Sashe 91
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
109
Zirga-zirga ta ke yi a dakinta ko kayan makarantar ta kasa fiddawa, can dai ta k'arasa fisge dankwalinta ta ajiye gefe, har da ribbon din da ta ke tufke yalwataccen gashinta na fulanin usul, ta zaune gefen gado.
'Kai anya kina da hankali Ikram? Me za ki yi da DAN KAUYE?'
Shine tambayar da wani sashe na zuciyarta ta jefomata.
Ta runtse ido sannan ta ja tsaki gami da mikewa tsaye.
"Craziness!" Ta fada a fili sannan ta rage kayan jikinta ta fada wanka.
Bayan fitowarta ne daga ita sai tawul ta tarar da kira har sau uku a wayarta, ta yi saurin dubawa, biyu daga wani saurayinta ne Khalid wanda kawai ta ji ba ta yi murna da kirannasa ba, ba kamar a baya da ya ke dan burgeta ba, ta shareshi ta bi bayan kiran 'yar uwarta Ihsan wacce itace ta kira sau daya.
"Ke ina ki ka shige ne ina nemanki?"
Cewar Ihsan. Ta dan dara,
"Yi hakuri baiwar Allah, wanka na shiga fa. Ya akayi, ya su Mami?"
"Mami ta fita siyayyar tsaraba na mutan Adamawa, ke ni bugowa na yi na ji ko da waccan munafukar za'a je?"
Murmushi Ikram ta yi.
"Babu inda za ta je, gobe ma zata koma kauyensu. Ina Man dinki?"
Ta ja guntun tsaki.
"Yana can inda ya ke, na ji yana batun shima ba a soma bikin Yayannaki yana nan ba don zasu je dangin Abbansa."
Dariya Ikram ta yi karo na biyu.
"Me ye na tsakin wai? Kefa ki ka cemin kin soma sonshi."
"Bazaki gane ba, ya iya tsara kalamai wallahi, matsalar daya yana son sanyomin batun zai min kaza da kaza bayan aure. Haka fa zuwan da ya yi satin da ya wuce, wallahi har rungumeni yaso yi na kauce. Amma hakan bai hana ni sonsa ba, saidai banason hakan ne kawai."
Baki Ikram ta ta6e,
"Sai hakuri da neman tsari daga sharrin shaidan, mai yiwuwa saboda shi kadai ya tashi gaban iyayensa shiyasa, kinga kuma yanda suke ji da shi."
Tsakin dai Ihsan ta k'ara yi.
"Za ki yi ankon Yaya Faruk? An fiddo." Cewar Ikram.
"Allah Ya sauwake!" Cewar Ihsan cikin daga murya.
Ikram ta ja tsaki sadda ta isa ga sif din kayanta da zummar fiddo na sanyawa.
"Kefa wani zubin banza ce, rashin yinki bakisan kamar kin nunawa mutane har yanzu kina sonshi ne ba, ai wallahi gwara ki yi ki cekare abinki, ga Abubakar dinki a gefenki. Ke kanki kinsan hakan ma abin alfaharinki ne tunda gayen karshe ne shima a haduwa."
Ihsan ta yi shiru sai kuma ta amsa.
"Barni tukun, sai na yi tunani. Bari na barki kada na cinye miki dan katin."
Daga haka suka ajiye wayar.
Ummi kuwa tun a daren ta karasa shirin kayanta, sun yi waya da mutan Gombe ya fi sau uku a ranar duk su dinma d'okin zuwanta suke yi. Yau ko ta kan abincin dare bata bi ba don ta dage wajen shirye-shiryenta, daga ta rufa akwati sai ta tuna da wani abin ta bude ta sanya, kamar yanzu da ta ke kokarin sanya wasu kayanta da zata bayar, tana cikin jerasu ciki ne, Faruk ya yi sallama ya shigo. Ta amsa tana mai duban kofar, fuskarsa cike da damuwa, kananun kayan da suka zame mishi jiki yau dinma su ya sanya. Cikin dauriya ta sakar mishi murmushi don kuwa ta fahimci sam tafiyar ce baya so saidai don babu yanda ya iya ne. Kafin ta yi wani yunkuri ya karaso ya kwantar da kai a kafadarta gami da rikota jikinsa ta gefe, ta lumshe ido batare da ta yi yunkurin hanashi ba don tuni ta daina wannan sai idan ta ga abin zai fi karfinta tukunna.
