Sashe 97
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Ikram zaune ta yi shiru yayinda yan uwanta ke faman danne-dannensu a waya, babu kunya Jidda da Fadila harma Baraka na aikin sanya hoton Amarya da Ango a dp, harma da aikawa group na zuri'a Baraka ta yi. Intisar na kwance saman katifa tana shan iskar fanka ga tulelan cikinta wata shida tana kallonsu da sauraron hirarsu tana dariya jin Aisha na fadin.
"Um su Yaya Faruk ashe shi yasan me ya hango da ya mak'alewa 'yar aikin Mami." Suka kara darawa.
Hankalin Intisar ya kai ga Ikram, ta zunguri bayanta da kafarta. Ikram ta dubeta, da hannu ta yi mata alamar tambaya na meke faruwa?
Ta yi murmushin yak'e sannan ta girgiza kai a nufinta babu komai. Intisar itama murmushin kawai ta yi duk da ta fahimci lallai akwai abinda ke damun Ikram din, tun zuwansu ta yi sanyi kamar wata miskila yanzun.
Ita kuwa Ikram ganin haka yasa ta wayancewa ta hanyar mikewa ta dubesu.
"Bari naga Hajiya Mama."
Daga haka ta mike ta fito tsakar gidan, saidai kai tsaye waje ta fito inda matasa da wasu cikin matan gidan ke tsaitsaye, wata hira ta ke yi wasu kuwa kawai gaisawa da yan uwa. Ta yi ta faman wulk'a idanu tana mai fatan ganin Gidado, cikin sa'a ta hangoshi saidai hangen nasa baiyi mata dadi ba don kuwa tsaye ya ke da Hafsa sai wata mace wacce ta kasance Yaya awajen Gidadon suna hira da dariya, ta kasa dauke idanu daga kan Gidado wanda ayau shigar fararen kaya ya yi ya dora bak'ar hula akansa. Babu zato ya kallo gefenta, murmushi ne saman fuskarsa, murmushi ta sakarmishi ba tare da ta san lokacin da ya su6uto mata ba sannan ta yi saurin kauda kai ta juya ta koma ciki. Ya soma fahimto wani abun a irin kallon da Ikram ke yi mishi, ya sha kamata tana satar kallonsa daga sun hada ido sai ta kauda kanta, a farko ya dauka kuskuren fahimta ne saidai zuwa yanzun ya soma saka alamar tambaya ga hakan. Ya basar da tarin tambayoyin da ke yawo a kwanyarsa ya cigaba da maganar da sukeyi akan zuwan Hafsa Abuja inda ya ce babu inda zata je ita kuwa ta kawomishi abokiyar shawararsa kuma yayarsa Sumayya akan ta lalla6ashi saidai firr ya k'i aminta acewarsa ta ji da karamin cikinta tunda tana fama da laulayi, dole ta hakura don daman karambani ya kaita matsawa kanta akan zuwan saninta da Gidado, shi din kaifi daya ne.
Misalin takwas da rabi na dare Ummi ta samu waya daga Mijinta akan ta fito yana kofar gida. Ta nunamishi akan ya yi hakuri akwai mutane ya nuna baisan zance ba.
"Na baki mintuna biyar karki wuce Malama, gani kofar gida. Mutanen ai sun san mijinki ne."
Ta ajiye wayar a sanyaye ganin ya katse ba tare da ya ko saurareta ba. Dada ta dubeta, don ta shigo wajen Dada daukar chajar wayarta.
"Idan kiranki ya ke karki k'i zuwa Boddo, mijinki ne."
Daga haka Dada ta fice, a kunyace ta mike rike da chajar ta fito, saida ta wuce wajen Amina ta bata har wayar sannan ta yafa mayafi akan doguwar rigar jallabiya da ta sanya don bacci daga haka ta fita tana ra6e-ra6e. Ta ci sa'a mutanen kofar gidan sun ragu sosai, ta hau lek'e-lek'e saidai ko mai kama da shi bata gani ba, sai hon da ta ji wanda ya sanyata duban motar, jeep bak'a wuluk sai shek'i ta ke, ba ka ganin na cikinta.
"Bismillah Amarya, angon na ciki." Cewar Jafar kenan abokin aikin Faruk wanda bata sanshi ba sai a yau ta soma ganinsa. Ta gaisheshi tana sunkwui da kai, ya amsa, kafin ta isa ya budemata kofar baya, ba musu ta shiga ta zauna sannan ta rufe kofar. Sanyin Ac da na tsadadden turaren Faruk Danzaki shi ya soma bugar gangar jiki da kofofin hancinta. Ta dan d'ago ta dubeshi, wannan katon sanye ya ke da riga fara k'al da dogon wando bak'i, ganin sun hada idanu yasa ta saurin sauke kanta.
