Sashe 81
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washegari misalin takwas bayan sun gama karyawa suka yi shirin tafiya, kamar kullum, yau ma Malam Balarabe ya shigo har dakin Dada don gaisheta, saidai ko kallo bai isheta ba, Ummi tana duban mahaifinta cike da tausayi har ya gaji ya kara da fadin.
"Za mu wuce." Uffan ba ta ce ba sai ma mikewa da ta yi ta fita, ya dan bita da kallo jiki a sanyaye kafin ya dubi Ummi.
"Idan kun gama sai ku fito, bari na je nan makwafta wata gaisuwa na dawo."
Ta amsa da to, bayan fitarsa ta ja bakin mayafinta mai adon jajayen fulawa ta rufa akan riga da siket din dake jikinta na wani fari da jan yadi, ta ci kwalliya don ta fi so suna ganinta cikin lumana koda suna fushi da mahaifinta su huce. Idan ka ga Ummi ba zaka ce itace ba, ta yi kyau kwarai hakanan ta ciko a kwana ukun da sukayi kacal, babu damuwa babu mai tsangwamarta ko kuma jifanta da kallon banza balle uwa uba gorin gida. Shigowar Dada ne ya katse tunaninta, ta rataye bakar jakarta.
"Kaga 'yata ta fito."
Ta dan tamke fuska don har zuciyarta bata jin dadin abinda Dada ke yiwa mahaifinta. Ganin haka yasa Dada ta rude.
"Ke meyafaru? Ko wani abin ya ce miki?"
Ummi ta dan karyar da wuya sa'ilin da ta ke zura takalmi kamar bata so ta ce.
"Don Allah Dada ki daina yiwa Babana haka ba dadi, don girman Allah ki yafemishi. Ya yi muku laifi saidai shima ba laifinsa ba ne, da kanta Saude ta tona dukkan mugun ayyukan da ta yi ciki har da.."
Zata fadi na kashe Ummanta da ta yi sai kuma ta yi shiru don batasan zafin da zata kara dauka ba.
"Bari ki ji kadan daga abinda ya faru."
Ta soma koro mata bayani a gajarce, da kadan cikin zaman da suka yi da Saude bayan mutuwar Hasiya da aikatau da ta yi da irin karamcin mutanen da suka dauketa aikin har zuwa komawarta Ringim da yanda abubuwa suka kasance har da haukacewar Saude da kai Habiba gidan yari. Ta dubeta.
"Naso 6oyemiki cewa kashe Ummana sukayi saidai naga kamar ba amfani. Komai da ya faru babu laifin Baba, idan hakane nima zan iya yin fushi ai tunda babu wani cikin yan uwan Ummana da ya nemeni, amma na yi hakuri da na fahimci ba ku da laifi kusan laifin na Saude ne tunda Baba ba cikin hayyacinsa ya ke ba. Ko don wannan don Allah ki yafemasa."
Dada ta dan daure fuska.
"Jeki suna jiranki, Allah Ya saukeku lafiya, ki gaidamin Inna Boddo."
Ummi ta dan yi murmushi a sanyaye kafin ta amsa da toh sannan ta juya ta fita. Dada ta bita da kallo, kafin bayan fitarta ta zauna da6as a saman gado. Kawai sai ta soma shar6ar kuka tana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Ashe haka lamuran suka afku? Ko jiya Malam ya yi niyyar fadamata saidai bata ba shi dama ba asalima tashi ta yi ta bar wajen. Ta tausayawa dannata ainun amman daman wanda bai ji bari ba zai ji hoho, illar rashin jin maganar iyaye kenan, sai gashinan ya janyowa kansa bala'i.
"Allah Ya jikanki Boddona, Allah Ya yi miki rahma." Ta fada a hankali.
Acan kuwa su Ummi suka gama sallama da kowa suka kama hanyar Jar Kwami har Haruna wanda shi ya yi musu rakiya.
Bayan sun isa kai tsaye gidan Lamido Shu'aibu yaya awajen Manu kakan Ummi.
Ummi ta dubi gidan, gidan gargajiya, saidai babba ne, suka shiga ciki. Anan kofar gidan k'asan 'yar rumfa, Lamido Shu'aibu ne kishingide saman wata darduma akan tabarma, ga wasu dattijai su biyar zaune gefensa ana hira, saidai ganinsu ne yasa su maida hankali garesu. Ummi ta lura da mutum uku masu kamanni farare ne saidai tsufa ya dakusar da haskensu. Malam Balarabe da Haruna ne suka karasa suka durkusa wajensu, yayinda Ummi da Mariya suka durkusawa a gefe suma. Bayan an gaisa, Lamido Shuaibu cikin harshen fulatanci ya ke tambayar ko su waye.
Shima ya ba shi amsa da fillancin ai tuni waje ya karade da murna, Malam Balarabe ya karasa suna dafashi baki a washe, wani har da goge kwallar farin ciki. Tsoho Mai ran karfe Usmanu Lamido ya dubi Malam Balarabe da harshen fulatanci ya ce.