"Tafiya za ki yi ki bari mijinki?"
Ta sunkuyar da kanta tana duban hannuwansa dake cike da gargasa. Har lokacin murmushi ta ke.
"Kaima ai tafiyar za ka yi."
Ya dago gami da sanya bakinsa saitin kunnenta.
"Ba zan samu rakiyarki ba kuma ko?"
Ya fada a shagwa6ance, numfashinta sai safa da marwa ya ke yi, ta kasa cewa uffan kasancewar ya cigaba da sarrafata son ransa, haka har tsayuwa ta nemi gagararsu.
Can kuma ya dago kai yana dubanta da idanunsa da suka yi k'ank'an.
"Na yi? Kin amince?"
Ta zaro ido tana dubansa. Abin ya ba shi dariya, ya ja kumatunta.
"Matsoraciya, kodayake na ga kin rage tsoron, oya tell me, ya akayi ya ragu?"
Ya karashe yana mai zama gefen gado ita kuwa na saman kafafunsa. Shiru ta yi kawai tana murmushi, ya ja karan hancinta har saida ta yi 'yar k'ara.
"Wani 6angaren kunyarki na burgeni, yana k'aramin sonki sosai, ina son mace mai kunya, shine babban ado ga diya mace, yanmatan yanzu basusan wannan ba, za ki yi mamaki idan ki ka ga yanda mata ke tallata kansu ga maza, za ki yi mamaki idan ki ka hau yanar gizo yanda mata ke aika hotunansu babu ko rufin kallabi da sunan neman mijin aure alhalin basusan cewar sam mazan da suka san abinda sukeyi bazasu kallesu da daraja ba, ke har fa wajen biki kawo tallar kawunansu suke yi ga maza har kuwa inda suke, za kuma ki yi mamakin ganin mahaukatan da ke tallatawa mijinki surarsu."
Ta hade fuska kadan. Ya kara matsarta a jikinsa yana dan murmushi.
"Saidai sun yi kadan, tsarin Allah muke nema koyaushe daga sharrinsu, in sha Allah zai karemu. Kinsan a inda na tsani kunyarki?"
Shiru ta yi ganin ya maimaita yasa ta girgiza kai. Saitin kunnenta ya yi mata rad'a.
Ai batasan sadda ta runtse ido gami da kokarin zamewa ba, saidai ba rikom ragon namiji ta samu ba. Dariya kawai ya yi mata.
Ya fi awa daya a dakin, daga an soma hirar arziki zai hau lalubenta, sannan a cigaba har dai a karshe ya fita sakamakon Daddy da ya yi kiransa ta waya yana nemansa, wannan ya sanyashi tafiyar dole.
Kwance ta ke tana faman juyi, can kuma idan ta gaji ta ja tsaki, wai meyasa haka ne? Ina ita kamarta ina kuma wani dan kauye? Meyasa ta kasa daina ganin hotonsa a kwayar idanunta, ta mike zaune gami da jingina da katakon gadon, batasan sadda hawaye ya zubomata ba, ba don komai ba sai don takaicin wannan lamari, abin kunya ne babba agareta, ta ja wawan tsaki cike da jin haushin kanta, wannan kuwa abu ne da bazata ta6a bari ya yiwu ba, wai ta ce KO A MAFARKI....! Ta yi adduoi ta shafa sannan ta kwanta, har dai bacci ya yi awon gaba da ita.
Washegari tun Asuba da Ummi ta farka bata koma ba, karfe bakwai zasu wuce, kai tsaye wanka ta fad'a ta sanya leshinta ruwan hoda marar nauyi.
Karfe bakwai kuwa aka fidda akwatinta, bayan sun kammala karyawa, Faruk har dakinta ya zo kafin ya wuce ofis suka yi sallama, haka ta wuce cikin kewarsu da kuma d'okin zuwa ga mahaifinta da kakanninta...!!!
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
110