← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 116

Sashe 109

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

  Su Jidda daidai ga Hajiya saida ta nunamusu rashin dacewar abinda su ka yi, hakuri suka bawa Hajiyar kasancewa suna ganin girmanta ainun don bata kasance cikin surukai masu sanya idanu kan abinda ya shafi zamantakewar yaransu ba, ta kama girmanta hakanan bata daure musu fuska. 
   Bayan wucewar watan azumi aka gabatar da karamar sallah. Ko ranar da suka hadu da sallah a gidan Hajiya banda gaisuwa babu abinda ya hadasu duk kuwa da cewa basu bita da kallon banza ba. 
    Nan kuma ta soma shirin zuwa Kano halartar bikin Amina wanda dakyar Faruk ya aminta ganin tana fama da jikinta itama. Ko su Ikram sun zo zuwa saidai makaranta, itama Baraka na fama da ciki dan wata biyar babu damar zuwa. Da kansa ya kaita, kai tsaye gidan Mami ta soma zuwa inda zata yi kwanaki uku sannan ta wuce gidan Hajiya Mama har zuwa gama biki. Babu tarbar arziki daga Ihsan sai dai ta samu sosai daga Mami da sauran mutan gidan wanda yanzu suke zaman aminci. 
    Mami sai nan nan ta ke yi da ita, abin ya sanyata farinciki sosai. Ihsan kuwa kallo bata isheta ba, sai idan ita ta gaisheta ko ta yi mata magana sannan zata tankamata a dakile kamar bata so. Ga shi kuma daki daya suke kwana, wannan abin na bawa Ihsan haushi don dai ba yanda ta iya ne.
  Yau Ummi na kwance saman gadon Fahad wanda yanzun ya ke kwana dakin Adnan, tana tunanin yanda ita ke gyarashi a baya, lokacin sha dayan dare bata jima da gama waya da rabin ranta ba inda ya ke fadamata tsananin kewarta da ya yi. Ihsan ta shigo dakin daga falo, jin haka yasa ta yin makwas tamkar mai bacci. Itama duk a zatonta bacci ta ke yi, hakan yasa ta saka waya a handsfree tana amsawa.  Ita da Abubakar ne wanda rikici ne zalla.
  "Kasan ina sonka shiyasa, kuma kasan bazan iya rabuwa da kaunarka ba amma a yanda na ke jin labarin irin yanmatanka da tuni na yi watsi da lamuranka."
  Ummi ta yi shiru jin amsar Abubakar wanda ta ke mamakin inda ya bar matarsa a wannan lokaci.
"Ki kara hakuri da halina, ni nasan ina da son mata, ki yarda kawai wannan kaddar..."
"Kada ka karasa, wannan son zuciyarka ne. Daga waccan yarinyar ta sanka, sai waccan ta dora hotanka a dp dinta, na soma gajiya Abubakar, kishi na neman fasamin zuciyata."
Kawai sai ta sanya kuka, ya rude yana faman kiran sunanta da magiya kan ta yi hakuri, saidai ina, tuni ta katse kiran da ta ga bai bar kira ba, kawai sai ta kashe wayar gaba daya. 
Ta jima tana kuka kafin ta kwanta cike da tausayawa rayuwarta, yanzu idan suka yi auren haka zata dunga fama da shi? 
  Ummi ta ji babu dadi kwarai, tana ganin Abubakar kamar bazai aikata irin haka ba, ashe kusan jirgi daya ya kwasosu da Kb dan uwan su Faruk, koda bikinsu bata ganshi ba ta ji ance yana Ghana karo karatu. Ta tausayawa Ihsan ainun, ta dan juya ta dubi gadonta, ta bata baya saidai ta tabbatar bacci ya kwasheta, juyar da kanta ta yi gami da numfasawa.
'Rayuwa kenan, kowa da kalar jarabtar da Ubangiji zai mishi, Allah Yasa mu dace, amin.' Ta fadi a zuciyarta kafin ta yi adduoi ta kwanta itama.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  127