"Ashe da rabon na kara sanyaka a ido kafin na mutu Abdullahi?"
Kunya ta bi ta cika Malam Balarabe ya hau bada hakuri yana nuna ba laifinsa bane. Ya waiwaya ga su Ummi.
"Ku karaso nan." Suka taho, Ummi ta durkusa ta gaishesu, suka zubamata idanu.
"Wannan itace diyar wajen Hasiya, itama Hasiyar sunanta, Ummi."
Suka yi kabbara.
"Ai ko baka fada ba na ga kamanni, matso gareni Boddo." Cewar Dattijo Usmanu. Ummi ta matsa gareshi tana jin hawayen farin ciki na kokarin zubomata. Ya rungumeta ya fashe da kuka, itama kasa jurewa ta yi ta sanya kukan, bawan Allah jikinsa har rawa ya ke yi. Saida aka basu baki sannan ya yi shiru. Ya dagota yana shafa fuskarta kamar Boddonsa.
Ta karasa ga Lamido Shuaibu shima ya dafa kanta yana murmushi mai bayyana hakora, duk girma ya kamashi dakyar ya ke gane mutane.
"Allah Ya yi miki albarka. Ya ji kan Mammarki."
Ta amsa da amin. Bayan duk an gama gaisawa sukayi cikin gidan inda tuni labari ya je musu ga diyar Hasina ta zo daga burrni. (Lol).
Nan aka zubawa Ummi ido ana kallonta baki sake, wasu dakyar suke samun karfin gwuiwar gaishe da su sakamakon ganin tsantsar kamanninta da mutan gidan. Kai tsaye Haruna ya nufi da su 6angaren Inna Boddo wacce tuni labari ya iso gareta saidai babu mai kaita ta ganota. Inna Boddo wacce ko tashi bata iya yi saida wanda sakamakon ciwon kafa da ta ke fama da shi, tana zaune a tsakar gida cikin rumfa saman gadonta na karfe don koyaushe nan ne wajen zamanta saidai yaran gidan su zo nan tayata hira.
Shigowarsu ce ta katse tunaninta, ta zubamusu ido, tana hada ido da Ummi ta zaro ido.
"Boddona!" Sai kuma ta soma kuka tana mikamata hannu, a guje Ummi ta karasa ga kakarta don ta gane wacece daga sunan da ta ambata, suka rungume juna. Fuskar kowannensu cike da farinciki.
Bayan an gaggaisa, ta ke tambayar Malam Balarabe sadda ya dawo, a kunyace ya bata amsa ya kara da neman gafara. Ta yi kamar bata ji ba don kuwa kokusa bata da rikeshi ba. Mariya dai an zama yan kallo sai rarraba idanu kamar shege a rabon gado.
Ranar Ummi dai ra rasa inda zata sanya kanta don dadi, haka ta wuni cikin yan uwa, dangi sai zuwa akeyi rututu ganinta. Wasu sunfi danganta kamanni da yanayinta da Inno Zahra data rasu saidai ita tana da yawan barkwanci da dariya, wasu kuwa sun fi karkata ga Hasiya.
Ranar fura da nono har saida ta ture, ga cima kala-kala da aka kawo musu. Mariya tana samun yaran abokan wasa shikenan kuma ta saki jiki har ta fice tare da su.
Ranar Ummi ta mance dukkan wasu bakkan cikinta. Kwanan Malam Balarabe biyu suka juya tare da Dan uwansa da kuma Mariya wacce itama ya ke son kaita ganin dangin mahaifinta wadanda bata sani ba, ba kuma yaso nan gaba azo baya raye ta tambaya ba wanda ya sani.
Ummi ta zama 'yar lele, kullum cikin hira, idan ta jima wajen Inna Boddo, nan kakanta zai nemeta, nan ma ba jimawa sauran matan musamman uwa ga Inno da Binta, Danejo itama zata shiga nemanta, don tunda ta ga Ummi ta ji kamar Innonta ce ta dawo. Rayuwa kenan, bayan wuya sai dadi idan har mutum zai jure ya yi hakuri da dukkan lamura, Allahu Ya bamu ikon juriya da hakuri ba don isarmu ba, Amin.
Ranar talata da misalin biyar na yamma, Ummi da wata yar uwarta Abu wacce itama jika ce a gidan suna tafe a hanyarsu ta zuwa gona kaiwa baban Abun abinci. Ummi na sanye da doguwar riga bulu mai adon fulawoyi bakake, ta tufke gashinta wanda tun tsifar da Dada ta yi mata bata yi kitso ba, fuskarta fayau, ta yafa mayafi akanta bata ko daura dankwali aciki ba, sai gashin ya yi tudu a tsakiya kadan, tana wasa da karar dake a hannunta. Suka tsinci muryar yayan Abu, Gidado yana kwalamusu kira ta bayansu. Tsayawa sukayi gami da juyawa, gaban Ummi ya yi wani mugun faduwa ganin wanda ke tare da Gidado. Murmushi tattausa ya ke jifanta da shi da kallon dama na fadamiki...
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
99