← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 116

Sashe 106

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

                ***    ***     ***
                      KANO
  Kwance ta ke tana duban hotunan da suka shigo wayarta ta (whatsapp) don bisa al'adarta duk dare idan ta gama komai sai ta bibiya ta ga ko akwai wadanda basu dace ba ta goge, kamar abinda ya shafi gawarwaki da hatsari. Karaf, idanunta suka kai ga wani hoto wanda yasa ta mikewa zaune babu shiri. 
  Hoton Abubakar ne tare da wata 'yar ajinsu Rukayya Tsigai, ai ba shiri ta hau online ganin wacce ta aiko,  Zahida Taskira ce daya daga cikin yan ajinsu wacce suka sanyamata sunan sanadin surutunta da tone-tone don ba a sirri da ita. Inda ta yi mata bayani kamar haka.
  "Aslm, Ihsan please ba batun gulma ko hada husuma ba, inace wannan shi ki ka ta6a nunamin matsayin wanda zai aureki? Magana ta gaskiya guy dinnan na sanshi tare da Tsigai, saidai ban gayamaki ba time din kada ki ji haushi, idan har dagaske shi ki ka za6a matsayin mijin aure zan baki shawara ki chanja tunani saboda wallahi guy din yana da son mata, Rukayya ba wajen Partyn wata cousin dinta sukayi hoton nan kuma na tabbatar suna chatting."
  Kan Ihsan ya yi dum, ta rasa meke mata dadi a duniya, batasan lokacin da ta soma hawaye ba tana ambaton Allah, saidai me? Ko kankani bata ji soyayyar Abubakar ta ragu ba sai kishi mai zafi da ya turnuketa, ba don tana sonshi ba babu abinda zai hana a yau ta rabu da shi. 
  Bata maidawa Zahida amsa ba don tasan zai iya komawa kunnen Rukayya Tsigai, kawai sai ta kira Abubakar ta ce ya hau online zata mishi magana. 
  Badiyya na kallonsa yana waya yana tambayar ko lafiya duk ya rikice saidai bata ce uffan ba, banda murmushi, idan da sabo ai ta saba da halin Abubakar na hira da yanmata balle kuma ta tabbatar cewa wannan Ihsan ce don duk cikin yanmatansa tana da yakinin ita ya ke yiwa so na aure tunda har ankai da sanya rana. Mikewa ta yi ta bar falonnasa shi dinma bai tsaidata ba don hankalinsa ya tashi jin muryar Ihsan din ba'a hayyaci ba. 
   Nan ta aikamishi hoton, duk sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, shakka babu wannan hoton ya jima, yanzun ma ba ya tare da Rukayya sun rabu akan zafin kishin Rukayyar kan yanmatansa, shi kam kullum adduarsa bai wuce na Allah Ya yaye mishi wannan mugun hali ba. 
  Ranar kam Ihsan ta yi kwanan bakin ciki, dakyar bacci ya saceta don idanunta saida suka kumbura. 
Washegari da ciwon kai ta tashi, koda Mami ta tambayeta sai ta ji bakinta ya yi nauyi ta kasa fadamata, tsoronta kada a fasa auramata Abubakar don Allah shaida tana sonsa yanzun musamman yanda ya ke kasheta da soyayyarsa mai tsayawa a rai wanda ta tabbatar da shi ya ke yaudarar yanmata sai kuwa kudi. 
  Ikram kadai ta sanarwa, Ikram da ranar ta tashi da farincikin jin Hafsa matar Gidado ta haihu da kuma dan kishinta a kasan rai duk sai ta ji nata 6acin ran ba komai bane idan an hada da na Ihsan. Ta hau salati, tasan tabbas Abubakar yana da kula yanmata don tasan wata kawarta wacce tasan shi saidai batasan har zuwa wannan lokacin ba, nan ta shiga bata baki da nunamata ta cigaba da adduar neman za6in Allah, katse wayar kawai ta yi. Abubakar ranar ya kira yafi sau biyar saidai ta k'i dagawa, ya bita whatsapp hakanan ya yi mata text saidai ko kusa bata maida amsa ba.  
    A ranar dai suka shirya don kuwa bata iya dogon fushi da shi, abin mamaki Zahida ba ta daddara ba ta turo wani, ai kuwa ta sha zagi kafin a karshe ta rufeta yanda babu damar da zata k'ara shiga sabgarta. 
                 ***    ***    ***
        A KWANA A TASHI....!
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

