← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 116

Sashe 23

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

                    ***  ***  ***
   'Me nayi?' Ya jefawa zuciyarsa tambayar da baisan amsarta ba. Ya jingina kansa jikin kujera gami da k'urawa talabijin ido. Babu abinda ya yi banda sada zumunci. 
   'Kar ka d'arsawa zuciyarka wani abin daban, kana tausayinta ne kawai.'
  Cewar wani sashe na zuciyarsa. Ya kauda maganar gaba d'aya ta hanyar kunna talabijin.

                     ***  ***  ***
  Sallamar da aka doka ne ya katse hirar da Habiba ke kwasa da mijinta. Ganin mai sallamar yasa duk suka washe baki, mijinta Yahuza ya mik'e.
  "Kai lale da mutan Kaduna."
  Fad'in Habiba kenan tana kokarin gyara tabarma. 
    Bayan sun zauna aka shiga gaisawa, Habiba ta zari gyale ta fita siyo ruwa. 
   Hajiya Munira kenan, 'yar kanwar Yahuza mijin Habiba, wacce ke auran babban ma'aikacin gwamnati a Kaduna. Ta zauna suka soma gaisawa da kawunta yana tambayar sadda ta iso. 
  "Kwanana biyu kenan ai Kawu."
  Ya jinjina kai kafin su cigaba da hira a haka har Habiba ta dawo dauke da leda mai ruwan sanyi da lemu tana fad'in.
  "Um, kaga fa tsabar zumud'i ko kudi ban dauka ba, bari yarinyarnan su zo su mik'a mishi."
    Suka dara sannan aka hau hira. A haka Dija ta dawo ta samesu. Ta ji dadin ganin Munira, suka shiga hira harma a karshe Munira ta nuna tana gayyatarta Kaduna koda na sati ne. Babu musu Dija ta nuna zata. 
   Kawu Yahuza da Habiba sunyi murna kwarai, ko ba komai sa dan huta da surutun mutane na cewar anbar yarinya ba aure sai gantali. Man aka tsaida idan Munira zata wuce, tare zasu tafi.
       Koda ta gama kwanakinta a kauyen, suka shirya tare da Dija da yaranta biyu, direbanta ya kwashesu zuwa Kaduna.

                   ***  ***  ***
                       ABUJA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  33

A kofar dakin sukayi kici6us, ya  sanarmata wai ta zo ta k'aro faranti su Yaya Faruk zasu ci abinci. Ta amsa da to, a sanyaye ta gyara daurin dankwalin atamfarta sannan ta bi bayansa. A zaune ta gansu a saman tebur gaba daya, ta dauke kanta ganin shi dinma gogan idanunsa akanta suke, kicin din ta fad'a ta bi umarnin Mami. Ta dauraye ta goge sannan ta karasa garesu cikin sassanyar tafiyarta, sam bata da kwaramniya...

     Ta kawo falon, tana kokarin ajiye suka had'a ido da ihsan ta samu tsarabar harara kuwa. Ta ajiye a gaban Faruk, wani daddad'an kamshi na turare ya bugi hancinta.
  "Thank you."

 Daga haka ta juya ta bar wajen, ya bi bayanta da kallo kafin ya numfasa muryar Ihsan ta doki kunnuwansa.
"Let me serve you."
  Ya dubeta ya dan murmusa gami da gyada kai, cikin siririyar muryarsa ya amsa.
  "Kar ki cika, ban tare da yunwa."

Suna ci suna hira, jefi-jefi yakan dubi hanyar da ta bi, Mami ke faman jan shi da hira yana bata amsa. Ihsan gaba d'aya ta gama tafiya a kallonsa, sai yanzu take tabbatar da hakikanin gaskiyar abinda take ji game da yayannata. 