Kwananta uku gidan Mami har ankon bikin Amina, Mami ce ta bada a dinkamata. Har ta cika kwanakinta babu wata jituwa tsakaninta da Ihsan duk da ita Ummin bata dauki gaba da ita ba don duk wayewar gari sai ta gaisheta matsayin yar uwarta musulma, a dakile Ihsan ke amsawa. 
  Saida Mami ta soma biyawa da ita wajensu Hajja suka gaisa, har Hajja ta matsa akan sai ta kwana, dole ta barta anan ta yi musu kwana daya daman acewar Mamin, ya dace ta kwanarmusu, a wannan kwanan saida Hajja ta kara neman afuwar Ummi don shakka babu ta ji kunya musamman jin cewa Ummin na dauke da juna biyu, tabbas idan Rabo Ya Rantse to duk kiyayyarka da auren sai an yishi. 
    Ummi ta ji dadi ta nunamata babu komai, sun sha hira kwarai har da dariya da su Modibbo wanda ke jikinsa ya matsa mishi a yan kwanakin, washegari ta wuce gidan Hajiya Mama.  
  Nan ma ta ga kulawa da tarba mai kyau daga iyalan Hajiya Mama har ita kanta. Su Maryam kamar su hadiyeta.
  Amina Amarya ta yi kyau ta gyaru tsaf, anan gidan zaayi yinin biki, kwarai Hajiya Mama ta yi musu kara. Acan gidan Innar Amina, yan uwan babansu ne na Nijar da na Innarsu anan Kano suka cika gidan. Amina ta sha mamaki jin cewa Malam Balarabe da kaninsa Baffa zasu zo daurin aurenta, ta hadata da Dada ta waya inda ta bata hakuri gami da nunamata ta so zuwa saidai bata samu dama ba, Amina ta nuna babu komai. 
    Da dare suna zaune a dakin su Maryam gaba daya suna hira da dariya, wayar Maryam ta yi k'ara, ta mike da sauri ta fita. 
  "Mene na gudun? Ai munsan mai kiran, Adnan ne."
   Cewar Rukayya cikin daga murya. Amina da Ummi suka dara. Amina ta cafe.
"Kai ke kuma ba'a sirri dake." 
  Dariya Rukayya ta yi.
"Ai naga sai wani 6oye-6oye sukeyi kamar bamusan komai ba, gwara mu nunamusu mun d'agosu."
  Ummi da mamaki ta ce. "Wai don Allah soyayya su ke yi?"
"Ba ki da labari? Gaskiya Amina kinci amanar kauna da ba ki fesamata ba, ai kullum suna mak'ale da juna ta waya duk da wani 6oye-6oyen da sukeyi munsan komai, daidai da Hajiya Mama ta sani."
  Ummi fara'arta ta karu.
"Kai na ji dadi wallahi, Yaya Adnan ya yi dace kam, Maryam ba ruwanta halayenta na burgeni. Sun dace wallahi."
"Karshe ma." Cewar Rukayya daidai lokacin da Maryam ta shigo ta mikawa Ummi wayar.
"Ga Yaya Adnan ku gaisa."
Ta kar6a tana tsuke baki. Ta yi sallama ya amsa gami da fadin.
"Allah Ya kiyayemana ke ranki ya dad'e."
   Ta hadiye dariyarta.
"Ai ni na yi fushi Yaya Adnan, ka daina nemana kuma ko na kira layinka yanzu ba ya shiga."
"Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Na ji kunya biyu. Na farko kirana da Yaya Adnan da ki ka yi, na biyun kuma, kiran da ban yi miki da sabon layina ba kasancewar wancan ya fad'i sai na barshi. Ki yi hakuri Ranki ya dade matar bestie."
  Sukayi dariya a tare, ta girgiza kai.
"Har abada, Yayana ne kai wallahi. To na hakura, ya fama da biro da takarda?"
  "Gashinan sai kuyita tayamu da addua. Kinga surukarki ko? Ta yi ko akwai gyara?"
Ta daga idanu ta dubi Maryam da su Rukayya ke tsokana ta yi dariya.
"Ta yi 100%."
Ya yi dariya cike da mamakin yanda tasan wani 100% domin ko kusa ba shi da labarin ana mata darussa. Saidai kuma bazai iya tambayarta ba.
   "Yauwa Ranki ya dade, ai da kince akwai matsala tuni zan dakata."
"Wace ni da fadin haka?"
Suka dara kafin su yi sallama.
Chapter 109 · 0% Book details