   125

Tun Ummi na zuba idon ganin 6atan watanta, har dai ta ji shiru, wannan ya daga hankalinta, ga wani haske da ta kara hakanan komai nata ya k'aru, watarana suna kwance da Faruk ya dubeta. 
  "Ummina ban yarda ba, anya babu ajiyata a wannan cikin naki? Kwadayinki ya yi yawa, yau kice magwaro, gobe ki ce bakyason kamshin turarukana."
  Ta kwanta jikinsa tana mai turo baki.
"Nifa bani da komai."
Ya ja karan hancinta.
"Zamu tantance yanzu. Taso muje."
Ta mike zaune idanu a waje ta ke dubansa.
"Ina?"
"Asibiti mana."
Ta yi narai-narai da fuska. Ya yi saurin toshe bakinta da hannu.
"Shii..karki soma rok'ona don kuwa sai munje."
Ta langa6ar da kai tana sosa idanu.
"To ai..ai yau babu aiki."
Cikin muryar rarrashi ya ce.
"Wajen Dakta zamu je, bamu jima da waya ba ya cemin yana asibiti." 
Ta turo baki.
"Please FAR HAS, allura fa zasu yi min."
  Ya matso da ita yana ji kamar ya hadiyeta. Saitin kunnenta ya yi magana.
"Ba wanda zan bari ya soka maki karfe a jiki, tashi ki chanja kaya kinji?"
  Ba musu ta mike, daman sanye ta ke da riga wacce ko k'ugu bata karasa ba sai kuwa wando shima da bai kai gwuiwa ba, ta kai kofa ya kira sunanta. Ta juyo fuska a turnu6e.
"I love you."
Furucinsa yasa ta murmusawa gami da lumshe ido ta budesu akansa. 
"Love you too." Ta furta a hankali ya sanya yatsunsa cikin sumar kansa yana murmushi gami da sauke ajiyar zuciya, wasu kance soyayya na raguwa bayan aure, shi kam ya rasa dalilin da yasa koyaushe soyayyarta gaba ta ke k'ara yi a zuciyarsa, Allah Ya sani kauna fisabilillahi ya ke yi gareta, tun dora idanunsa da ya yi akanta, bai ta6a hutawa daga tunaninta ba har saida ya mallaketa. Mikewa ya yi shima ya fad'a bandaki don kimtsawa. 
   Lokacin karfe hudu ta kusa, Ummi ta kammala shirinta cikin wani koren leshi dinkin riga da siket, ta yafa farin mayafi ta sanya takalmi flat mai kalar fari da baki. 
   Saida sukayi sallar la'asar kafin su fito kasancewar ranar bata da lesson don daga litinin zuwa juma'a sukeyi, kwarai Malamar na yabawa da kokarin Ummi don har mamakin kaifin basirarta ta ke, ko wata basuyi da somawa ba, ta iya abubuwa da dama.
   Gogan kananun kaya ya sanya, wandon 3quarter ne fari k'al, sai kuwa t-shirt dinta mai layi-layi fari da bak'i. 
  Idan ka gansu dole ka k'ara daga ido ka kallesu don kuwa sunyi matukar dacewa da juna. Saida ya budemata 6angarenta ta shiga ta zauna kafin shima ya shiga, maigadi ya budemusu gate suka fita. 
   A asibitin suka iske Dakta Ridwan, yana duba wasu kasancewar yawanci ranakun hutu, manya yafi gani, saida ya sallami wasu kafin suka shiga.
  "Ango na Amaryarsa." Ya fada yana dubansu fuska dauke da murmushi. 
Suma murmushin sukayi Ummi na sunne kanta, Faruk ya kara matse hannunta cikin nasa.
"Ya son ranka?"
Sukayi dariya don tsakaninsu babu wani zancen raini, sun dauki junansu tamkar abokai musamman su ukun nan idan an cire Babban Yaya wanda ba koyaushe ya ke biyewa shiriritarsu ba. 
   Ummi ta gaisheshi ya amsa tana tambayar su Muhsin. 
"Suna nan lafiya."
"Ai ba'a kyauta ba, ya dace a kawo mana su koda ran Friday ne." Cewar Faruk. 
  Dakta ya yi dariya.
"Karku damu, duka yaranku zasu zo hutu, ai (second term) din ya kusa k'arewa."
  "Wai me? Noo, kar a kawosu duka, ba zasu takura min Bebina ba."
Dariya Dakta ya yi.
"Oh, har ka tabbatar da ka samu bebin? Toh ai sai ku tashi ku je Allah Ya raba lafiya." Ya karashe yana mai daure fuska da wasa.
Faruk na murmushi yana mai dafe goshi.
"Please ka yi hakuri, dubamin ita yau wata biyu kenan bata ga period dinta ba."
Saida gaban Ummi ya fadi ta dan dubeshi, ya dagamata gira yana murmushi.
"Eh ko?"
Ta kauda kanta a kunyace. Dakta murmushi ya yi ya ce.
"Lil kenan."
Daga haka ya janyo takarda ya yi rubuce-rubuce bayan gama yiwa Ummi tambayoyi daga haka ya mikawa Faruk takardar.
"Sai ka je a auna fitsarinta."
Ba musu ya kar6a suka fita, bayan fitarsu ta dubeshi.
"Kai FAR HAS, ko kunyar Dakta ba ka ji ba ka ke magana haka?"
Ya daga kafada kadan yana yamutse fuska.
"Don bakisan ma waye Dakta ba shiyasa ki ke fadin haka, sa'ar da na ci yana jin kunyar idanunki da sai na koma ni ke jin kunyarsa."
Dariya kadan ta yi kawai batare da ta ce uffan ba. Bayan angama auna fitsari an basu sakamako suka koma ga Dakta. Ya bude takarda ya karanta yana murmushi kafin ya dubesu kadan, Faruk ji ya ke kamar ya warce takardar, cikin zakuwa da son sanin meke faruwa ya ce.
"Wai don Allah ka yi magana mana."
Dariya Ridwan ya yi. 
"Bani goron albishir."
Ya fada yana mai mikamasa hannu. Faruk ya wawuro na'urar auna jini (Sphygmometer) ya dora saman hannunsa. Har Ummi saida ya bata dariya, shi kansa dariyar ya yi. 
  "Toh nagode dai na tausayamaka tunda naga ka damu."
Ya dubi Ummi fuskarsa a sake.
Chapter 106 · 0% Book details