"Ina wuni."
"Bazan amsa ba, keda ki ka so ki k'i fitowa wani wai mutane."
Ta yi shiru tana wasa da zoben hannunta. Ganin shima bai ce uffan ba yasa ta fadin.
"Ka yi hakuri don Allah."
Ya lumshe ido yana murmushi alokaci guda kuma ya tura yatsunsa na dama cikin sumar kansa.
Ba zato kuma ta ji kansa saman kafafunta yana duban fuskarta, yanayin jikinta ya sauya, ta na mai jin wani iri tun daga tsakiyar kanta har kafafunta. Bata kuma ankara ba, ya kunna wayarsa hakan ya taimaka wajen ganin fuskarta sosai, ta runtse idanu zata kauda kai saidai bata samu damar hakan ba don tuni ya ajiye wayar ya janyo fuskarta zuwa tasa. Nan kuma lamura suka chanja daga gareshi zuwa gareta. Don kansa ya saketa ya na dubanta, ita kuwa mayafinta ta sha zata rufe fuskarta yayinda ta ke faman sauke ajiyar zuciya.
"Kimin alfarma daya, kinji?"
Ya yi maganar cikin rad'a, a hankali ta daga kwayar idanunta ta dubeshi, idanunsa a rufe sai ta ganshi kamar mai shafa mai na k'ara hasken fata sakamakon hasken da ta ga ya yi mata. Bai saurari amsarta ba ya bude idanu cikin nata ta yi saurin wayancewa da kallon kasa. Murmushi ya yi.
"Abinda ki kemin a waya shi na ke fatan samu yanzu."
Gabanta ya buga, ta dubeshi kadan ya shagwa6e fuska.
"Please."
"Ka yi.."
"Ba za ki bar motarnan ba sai kinyi ko kuma na wuce dake Otal."
Ya fada babu alamun wasa, tasan sarai zai iya aikatawa. Ta runtse ido tana ji kamar ta yi me, ta daure ta kai hannu ta ja wayarsa ta danne hasken da hannunta, da sauri ta aikata abinda ya umarceta, dariya ya yi gami da mikewa zaune.
"Matsoraciyata." Ta hau murza idanu da hannu tana murmushi.
"Na yi masifar kewarki Ummina, ina kara sonki a kowane rana."
Shiru ta yi tana mai jin wani dadi a kasan ranta.
"Inama zan iya bayyanamaka irin son da nake maka Yaya Faruk?"
Ji ta yi ya dora kansa a kafadarta ya sanyata jikinsa da hannu daya.
"Mezai hana Ummina, please sanarmin, na jima ina son jin kin furta kina sona da bakinki ba don bansani ba, saidai ina son ji."
Ta hau rarraba idanu, ya akayi maganar zuci ya fito fili har ya shiga kunnensa? Ta hadiyi miyau, anya zata iya?
'Ki ka yi wancan ma bare wannan?' Cewar wani 6angare na zuciyarta. Ta ji ya kara matsar hannunta.
"Please Ummi, taimaki Faruk dinki kinji? Ji yanda kirjina ke bugu don kaunarki."
Ya kai hannunta saitin kirjinsa, aikuwa bugun ya ke da sauri-sauri. Ya kai bakinsa saitin kunnenta.
"Zuciyata zata fashe da sonki."
Ta lumshe ido tana jinta kamar a Aljannah, murmushi saman fuskarta ta yi kasa da kanta. Dakyar ta bude baki ta yi magana.
"Ina...ina..." Sai kuma ta yi shiru.
"Say it please."
Ya yi maganar da siririyar murya, ta kasa jure sakonnin da ya ke aikamata, ta kara runtse idanunta.
"Ina sonka."
"Irin wanda na ke miki?" Ya yi tambayar ba cikin nutsuwa ba, ta rasa bakin amsawa, shi dinma bai saurari amsar ba ya cigaba da jero tambayoyin kamar a dakin jarabawa. Ita dai Um kawai ta ke binshi da shi, yanda ya ke mata yasa har hawaye ta ji sun zubomata na tausayi da kuma tsananin kaunar Faruk, ta ji ko k'uda bata kaunar ya shiga tsakaninsu, ta ji ta kara sallama mishi zuciya da gangar jikinta, ta ji nan duniya babu abin so da kauna gareta sai Faruk. Shi kadai tallin tal ta ke so ta ke kauna koda kuwa za'a kawomata wanda yafi Faruk komai da komai, ita sai Umar-Faruk Danzaki, babu gudu babu ja baya....! So kenan...!!!