  Ummi a d'aki zaune ta yi zugum tana tunani. A karshe ta d'aga rigarta ta shinshina gami da lumshe ido. Ita kam tana son kamshi a rayuwarta don dai babu yanda zatayi ne ta samu. Musamman wannan turaren da ta ji awajen Faruk, sai ta ji ya doke duk wadanda ta saba shak'a wajen masu gidan. 
   'Komai na Yaya Faruk ba irin na kowa bane, komai nasa daban. Ya ji dad'in rayuwa.' Cewar wani sashe na zuciyarta. 
   'Kada ki kai kanki inda Allah bai kaiki ba Hasiya, babban goro fa sai magogin karfe, a komai na rayuwa Faruk ya d'ara ki, babu gatan da Allah bai ba shi ba. Yafi karfinki nesa ba kusa ba.'
  Wannan tunanin yasa ta numfasawa, wani hawaye ya taho mata wanda bata iya hanashi kwaranyowa ba, shikenan su yan aiki basu da gata? 
  A daren dakyar ta iya kokawa da zuciyarta har ta samu ta runtsa domin kuwa bata k'ara fita falon ba, asalima batasan sadda Faruk ya bar gidan ba, ta dai ji maganar Ihsan na fad'in  Babban Yaya wanda ya nuna shima yazo daga baya.

     Tunanin duniya ya ishi Ihsan, ta gama tabbatarwa lallai tana kaunar Yaya Faruk, a wannan daren yini ta yi kallon hotonsa wani dad'add'e da sukayi da Adnan da Haidar. Karshe dai ta kirashi a waya, bayan sun gaisa ya nemi sanin wace don bil hakki ba shi da lambarta. 
  "Ihsan ce." 
  Ya yamutsa fuska cike da mamaki sa'ilin da yake goge fuskarsa da tawul daga shi sai gajeran wando ya fito wanka.
  "Oh, kanwar Adnan?"
Ta ji haushin kanta, wato ko lambarta babu a wayarsa? Da tasan da haka da bata bayar da kai wajen kiransa ba. Kamar zata yi kuka ta amsa da eh.
  "Ok, fatan lafiya?"
Ta daure ta had'iye 6acin ranta.
"Daman na kira na ji ya kuka isa gida?"
  Ya dan saki fuska.
"Alhamdulillah. Nagode."
  "You are welcome."
Ya dan murmusa gami da jinjina kai.
"Good night.". Daga haka ya ajiye wayar batare da ya katse kiran ba ya cigaba da abinda yake yi. Babban Yaya na gefen gado zaune yana tura sak'o email a laptop dinsa.
  Takaici da bakin ciki suka tararwa Ihsan, ta katse kiran don kanta. Duk da ta ji haushinsa, hakan baisa ta ji zuciyarta ta bar magagin kaunarsa ba. Inama zai aureta? Ta ayyana a ranta, wani tsalle tayi a saman gadonta gami da kwakwume filo tana murmushi, a haka har bacci ya soma fisgarta ta yi addu'a ta kwanta.

    Faruk yana kwance, ya zurfafa cikin tunani, a gefe yana dan tsintar hirar Babban Yaya da matarsa tamkar wasu sababbin aure, ya lumshe ido yana mai fatan bacci ya yi awon gaba da shi ko don ya daina ganin abinda ya ke gani a kwayar idanunsa, hakanan yabar jin sautin muryar da ta k'i gushewa a dodon kunnensa ba don komai ba sai don tsoron kada tunaninsa ya tabbatar da hakan, bayaso yanayin ya sauya zuwa ga abinda ya ke tsananin gudu. 
  Haka bacci ya sureshi cike da tunani da mafarkai masu dadi da ban mamaki.
   Washegari da wuri suka tashi, bayan sun kammala shiri suka dunguma zuwa daurin auren da Daddy ya turasu, sosai kuwa Alhaji Labaran ya ji dadin zuwansu, a karshe sukayi sallama suka nufi gidan Hajiya Mama. Basu jima ba suka wuce don a ranar zasu juya zuwa Abuja. 
   Suna komawa gida kuwa suka tattara suka bar garin Kano...!

       [truncated by WhatsApp]
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

35
                  KADUNA
  Mutan Kaduna sun isa lafiya lau, Dija cikin garin ya zamemata bak'o don bata ta6a zuwa ko'ina ba banda Katsina kauyen k'urfi inda nan ne asalin mahaifinta Yahuza. Ta yi mamakin ganin k'erarren gidan da Munira ke rayuwa cikinsa a unguwar Malali, ta sauke ajiyar zuciya har ta kasa 6oye mamakinta ta fito da shi fili.
  "Gidanki mai kyau."
Munira ta murmusa.
"Nagode 'yar uwa."

