Sashe 88
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ya ji abincin ya fita ransa dole ya ja baya gami da zuba ruwa ya sha.
Ta dubeshi, tana son tambaya ko ya k'oshi saidai ta kasa, ita batasan meyasa duk kunyarsa yanzu ta ke ji ba, ta fahimci kuma ba haka ya ke so ba. Yana kallonta tana faman juya cokali, kawai ta mike ta dauke zuwa kicin. Koda ta fito bata ganshi a falon ba, itama sama ta nufa don jin an soma kiraye-kirayen sallah.
Saida ta idar sannan ta ciro Al-kur'ani ta dan karanta inda aka biyamusu sannan ta rufe. Wayarta ta dauko, tana son kiran Antinta Amina don neman shawara saidai babu kudi cikinsa, tunawa ta yi da kudin da babanta ya bata cikin wanda ta ba shi da ta taho da shi, ya ragomata koda za ta siya wani abun, hamdala ta yi kafin ta mike ta nufi jakarta ta rataye, dubu daya ta ciro sannan ta fita, daman da hijab a jikinta.
Allah Ya taimaketa Hajiya bata falon hakan yasa ta zarcewa kasa.
Kai tsaye farfajiyar gidan ta nufa, saida gabanta ya fadi ganin Faruk ya shigo, da alamu dai daga masallaci ya ke, shi dinma ita ya zubawa ido da mamaki, ta ja ta tsaya har ya karaso.
"Ina za ki?"
Ta nunamishi kudin hannunta.
"Kati nake so shine zan bayar a siyomin."
Jin haka ya tamke fuska.
"Meyasa ba ki sanarmin ba? Hakkina ne fa nasan dukkam abinda ki ke so, ya kamata ki chanja Ummina, banason wannan kunyar taki a yanzu, bani da bukatarta, please ki saki jikinki da ni. I'm now your husband."
Ya karashe da murya mai kamar rada sannan ya gifta ta ya yi gaba, gaba daya jikinta ya yi sanyi dole ta bi bayanshi. Sashensa ya nufa, itama ta yi nata dakin. Kwanciya ta yi saman gado ta yi shiru kawai, haka har aka soma kiraye-kirayen sallar Isha'i, ta gabatar, jimawa kadan ta fito falon bayan ta cire hijabin ta linke.
Hajiya ta tarar zaune tana waya da Hajiya Mama inda suke tattaunawa akan bikin dangatan nata har ta ke sanarmata da batun zuwan su Babban Yaya gobe don tattaunawa. Ummi daman bata zauna falon ba, kai tsaye k'asa ta sauka don kuwa saida ta yi da na sanin fitowa don tuni ta fahimci maganar me sukeyi.
A kasa ta samu su Binta sina kallon wani series da akeyi da harshen larabci, zama ta yi saman kujera kafin ta dubesu sannan ta maida dubanta ga talabijin din kawai kuma sai ta kwashe da dariya sosai, dariya wacce rabonta da irinta tun dawowarta daga Gombe da suna hira da Binta a kicin. Suka dubeta.
"Lafiya Ranki ya dade?" Ta dan harareta da wasa don ita ta nuna sam batason sunan saidai kamar da gayya ma Bintar ke yi. Dariya itama Bintar ta yi.
"Ku ku ka sanyani dariya, kun nutsu kun zubawa talabijin idanu kai kace kunsan abinda su ke cewa."
Suka dara, Samira wacce ta zo bayan tafiyar Ummi Gombe ta dubeta.
"Ai soyayyar kadai idan ki ka kalla wallahi ranki fari zaiyi, kinga nan."
Duk suka maida hankalinsu kan talabijin, abinci zata ba shi da cokali yayinda ya ke jingine da filo a gadon asibiti, ya tarr ya hanata ba shi da cokalin, dole tasa hannu har wani take aka sakomusu, har idan ya 6ata bakin ta gogeshi mishi, karshe ma ya hada da yatsunta ya tsotsa. Ummi ta saci kallon su Binta suka kwashe da dariya, sai kuma suka nutsu. Shiru ta yi har da taguminta tana kallo da murmushi. Basu ji zuwansa ba, hakanan bata ko lura da sadda ya yiwa su Binta alama da su bar wajen ba, balle kuma zamansa gefenta. Hankalinta ya lula wata duniya, tunaninta bai wuce inama itama za ta iya hakan gareshi ba, sumbatar da ta ji a wuyanta ne yasa ta juyawa a firgice tana salati a fili, murmushi ya ke jifanta da shi, idanunsa sun kankance yana dubanta. Gabanta ya hau bugu, ta waiga babu su Binta ko dalilinsu, ta dubi talabijin, tuni ashe an wuce wajen sai ma likita da ta ga ya shigo dakinnasu(a film din), ta dan ja baya gami da shafa goshinta. Duk ta rasa me zata yi don kunya ta hau wasa da zoben gwal din dake hannunta wanda ya bata. Ya matso daf da ita.
"Kina so kina kaiwa kasuwa kenan?"
