Sashe 95
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Misalin bakwai na safe matan gidan suka tashi da aiki tuk'uru sakamakon bak'in da zasu yi daga Abuja masu kawo lefe da sauran kaya na al'ada.
Wajen karfe goma sha daya ita kuwa Ummi tana dakin Abida tana gwada kayanta kaloli biyar da Mahaifinta ya dinkamata na fitar biki anan, kaya masu tsada wanda acewarsa tunda bai yi na daki ba to wannan bazai gagareshi ba. Dinki na zamani akayi mata wanda ya zauna d'abas a jikinya, daidai da Amina saida ya siyamata ankon da yan uwan Ummi mata na Gombe suka yi, abinka da aikin kudi telar washegari sukayi zata je kar6a don a ranar sauran kwana daya bikin.
ABUJA
Su kuwa mutanen Abuja mutane shida kawai suka tafi kai lefe, Hajiya Mama da Hajiya Karima suna ciki, sai kuwa Hajiya Hadiza da Hajiya Bahijja, kanne ga Gen. Ahmad Danzaki sai kuwa wata Yayarsu da cikon mutum daya daga Adamawa. Sauran jama'a kuwa da zasu halarci yini da budar kai sai washegari zasu iso cikinsu kuwa harda su Mami da su Jidda.
Ikram ji ta yi kamar ta zuab ruwa a k'asa ta sha jin cewar zaaje Gombe daga can a taho da Amarya ayi na nan. Murnarta har mamaki ya bawa su Jidda balle kuma Ihsan wacce bata ta6a zaton hakan ba. Koda ta ga yanda Ikram ke rawar jikin hada kaya tun ma lokacin tafiyar baiyi ba ta gyada kai.
"DAN ADAM kenan, yanzu ke ba abun ki tayani bakin ciki bane Ikram, ba abun ki tayani zubar da hawaye bane, ko labarin matsayin Ummi ga Abubakar mai iso ga kunnuwanki ba?"
Ikram ta dubeta jiki a sanyaye.
"To ya zamu yi Ihsan banda mu yi hakuri, komai fa na Allah ne, ba yanda zamu yi tunda haka Ya tsaro za ki auri dan uwan Ummi, ni ai ba zuwan farinciki zanyi ba, ba kyaso ki ga yanda zasuyi shagalinsu ba?"
Ihsan ta ja tsaki yayinda idanunta suka cika da ruwan hawaye, shikenan fa k'aryarta ta k'are, wani aji da jijji da kai yanzu saidai ta yiwa wata ba Ummi ba tunda dan uwanta zata aura, ita kam tasan ko giyar wake ta sha, ba zata tunkari Abbanta ta ce ta fasa auren Abubakar ba, sannan bayan wannan ma ga sonsa da ta ke ji a ranta. Sam, ba zata iya hakura da shi ba a yanzun, da ya ya ma ta soma sonsa da har za ta soma tunanin guje mishi? Ita kuwa babu Gomben da kafafunta zasu taka.
'Ko ba ki je yanzu ba dole ki je a gaba tunda za ki auri dan Gomben.' Cewar wani sashe na zuciyarta.
*** *** ***
Bayan Azhar su Hajiya Mama suka isa, alokacin Ummi suna dakin Abida suna faman kwasar hira, Mariya wacce itama Malam Balarabe bai jima da daukota daga gidan kakanninta ba saboda bikin ta shigo a guje da yaran gidan.
"Adda Ummi, Adda Ummi!" Haka ta ke fad'a kamar yanda ta ji sauran yaran gidan na fadawa Ummin. Ta zube gabanta tana numfarfashi, yarinyar gaba daya ta chanja ta yi ki6a kamanninta da Saude na nan kamar an tsaga kara an karyashi.
"Meyafaru?"
Cewar Ummi wacce duk kiran ya rudar da ita.
"An kawo lefenki."
Ta ja guntun tsaki tana tureta, su kuwa su Amina suka dara, nan suka ja mayafi suka nufi hanyar fita Amina na fadin.
"Ah, bari muje na gaisa da mutan Abuja."
Gaba daya kowa ya tafi aka bar Ummi nan zaune ta yi shiru don gani ta ke kamar mafarki ta ke yi, wai lefenta? Ta yi tsuru tana rarraba ido.
Hajiya Mama ta kama baki ganin Amina lokacin da ta ke gaisheta.
"Ke kam ai kin zama 'yar gida shiyasa tunda ki ka kira ki ka ce kunzo lafiya ban k'ara ganin kiranki ba."
Akayi dariya, Amina ta hau sunkuyar da kai itama tana darawar.
Masaukin da aka tanadarmusu(wato gidan da ke makwaftaka da wannan, wanda ya kasance na Aminin Malam, Manu kakan Ummi saidai ba wanda ke ciki sai kuwa bak'i da ake saukewa) nan aka kai kayansu, saida suka yi sallah sannan aka hau gaggaisawa daga nan suka ci abinci, nan kuma aka hau buda lefe, ita dai Ummi banda sautin bud'a babu abinda ta ke ji, kaya ne masu tsada aka sanyamata, akwatinta saiti cif, harma da wani daban na kayan lalle da na budar kai da sauransu, cikin suturu kuwa har da dinkakku.
Ummi na faman zirga-zirga ta yi can ta koma nan ba zato ta ji Amina ta d'ane bayanta tana tsalle da dariya. A farko ta tsorata don har gabanta ya fadi saidai jin muryar yasa ta numfasawa.