  Bayan shigarsu ciki ne ta gane wajen ba komai bane, domin sakin baki tayi tana karewa falon kallo wanda ya yi bala'in had'uwa. Zata iya cewa tunda take bata ta6a zuwa gida makamancin wannan ba. Haka Munira ta rakata har dakin bak'i a sannan ta koma ga yaranta Tasleem da Haris. 
  Ita dai Dija k'arewa komai kallo takeyi, tsaf, kamar ansan da zuwanta. Gado ne sai aka shimfida kafet a k'asa, a gefe sif ne maidaidaici na kaya, sai bandaki. Ina zata samu wannan a kauyensu kuma gidansu? Tunda dai akwai masu ginin zamanin, amma bata ta6a kwana ba. Tayi tsalle saman gado don dadi saikace wata 'yar shekara goma. 
    Munira ta dawo ta ajiyemata sabulu da soso a bandaki, ta umarceta da tayi wanka. Bayan ta kammala ta shirya tsaf sannan ta fito suka ci abinci saman tebur abin sai ya yiwa Dija banbarakwai, hatta yaran and saida sukayi mata dariyar yanda ta dunga nuna kauyenci saman tebur. A karshe suka tashi sukayi magriba mai aiki ta kwashe komai. 
Suna zaune a falon ita da yaran suna kallo, Munira kuwa na kicin tana shiryawa maigidanta abinci, suka ji sallamar maigidan.
    Gaba daya yaran suka mike suna ihun murna, hakan yasa Dina kallonsa. Sakin baki ta yi yayinda gabanta ya hau dukan tara-tara, haka mijin Munira ya had'u?

   Sanye yake cikin farar shadda, bak'i ne kuma dogo, yana da kyau babu laifi. 
  Ya rungume yaransa yana mai farincikin ganinsu, zuwan Munira da sauri ne yasa shi bud'emata hannu ta karaso ta shiga ya hadasu ya rungume gami da lumshe ido, a hankali ya yiwa matarsa rad'a ta dubeshi tana murmushi ta sakarmishi hararar wasa shima ya kashemata ido yana murmushin.
   "Sannu da zuwa."
Maganar Dija ta maidosu hayyacinsu, sukayi saurin sakin juna, ita kuwa tuni ta tafi a kaunar mijin Munira. Munira ta matsa da sauri shi kuwa ya dake ya amsa yana mai tambayarta mutanen kauye.
  "Duk suna lafiya, sunce a gaisheku."
  Ya amsa fuska a sake sannan ya maida hankalinsa ga Tasleem da Haris.
  "To, a jira nayi wanka na fiddo muku tsaraba ko?"
  Suka hau tsalle da ihun murna. Ya jinjina kai.
"Kuma ku nemomin tsarabar da ku ka kawomin idan ba haka ba nima zan fasa baku."
  Nan ya yi gaba yana dariya Munira da Dija na tayashi. Yaran kuwa kansu ya dauki chaji don basu yowa babannasu tsarabar komai ba. Haka sukayita tunani lokacin har Munira ta bi bayan mijinta, hakan yasa suka koma ga Dija don ta nemomusu mafita.
   Munira na shiga mijinta Deen (Zahraddeen) ya d'agata cak yana juyi da ita gami da fadin.
  "Oyoyo sweetna." Sukayi dariya, dakyar ta zame daga rik'on da ya yi mata ta dan daki kirjinsa. Cikin muryar shagwa6a tace. "Kaidai wallahi ba ka rabo da abin dariya."
Ya k'ara janyota yana murmushi da nok'e kai.
  "Eh mana, musamman ma idan agaban sweetna nake."
  Tayi dariya ta kwace jikinta gami da fad'awa bandaki don had'amishi ruwan wanka.
   Acan kuwa Dija ta kasa sukuni, hankalinta gaba daya baya wajen Tasleem da Haris masu tambayarta tsarabar da zasu bawa babansu. Mik'ewa ta yi.
  "Kuje kicin ku nemi wani abun da mamanku ta kawo.".  Da gudu suka wuce, dakinta ta koma ta zauna tana tunani, tunda take bata ta6a susucewa akan kowane d'a namiji ba kamar wannan, ta yi murmushi gami da k'udurta mugun abu a ranta.
Chapter 23 · 0% Book details