Ya watsamata tambayar cikin narkakkiyar muryarsa wacce soyayya ta cika. Ta hau girgiza kai batare da ta ce komai ba. Bai saurareta ba ya ja hannunta sadda ya mike tsaye.
"Oya, taso ki ga wani abu."
Ta mike ta zare hannunta da dabara kafin ta bi bayanshi a sanyaye. Ganin hanyar da ya nufa na samansa yasa ta tsaya cak duk a firgice. Ya juyo ya dubeta idanunta ya yi rau-rau, tsoronta lokacin cin abinci ne kada Hajiya ta nemesu, kada ma Hajiyar ta dauka ita ke zuwa wajensa tunda ta ga sadda ta sauko. Hannunta ya kama ya soma taka matattakalar, tana zamewa kadan-kadan saidai bai saketa ba har suka isa. Tsoro ta ji ganin sun wuce falo har ya sada ta da k'uryarsa.
Dakin yana nan yanda ta sanshi, bai jira cewarta ba ya sanyata jikinsa. Tun tana a'a, da kuma rokonsa akan ya kyaleta, kamar baisan ta na yi ba. Ganin yana kokarin zuge mata zif yasa ta yin baya da sauri ta fito falo, tsaki ya ja, abin kuma ya soma ba shi haushi, wannan sam ba zai lamunta ba, tana abu kamar wacce batasan menene aure ba, ya dauki dankwalinta ya biyota da shi, tana tsaye hanyar matattakala, mik'amata ya yi fuskarsa a murtuke. Yana dubanta da jajayen idanunsa wanda har da 6acin rai cikinsu ga kuma fitina. Wannan abun ya zama sakarci kuma, ina laifin ma da ya iya jurewa har aka daura auren? Da ace tasan yanda ya ke mutuwar so da sha'awarta da bata soma tunanin yi mishi gardama a dan abinda zai yi na rage zafi ba, sam ba shi da nufin wani abu bayan kalilan din da ya ke kwadayi a yanzun. Anan zasu samu matsala.
"Kina iya tafiya."
Ta yi narai-narai da fuska.
"Ki tafi nace!"
Ya fada da dan daga murya, ta soma hawaye sai kuma ta juya da sauri-sauri ta bar wajen.
Ta ci saa Hajiya ta yi sashen Daddy, ta wuce dakinta ta kwanta ta soma kuka. Saida ta yi mai isarta sannan ta share fuskarta, wayarta ta ji ta yi karar shigowar text, ta janyota, shi dinne ya turomata kudi daga acc na banki. Ya saba yi mata hakan shiyasa tun bata gane ba ta fahimta, bata yi wata-wata ba ta dannawa Amina kira, saidai bata sameta ba, shaf ta mance cewar sun je Nijar. Ta ciji le66anta, shigowar Hajiya Babba ne ya sa ta gyara fuskarta da sauri, ta amsa sallamarta. Hajiya ta lura akwai wani abun, ta karasa rike da wata roba a hannunta ta zauna gefen gadon.
"Lafiyarki kuwa?"
Ummi ta yi murmushin yak'e.
"Bakomai Hajiya."
"Ya za ki cemin bakomai alhalin ga idanunki a kode?"
"Kaina ke ciwo." Ta samu bakinta da shararo karya. Hajiya ta numfasa.
"Allah Ya sauwake."
"Amin."
"Rike wannan."
Ta mikamata robar, ta dubeta.
"Da safe da dare ki dinga sha da madara kinji? Akwai wasu ma da na sanya akawomin, Ummi ina miki kallon diyata, abinda zan yiwa Ikram zan miki shi, wannan kunyar tawa nakeso ki daina jinta kinji ko? Ki daukeni kamar uwa agareki."
Kanta a kasa ta gyada kai.
"In sha Allahu Hajiya."
Murmushi Hajiya ta yi sannan ta dafe kanta.
"Allah Ya yi miki albarka, ki tashi ki je ki ci abinci."
Da murmushin itama ta amsa da toh.
Ta bi bayan Hajiya da kallo, ji dai yanda mutanen nan suka dauketa da girma, ta tuna yanda ta ke 6atawa dansu a rai akan hakkinsa, dagaske batasan rayuwar aure sosai ba, duk wani kissa ko kisisina bata ta6a hirarsa da wani ko wata ba, to waye mai koyamata ma? Duka-duka idan a makaranta ake koya, yaushe ta soma zuwa makarantar? Ko wata biyar cikakkiya bata yi ba a makarantar Kano, sannan ita din ba karatun litattafai ba, hakan kuma bai hadasu da Amina, ta dai soma jin kadan daga bakin su Abida, kamar biyayya da bin umarni da sauransu. Dole ta zage damtse ta koya, kamar dai yanzu da ta ga kulawar matar nan ga mijinta duk da cewar a fim ne, amma kwarai sun burgeta.
'Mijinki dan boko ne wayayye, sai kin zage damtse kin kula da shi.' Cewar wani sashe na zuciyarta.
A ranar basu kara haduwa ba, ta kira wayarsa yafi sau biyu bai daga ba, hakanan ta hakura, ranar bata iya baccin kirki ba.
Washegari....
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
106