"Kai don Allah Anti."
Kafin ta kai ga juyowa ta ji Amina na kuka har da sheshsheka, da sauri ta juyo daman itama karfin hali ta ke yi kawai, nan suka hau kuka babu mai rarrashin wani. Kusan duk abu guda suke tunawa. Amina ta dubeta.
"Ki godewa Allah Ummi, ki godemiShi, Ya so ki da rahmarSa, Ya baki matsayin da kudi ko karfinki bazai ba ki ba har abada. Na ta6a ce miki Yaya Faruk ya fi karfinki, matsayinki da na shi ya sha bamban, a wancan lokacin ina jiyemiki tsoron shiga wahalar rayuwa ne, shiga cikin wadanda suka fiki da komai. Ga shi da Allah Ya yi ke din matarsa ce, sai Ya maida komai ba komai ba, ma'ana tulin matsalolin da muke hange ba wasu matsaloli ba, shakka babu ayau na k'ara godewa Allah da naga lefenki, na kalli dama da haguna naga dangin Ummina cike a daki, Ummina 'yar dangi ce! Allah Ya baku zaman lafiya da Yaya Faruk, Ya baku ikon rike juna bisa amana har abada."
Ummi ta kasa komai sai murmushi ga hawaye na zuba, Amina ta ja ta suka zauna ta hau share mata hawayen, kafin waninsu ya ce komai, wayar Ummi ta hau ringing, suka kai dubansu ga wayar sannan Amina ta dara.
"Bari na koma wajensu Hajiya Mama, ki gyara fuskarki fa don nasan zasu buk'aci ganinki."
Daga haka ta fice, haka ya bata damar janyo wayar, gogannata ne kuwa. Dakyar ta iya dagawa, tana dagawa kuwa ta ji ya sakarmata gud'a a kunne, batasan sadda ta tuntsire da dariya ba sosai, shima yana tayata, saida suka yi mai isarsu sannan suka tsagaita.
"Kai don Allah."
Ta fada a shagwa6ance, yanzu kam ta saba da Faruk ta saki jiki da shi.
"Kai don Allah me? Ko ba Amaryar Faruk din bace?"
Murmushi kawai ta yi.
"Ina zuwa, kiran Daddy na shigowa, zan k'ara nemanki."
"Toh." Ta fada sannan sukayi sallama, kafin ya k'ara kira su Abu da sauransu suka shigo tafiya da ita gaisawa da surukai.
Haka suka sanya ta lullu6e fuskarta da mayafi sannan suka fita. Ba yanda ta iya dole saida sukaa budemata fuskarta, kowannensu ya yaba, to idan ma basu yaba din ba ya zasuyi tunda an riga da an daura? Hajiya Mama ita mamakin kyawun da Ummi ta k'ara kawai ta ke yi, ashe rashin samun hutu da gyara ne ya sanya ta koma gatanan? Bayan fitar su Ummi, matasan gidan suma suka shigo aka gaggaisa, Hajiya Mama bata yi mamakin ganin Abubakar ba tunda labari ya iso gareta, acewarta ma sai ko baa fada ba za'a ga kamannin Alhaji Kabiru da wasu cikin yan uwan Ummin.
Anan ne kuma sauran abokaan tafiyarta suka ga mijin da Ihsan zata aura, sun yaba kwarai.
Dangin Ummi suka hada su da(snacks) da kwalayen lemuka da suka yi musu aka kai masaukinsu aka ajiye. Washegari wajen daya da mintuna su Ikram su Mami aka iso, Mami ta dake matuk'a don yanzu jikinta ba karamin la'asar ya yi ba musamman ma ganin kawarta mahaifiya ga Abubakar, Hajiya Salma.
A ranar ne kuma ake lalle.Tun zuwansu basu sanya Amaryar a idanu ba sai da aka soma biki.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
114
Ummi ta shirya cikin wata koriyar atamfa mai adon kaloli jiki, ta yi kyau matuk'a a wannan rana, filin taro sosai Abubakar ya kama, shi ya biya komai, abinka da aikin kudi, nan aka gyare wajen aka yi kwalliyar kumbo a gefe da gefe inda amarya zata zauna sai kuwa tuntun da aka aka sanya, da katon darduma inda akai kawayen amarya zasu zauna sai kujeru.
Sai awajen taron Mami suka hadu da Amarya Ummi, Ikram tun zuwanta ta ke rarraba idanu na son ganin inda zata ga rabin rannata saidai bata ganshi ba.
Wajen ya burgesu ainun, da ka gansu kaga zuri'ar Modibbo da ta Danzaki, sunyi kyau har sun gaji, suma dangin Ummi, sun cekare abinsu. Kowannensu da baiwar kyan da Allah Ya yi mishi bakake da fararensu.
Amarya ta sha lik'i a wajen dangin mijinta hakanan suma danginta ba'a barsu a baya ba. Mami koda ta je lik'amata har saida ta rungumeta, wannan abu da ta yi yasa Hajiya Mama jin dadi matuka har batasan sadda ta hau lik'a musu kudi ba. Ummi har hawaye ta yi don dadi, shakka babu wannan ya nuna Mami ta sauko. Jidda kam su dai yan bin yarima asha kida ne, to me zasu ce tunda wacce suke ganin kusan ba'a kyauta mata ba itama ta sauko? Ina ga su 'yan karan kada miya?
Sai wajen Magriba suka tashi.