Sashe 69
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
88
Misalin karfe goma na dare, Ummi kwance saman gado tana tunane-tunane, ta ji shigowar su Ikram, wannan dalilin ne yasa ta rufe idanu tamkar mai bacci. Tana ji suna faman hirarsu kafin Ikram ta ce.
"Wai wannan isashshiyar har ta yi bacci? Lallai yau ko ta jira a yi mata iso kan gadon? Um, kan mage ya waye."
Baraka ta dara.
"Ai ko bata hau ba dole ma ta komo, ni banason abinda zai ta had'amu da Hajiyarmu muna 6ata ranta kan abinda mukasan mun fishi."
Ikram ta ta6e baki gami da mikewa. Cikin muryar rad'a ta ce. "Bari yau dai na bincika wayar nan nata." Ta mike tsaye tana mai zagayawa 6angaren da Ummi ta ke, Ummi na jinta ta dauki wayar a hankali, can kuma ta ja tsaki.
"Wallahi nasan aikin Yaya Faruk ne don wannan illiterate din ba zata iya ba."
"Me kenan?"
"Wai pattern lock yasa mata."
Baraka ta yi dariya, za ta ajiye wayar ne hankalinta yakai ga zoben dake yatsar Ummi, ta zaro ido tana karemishi kallo kafin ta dubi yar uwarta da muryar rada ta ce.
"Kinsan zoben gwal ne a hannunta."
Baraka ta mike tana mai soma takowa wajen hadi da fadin.
"Wasa ki ke."
Sai kuma ta kama yatsan a hankali ta kurawa zoben ido itama, kafin kuma ta saki yatsan.
"Lallai abin babba ne, a ina ta samu?"
Yar harararta Ikram ta yi suna kokarin barin wajen.
"Wa ki ka san zai bata bayan Yaya Faruk? Ai inaga nan gaba ma (salary) dinsa gaba daya akanta zai k'are. Har tausayi ya ke ban, Allah dai Ya karya wannan sihirin tun ba'a kai ga aurennan ba, idan kuwa aka yishi ba karamin mijin tace zaayi ba."
Haka sukayita hira akanta tana jinsu hakanan tana ji kamar ta yi kuka har suka gaji suka gangaro kan Ihsan. Inda Baraka ke fadin tasan mijinnata, don kuwa saurayin wata kawarta ce a baya, ta tabbatar shi din yana da yanmata kala-kala acewarta saidai Ihsan ta yi hakuri ta kauda idanu akan wannan tunda har ta nuna ta ji ta gani.
Tun tana jinsu har bacci ya yi awon gaba da ita.
Cikin dare aka yi ruwa sosai wanda bata da masaniya sai washegari bayan tashinta daga bacci. Ruwa duk ya shigo ya jik'a labulen dakin, ta dubi inda su Baraka ke kwance, har lokacin (karfe shida da mintuna) basu tashi ba, murmushi ta dan yi, tasan jiya sun jima basu kwanta ba.
Kai tsaye wanka ta fad'a sanin cewa da wuri zasu wuce don Hajiya Babba ta ce kafin takwas zasu tafi. Tana fitowa ta iske Baraka zaune bakin gado, itama bandakin ta shiga tana mitar Ummi bata ko tashesu sun yi sallah ba, ita dai hakuri kawai ta bata daman ita fashi ta ke.
Garin ya yi sanyi-sanyi hakanan har lokacin akwai hadari bai gama yayewa ba duk kuwa da cewar duhu bai gama fita ba. Ta shirya cikin wani bulun Swiss Atamfa mai haske, tana da adon manyan fulawoyi wanda acikinsu aka yi kwalliya da kalar bulu mai turuwa. (Lol..ku nemi Aysha ku siya). Dinkin riga da siket ne, rigar simple akayi mata mai hannu (3 quarter) ta zauna das a jikinta, hoda da kwalli kawai ta shafa, lokacin har Baraka ta fito ta yi sallah ta shiga wanka, ita kuwa Ikram na saman darduma tana addua saidai idanunta na satar kallon Ummi don duk hassadar mai hassada bazai k'i aminta da kyawun da ta yi ba. Ko ita kanta shigarta ta burgeta saidai ba fa zata nuna ba.