K'arar wayar ce ta firgitasu, ya ja tsaki gami da dauka. Jafar ne, ya soma mishi magana akan dare ya yi haka kuma ga hadari a garin. Dole ya amsa da toh sannan ya ajiye wayar ya kwantar da kai saman kujera yana duban Ummi da murmushi saman fuskarsa. Ta kauda kai tana gyara zaman mayafinta.
"Saida safe."
Cewarsa, ta amsa,
"Allah Ya tashemu lafiya."
Daga haka ta soma kokarin bude kofar.
"Ummina."
Ta juyo tana dubansa.
"Ina sonki dagaske fa."
Murmushi ta yi wanda yasa ta k'ara burgeshi.
"Nima haka." Daga haka ta yi saurin bude kofar ta fice. Jafar ya shiga shi kuwa ya tsallako gaba suka bar unguwar.
Ta yi mamakin ganin har wasu sunyi bacci, saida Amina ke sanarmata cewa goma ta wuce sannan ta yi guum kawai da bakinta duk kunya ta isheta sai kuma ta hau fadin.
"Lokaci yanzu ba dai gudu ba, Allah Yasa mu cika da imani."
"Amin dai." Cewar Amina da sauran wadanda basu kai ga bacci ba suna masu danne dariyar da ta tahomusu.
Washegari aka rankaya Jar Kwami inda aka ga tsoffi aka gaggaisa shima Ango ya je suka ganshi sannan ya wuce da tawagarsa a ranar, su kuwa su Ummi ba su suka baro Gombe ba sai washegari bayan ta sha nasihu daga iyayenta da kakanninta, Malam Balarabe har kuka ya yi na ganin zai kara nesa da diyartasa saidai wannan karon hankalinsa kwance tunda yasan gidan aure ta nufa. Mutan Jar Kwami kowa aka nuna mishi Mami da su Hajiya Mama matsayin surukan matar da Abubakar zai aura wato Ihsan sai su hau cigiyarta saidai ace musu bata zo ba, koda Ihsan ta ji baki kawai ta ta6e don har kuka ta yi sakamakon ganin hoton Ummi da Faruk saidai ko zata mutu ta barshi kenan, amma har lokacin akwai ragowar tabon sonsa cikin zuciyarta.
*** *** ***
[truncated by WhatsApp]
[2/5, 6:53 AM] +234 703 962 5239: DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Sadaukarwa ga dukkan masoyan FAR HAS....!
117
ABUJA
Amarya da danginta har ma da dangin miji suka iso gaba daya, Hajiya Babba da su Hajja wacce ta sauko ta dangana, suka tarbesu hannu bibbiyu. Har da kishiyoyin Mami, wato Hajiya Binya da Lubna da yaransu, su Iklima yanzu gaba daya ta chanja kamar ba ita ba don har rungume Ummi ta yi.
Ummi a dakinta ta sauka da kawayenta wannan karon ko Amina ba'a ware ba.
Saida sukayi sallah sannan aka ci abinci, a ranar ne zaayi Dinner, ango ya wuce da amaryarsa. Gidan a cike suka iskeshi sakamakon ranar ne Hajiya Babba ke yininta. Wanka suka sanya Ummi ta yi ta hade cikin wani tsadadden leshi ja mai adon duwatsu, dinkin ya zauna d'abas a jikinta, haka aka rufemata kai aka kaita wajen su Hajja, nan suka rufarmata da nasihu, bayan kammalawa aka wuce da ita wajen Hajiya Babba da kawayenta har su Hajiya Mama gaba daya, suma suka tofa nasu albarkacin bakin har Hajiya Babba na fadin. "Ummi diyata ce daman."
Wannan furucin ya yiwa Ummi dadi matuka, abin mamaki wajen la'asar sai ga Husna da abokan karatunsu na Islamiyya, ashe Faruk din da kansa ya kaiwa Husna kati na dinner party ta bawa abokan karatunsu harma da na yinin Hajiya Babba inda duk suka sanya ankon da suka yi, har kunya ta ji don tasan ta fadawa Husna bikin kuma suna waya saidai bata samu damar bata kati ba. Su Fati burinsu bai wuce na son sanin waye mijin ba don har lokacin Husna bata sanarmusu komai ba hakanan ko hotonsa basu gani ba.
"Ni dai Anti Ummi sai rarraba idanu nake naga ta inda zan ga Yayanmu."
Ummi murmushi ta yi kawai.
"Za ki ganshi."
Husna ta dara.
Nan kuwa Ummi ta shiga nunamata yan uwanta suna gaisawa.