← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 116

Sashe 94

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

    Bayan gama gaggaisawa mazan suka fita, itama Gwaggo daki ta koma.  Ummi ta ja Amina suka koma sashen Anti Halima.
  "Kinga ikon Allah ko Anti?"
"Allah kenan, ashe duk firiritar Ihsan kuma danginku za ta shigo? Wannan lamari saidai Allah, ya dangantakar ta ke?"
  "Gwaggo Binta kakarsa uwa ce ga Ummana. Nima tana matsayin kakata."
  Amina ta hau gyada kai sai kuma ta soma dariya Ummi na tayata tana tambayar ko lafiya.
Girgiza kai ta yi.
"Wallahi Ihsan gwanar wulakanci ce ta ban tausayi kawai, yanzun ko da wane idon zata kalleki? Shiyasa a duniya ba'ason ka dunga wulakanta DAN ADAM don bakasan mai yi maka rana ba gobe."
   Murmushi Ummi ta yi kawai tana kokarin goge wayarta wacce ta koma yaluwa saboda kurkum.
    Sai dare Abubakar ya samu damar ke6ewa da Ummi sadda ita da Amina suka je kai mishi damammiyar fura inda ya je zaune tare da Gidado (wanda shima bai jima da zuwa ba daga Jar Kwami) suna hira. Kusan ma a kyau har Gidado ya tsere Abubakar saidai shi zai nunamishi wayewa da hutu sosai da kuma zurfi a ilimin boko don kuwa shi Gidado iyakarsa sakandire ya watsar ya fada kasuwanci, Kano ya ke zuwa saro kayan sawa na mata ya ke siyarwa, sosai yana samu don asirinsa a rufe. Matarsa daya Aisha wacce sukayi auren soyayya sai dansu da baifi shekara daya ba don duka-duka aurensa ko shekara biyu baiyi ba saidai idan Gidado ya sanya sutura sai ka rantse ba mazaunin Jar Kwami bane musamman idan Abubakar ya mishi aiken suturu daga Adamawa. 
    Da sallama suka shiga suka ajiye furar kafin su gaishesu, suka amsa. Ummi ta dubi Gidado da murmushi saman fuskarta.
   "Yaushe ka zo?"
Shima murmushin ya mayarmata.
"Ko awa biyu cikakku banyi ba."
Ta gyada kai sannan ta mike zata bi bayan Amina wacce daman suna ajiyewa ta fito, Abubakar ya dakatar da ita.
"Ummi."
"Naam." Ta amsa tana dubansa gabanta na dukan tara-tara.
"Please ke ce dai wacce na sani a Kano gidansu Ihsan?"
  Ta gyada kai a sanyaye. 
"To meya kaiki can?"
Gidado ya cafe.
"Au ka ta6a ganinta acan kenan? Ai ta zauna can."
Jin haka Ummi ta mike da sauri, tana jin Gidado ya soma labartamishi yanda lamura suka kasance ita kuwa tuni ta soma zura takalminta, suka kama hanya da Amina tana sanarmata yanda akayi, Amina murmushi ta yi.
"Allah Sarki." Shine abinda ta ce kawai. 
                  ***   ***   ***
                     ABUJA
 Tun bayan sati da kwanaki da tafiyar Ummi, Ikram bata cikin nutsuwarta, gaba daya ta rame ta koma wata shiru-shiru, koyaushe bata da aiki sai na kuka ga wani ciwon so da ya addabi zuciyarta har tana ji idan bata samu cikar burinta ba zata iya rasa rayuwarta. Har mutanen Kano suka iso Abuja bata da walwala sosai, kowa sai ya tanbayeta damuwarta amman ta nuna ba komai kawai bata jin dadi ne, Ridwan har dubata ya yi ya kuma gano damuwa ce kawai ta sanyawa kanta, tanbayar duniya ya yi mata amman babu amsa. Daidai da dinkin ankon da sukayi kala biyu ya yi mata yawa sakamakon ramar da ta yi. 