Ummi ta tattara kayanta a jaka sannan ta soma gyara saman gadon bayan ta dauke musu wayoyinsu, tana kokarin share dakin ne Intisar ta shigo da sallama. Bayan sun amsa ta zaro ido tana duban Ikram don ita tuni ta yi wanka ta saka doguwar riga 'yar kanti mai mayafi.
"Ke Ikram, ko wanka ba ki yi ba?"
Ikram ta mike tana cire kayan jikinta.
"Wallahi yanzu zan shiga yau sanyin da gari ya yi yasa mun makara sallar Asuba ma."
"Kedai fadi gaskiya tun daga can dakin muke jin hirarku fa har muka yi bacci." Intisar ta amsa lokacin da ta shigo dakin sosai.
Ummi ta gaisheta, ta amsa fuska a sake tana kallonta, kwarai shigar Ummi ta burgeta don ta yi kyau ainun, ga dirin jiki da Allah Ya bata.
Fitowar Baraka ce ta katse tunaninta, Ummi ta fice don dauko tsintsiya da tsumman tsane ruwan da ya shigo ta windo.
Babu kowa a falon sama, kai tsaye ta sauka k'asa, nan dinma ko fitila ba'a kunna ba, ta karasa hanyar kicin inda anan ne ta gano haske, Larai ce ke faman soye-soye tare da Hafsatu sabuwar mai aikin Hajja, ta gaishesu Larai ta kama baki.
"Oh ni, Ummi kinga yanda ki ka haska kuwa?"
Ta basar da zancen tana dan murmushi lokacin da ta ke kokarin daukar tsintsiya da abin kwasar shara.
"Larai tsumman guganku yana ina?"
"Me zaki yi 'yar nan? Ke ai kin wuce aiki yanzu."
Ummi ta dan daure fuska.
"Ni wallahi bana son hakan da ki ke yimin."
"Jimin 'ya, Hafsatu ko karya nayi ne? Ina Ummi ina aiki?"
Hafsatu dake mikawa Ummi tsumma ta yi dariya kawai, ai kuwa Ummin na kar6a ta fice da sauri don dagaske Larai ta bata haushi. Tana jin dariyarsu. Ta soma taka matattakala ta ga an kunna fitilun falon, hakan yasa ta kai dubanta ga mai shi. Ido hudu sukayi da shi yana sanye da riga da wando yan kanti sai jacket da ya dora bak'a a saman rigar wacce kana hangota fara k'al, hakanan farin wando ne dogo na jeans a jikinsa.
Idanunsu suka sark'e cikin juna, wani kyau ta ga ya yi mata na daban duk da ta lura da jan da saman hancinsa ya yi can kuma ya saki atishawa, ya rufe bakin ta hanyar amfani da dan hankicif din dake a hannunsa. Kafin ya kai ga cewa wani abu, Haidar ya shigo shima sanye cikin kananun kayan, da sauri ta haye sama bata bari ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu ba. Ya numfasa yana duban Haidar wanda ke kokarin zama.
"Wai murar ce haka? Ai saida nayi-nayi akan ka kashe fanka ka nuna kai zafi ka ke ji."
Shima zaman ya yi yana mai dan ta6a karan hancinsa da ya ke ji yana mishi zafi.
"Daban da murata na zo saidai ba ta yi karfi haka ba sai yanzun."
"Ya dace ka nemi magani ka sha."
Haidar ya amsa yana kallon hanyar sama.
"Wai kada dai basu tashi ba? Muna da ayyukan yi fa."
Ya tuna hasken idaniyartasa wacce shigarta ta yau ta daukemasa hankali, murmushi ya danyi.
"Sun tashi mana."