidai, da rabon ayi da ni."
Sukayi dariya iyayen, shi kuwa gogan murmushi kawai ya yi. 
   Dakta ya gaisar da su Daddy sannan aka zauna yana fadin shi fa sai ya ga fuskar surukarsu. 
  Ikram ce ta shigo rik'e da hannun yaron Dakta, Ma'aruf, wanda ke faman rigimar zuwa wajen ubansa. Nan itama ta yi sararo tana duban Ummi.
  "K'araso mana, yau fa babbar bak'uwa mukayi, matar Sadaukin Hajiya."
  Ikram ta dubi Hajiya, Hajiya ta kauda kanta, to me za ta ce? Idan Faruk ya ce ga wacce ya ke so ya zata yi? Batun Ihsan ne sai yanda sukayi da shi. 
  "Mene sunanta ne?"
Daddy ya tambaya.
"Hasiya." Cewar Faruk, Ummi ta lumshe ido jikinta na rawa, tana gudun ace za'a bud'e fuskarta. 
  Ikram ta saki hannun Ma'aruf sannan ta karaso tana yar dariya na dole.
"Nidai sai naga fuskar Antina."
  Kafin Ummi ta yi wani yunk'uri, ta d'an bud'e mayafin ta lek'a. Zaro ido ta yi gami da bud'e mayafin gaba daya tana salati.
   "Me..." Kowannensu ya mak'ale tambayar da ya yi niyya sakamakon fuskar Ummi da ta bayyana agaresu. Daddy yana mata kallon sani don tabbas yana ganinta jefi-jefi a gidan, saidai baisanta a suna ba ko matsayi. 
  Hajiya ta ji jikinta ya yi mata nauyi ta dubi Faruk, shi dinma ita ya ke kallo, gaba daya alamun tausayi, tsoro da kuma firgici sun bayyana saman fuskarsa. Ta maida kallonta ga Ummi wacce ta ke kuka sosai ga jikinta da ke kad'awa kamar mazari. 
  "Meke faruwa ne?" Fadin Daddy yana dubansu. Hajiya ta kasa kwakkwarar magana, karshe ma ta mik'e ta nufi dakin Daddy. Ikram da ta ke duban Ummi duba na tsana ta nunata da yatsa.
  "Daddy wannan ba kowa bace face 'yar aiki, a gidan Mami ta ke a Kano shi ne ta dan zo nan, ita Yaya Faruk ke son kawomuku matsayin suruka alhalin ita din ba..." Wani kyakkyawan mari ne ta ziyarci kuncinta daga uban gayya, ta rike kuncinta wanda ba karya ta ji marin matuk'a. Ya nunata da yatsansa mai rawa, idanunsa sun kad'a ainun.
  "Koda wasa, koda wasa ki ka k'ara wannan kuskuren sai kin raina kanki! Yaushe raini ya shiga tsakanina da ke?!"
  Dakta cikin 6acin rai ya ke dubansa.
"Ba ka da hankali Faruk! Akwai wani abu a kwakwalwarka, ina kai ina wannan? Akanta har ka d'aga hannu ka mari k'anwarka?!! Haba Faruk!! Wannan zubda k'ima har ina?!!!"

    Faruk ransa ya yi mugun 6aci, ya girgiza kai yana duban Dakta.
  "Na yarda k'ima da komai nawa su zube, sannan don Allah ba kai na kawowa Ummi ba, da ta yi maka da bata yi maka ba, wannan ruwanka." 
Tsananin mamakinsa ne ya kama su, tunda suke da shi basu ta6a ganin kalar tashin hankali har haka akan fuskarsa ba sai a yau d'in, haka koda wasa bai ta6a yiwa wani cikin yayyunsa rashin kunya ba ko dai mayar musu da magana. 
Daddy kallonshi ya ke yi yana nazari, shi yasan waye Faruk, mutum ne mai tsananin hakuri, kusan duk a yaransa daga Usman(Babban Yaya) sai shi a fannin hakuri, yakan hakura da abu duk son da ya ke mishi matukar wani cikin yayyunsa ya nuna baiyi ba saboda tsantsar kauna ta jini d'aya da ke gudana tsakaninsu. 
  Ya maida dubansa ga Ummi yana nazari, can kuma ya dubi Ridwan.
  "Wuce gidanka."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Chapter 51 · 0% Book details