  Yau ma babu kowa a gidan, Hajiya sun fita tare da su Mami ganin gida, ita kuwa Ihsan da su Maryam sun tafi gidan Baraka can zasu wuni har da wasu cikin bak'in Adamawa, manyan kuwa suna can kwatas suna hira da Hajjah wacce ta zo ko don jikanta. Tana kwance daga ita sai shimi da dogon wando wanda da kadan ya wuce gwuiwa, wuf ta mike tsaye, kai tsaye kofa ta nufa, babu kowa a falon, hakan ya bata damar zarar mukullin kofarta wanda ana iya amfani da shi wajen bude kofar dakin Baraka inda ya zama na Ummi a yanzun. Ta bude dakin ta shiga gami da sakayawa yanda ba za'a gane ba, dakin a gyare tsaf don duk bayan kwana uku sai Binta ta gyarashi, ta hau rarraba idanu har Allah Ya taimaketa ta hango jakar Islamiyyar Ummi rataye a jikin wani dogon karfe na rataye kaya. Da sauri-sauri ta isa wajen ta janyo jakar ta soma bincikawa, ba ta ci wuyar ganin hoton da ta ke nema ba, ta kurawa hoton Gidado ido hawaye suka zubo a kuncinta, shine saurayin da a iyakar tsawon rayuwarta bata ta6a ganinsa ba sai a hoto, ba kuma ta ta6a son wani ba kamar yanda ta ke sonshi, da sauri ta dubi kofa sannan ta shiga maida litattafan Ummin cikin jaka gudun kada wani ya zo ya isketa, ta sanya hoton cikin rigarta ta fito ta maida kofar ta rufe. 
  Shigarta dakinta nan ma hoton ta yi ta kallo tana murmushi, bata ta6a zaton zata so wani namiji haka ba, kuma wai dan kauye. 
"Ba kauye ba, ko cikin daji ka ke rayuwa zan iya binka Hubbyna, bansan sunanka ba na kamu da sonka, ban ta6a ganinka ba ido da ido, amman na ganka a mafarki fin sau uku har dariya ka yimin. I so much love you."
Ta rungume hoton, ranar kam kowa ya ga chanji a tattare da ita don ta yi wuni na dadin rai, babban burinta yanzu bai wuce na son ganin zuwan su Ummi Abuja ba ko Allah zai taimaketa da ganin sanyin idaniyarta. 
  Mami na dakin Hajiya zaune suna hira da yan uwanta, wayarta ta yi k'ara, kai tsaye ta daga da sauri ganin Hajiya Binta abokiyar zamanta. Suka gaisa a mutunce suka sha hira tana tambayar mutanen Abuja sannan sukayi sallama, sai kuma ga kiran mijinta. Labarin da ya zo mata da shi yasa jikinta wani mugun sanyi, banda ikon Allah kenan babu abinda ta ke ambata a fili hakan yasa su Hajiya Mama da Hajiya Babba harma da Hajiya Karima (cousin) dinsu ta Adamawa suka zubomata idanu. Bayan ajiye wayar ta dubesu.
"Kun ji ikon Allah ko?"
"Meyafaru?" Cewarsu har suna hada baki.
Mami ta numfasa.
"Ashe Alhaji Kabiru Jimeta uba ne wajen Ummi? Dan uwan mahaifiyar Ummin ce."
  Mamaki ya cika kowannensu banda Hajiya Karima da batasan kan zancen ba saidai tasan Alhaji Kabirun. 
   "Lallai fa ikon Allah!" Cewar Hajiya Mama.
  "Yanzu suka yi waya da Alhaji Kabirun ya ke sanarmishi, don su suna ma Gomben."
  Murmushi Hajiya Babba da Hajiya Mama sukayi wannan karon, banda hamdala babu abinda kowannensu ke yi a zuci musamman Hajiya Mama da ke jin kamar ta yi ta kyakyata dariya ga yar uwarta. Ai kuwa ta kasa hadiyewa ta hau yinsa, Mami duk kunya ta isheta ta yi shiru kawai tana Umm.
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

113

"Allah Sarki rayuwa." Shine kawai furucin da Hajiya Mama ta yi bayan kammala dariyarta. 
  "Wai duk meyafaru ne?"
Cewar Hajiya Karima.
Hajiya Mama ta dubeta.
"Ba zaki gane ba Karima, bari har mu je Gombe gobe za ki gane komai."
"Toh ganar dani mana."
  Mami ta ta6e baki gami da mikewa.
"Ina zuwa." Ficewa ta yi tsabar ta rasa abin cewa, suka bita da kallo kawai. Hajiya Babba ta ce.
"Ki share batun Sadiya, kinsan ita fa abin dariya ba ya mata kadan."
  Hajiya Mama ta k'arawa darawa kawai. 
   Hajiya Babba ta share maganar gami da sanyo maganar yanda zasu yi tsare-tsarensu. 
                   ***    ***    ***
                       GOMBE
Chapter 94 · 0% Book details