Sashe 15
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ta sauke ajiyar zuciya, gami da zame jiki ta durkusa a wajen. Yau Faruk ne yayi mata murmushi? Sai tace tun zuwansu bata ta6a ganinsa cikin fara'a haka ba. Mai yiwuwa saboda farincikin bikin dan uwansa ne. Jin da tayi ana ihu da shewa daga falon ne yasa ta saurin mikewa itama ta samu dama dakyar tana lek'e. Turare ta gani wata tsohuwa cikin wadanda suka zo daga Adamawa tana ta fesawa Ango da Amarya. Masu hoto suna faman yi, Faruk na daga hannun kujera zaune agefen wata mace da bata fi shekaru ashirin da bakwai ba, wacce itama cikin bak'in Adamawa take. Sai hira sukeyi suna dariya. Sunyi kama kwarai, kana gani ko ba'a fada ba kasan jini d'aya suke. Haka dai aka gama hotuna, Ango Haidar da tawagarsa suka fita. Wannan karon banda yayyun Haidar da Faruk, su kam zama sukayi ana gaisawa da hira da 'yan uwa. Tana ji anata yiwa Faruk tsiya akan shima ya dace yayi aure, abin banda dariya babu abinda yake ba shi, domin shi dai har kawowa wannan lokacin bai ga matar da ta kwanta mishi a rai ba har yakejin cewar zai iya aurenta. Duk cikin masu nuna masa kauna da so, duk cikin masu yi kishi tallar jikkunansu batare da sun buk'aci ko sisinsa ba, babu wacce ya ta6a yiwa kallon rahma. Asalima wannan d'abi'ar gaba daya haushi take ba shi wai ace mace ke tallatawa namiji kanta, yana daukar hakan a matsayin rashin aji da sanin darajar kai.
Dakyar ya samu ya silale ya fito daga falon, Ummi ta bi bayansa da kallo sannan ta maida hankali ga tsoffin dake faman shige da fice suna rabon abinci.
"Ummi." Ta ji muryar Amina a kanta. Wani sanyi ya mamayeta, ko babu komai zata samu abokiyar hira. Ta zaro ido tana murmushi.
"Anti, kinga kuwa yanda kikayi kyau? Masha Allah." Ta harareta kadan
"Lallai ma Ummin nan, wallahi ban kaiki ba, kinga yanda kikayi kyau kuwa yau?"
Ummi ta girgiza kai.
"Ban kaiki ba Anti."
Amina ta dara gami da jan hannunta.
"Taso mu zagaya baya, tun dazu ai ina can."
Ummi ta mike suka zagaya. Babban fili ne mai shuke-shuke, nan dinma akwai mutane saidai ba kamar cikin gidan ba, kusan ma yanmata sunfi yawa anan. K'asan wata bishiya suka zauna asaman kujeru inda wasu yara biyu da Mace rike da yarinya wacce bata fi watanni uku ba suke zaune. Ummi ta hango kamannin matar sosai da Amina, hakan yasa ta gaisheta, cikin sakin fuska itama ta amsa. Amina ta dubi yaran.
"Ahmad, ja Kulsum ku tafi wasa Antinku ta zauna."
Ba musu yaron ya amsa sannan ya mike suka bar wurin, daman sun k'agu su tafi wasansu amma ta hanasu da cewar sai sun ci abinci.
Bayan sun zauna Amina ta kalli 'yar uwarta wacce daga ita sai ita a haihuwa.
"Anti Hauwa, wannan itace Ummi da nake baki labarinta. Ummi wannan itace yayata Anti Hauwa, daga ita sai ni a wajen Innarmu. Babbar yayarmu Anti Fiddausi tana Katsina, acan take aure. Yaranta biyu, da Kulsum da kuma wannan bebin, Anisa. Ahmad shine auta wajen Innarmu."
Bayan ta kai aya, Anti Hauwa ta sanya dariya.
"Toh 'yar jarida, oh Amina." Ta karashe tana kama ha6a, abin sai ya bawa Ummi da Amina dariya.
Anti Hauwa ta dubi Ummi fara'arta ta k'aru don kuwa babu abinda Amina ta 6oyemata dangane da Ummi.
"Sannu Ummi, fatan kina lafiya?"
Ummi ta gyada kai gami da sakin kyakkyawan murmushinta.
"Lafiya kalau Anti. Ya wajen su Inna?"
Abin ya yiwa Anti Hauwa da Amina dadi.
"Inna tana lafiya, taso ta zo amma matar kaninta bata ji dadi ba, ta je dubota. Watakil daga can tayo nan."
Ta gyada kai gami da yi mata fatan samun lafiya. Nan kuma hira sosai ta 6arke tsakaninsu. Anti Hauwa da Amina suka gangaro kan batun Saurayin Aminan, Bello wanda ya matsa akan shi zai turo magabatansa. Anti Hauwa ta bata shawara akan ta sanarwa Inna idan yaso sai a had'ashi da wani ya rakashi har can Nijar su gaisa da yan uwan mahaifinsu.
Haka suka tsayar da shawara.
Sun wuni tare, Anti Hauwa sai bayan la'asar ta bar gidan, Hajiya Mama harda bata kudi tayi na mota. Dakyar ta kar6a don mutunci da karamci irin na Hajiya Mama har yana so yayi yawa, mace ce da babu ruwanta. Harda kayan rabo ta had'a ta bata, ta sanya aka yiwa Inna (takeaway) na abincin biki tace ta kai mata domin ba wani nisa ne tsakanin gidansu Inna da gidan Anti Hauwa ba. Ta kar6a da godiya.
Tafe suke gaba dayansu da Anti Hauwa da Ummi da Amina, wadanda suka yo mata rakiya don ta samu abin hawa, kasancewar babu laifi akwai 'yar tazara tsakanin gidan da babban titi. Ummi na rike da Anisa wacce ke faman kalle-kalle idanunta tarr a bud'e. Yarinyar ta shiga ranta, haka kawai ta ji tana kaunarta ko don bata ta6a ganinta rik'e da yarinya k'arama haka bane? Oho.
A farfajiyar gidan, samari ne da d'aid'aikun yanmata suna hira, daga ganinsu kaga yan uwan juna. Suka wucesu suka fita.
Suna tafe suna hira a haka har suka iso titi, bayan sun samarmata d'an sahu, ta shiga sukayi sallama. Ta dubi Ummi da murmushi mai bayyana hakora a saman fuskarta.
"Toh Ummi, sai na ganki a gidana wataran ko?"
Ummi ta amsa da toh tana maida martanin murmushin. Suka juya tare da Amina suka kama hanyar komawa. A hanyar ma hira sukeyi, Amina na yi mata korafi akan ita ko dan fita unguwa bata tambayar Mami ne? Ummi ta ta6a baki kadan.
"To Anti wa nake da shi a garinnan?"
"Kina da mu, wataran ki tambayeta kizo na kaiki wajen Innarmu ku gaisa."
Murmushi Ummi tayi wanda yayi daidai da giftawar wata farar honda mai bakin gilasai ta gabansu.
"Wannan kamar motar gidan su Alhaji." Cewar Amina kenan. Ummi da batasani ba ta bi motar da kallo kawai wacce ta koma tafiya sannu-sannu tamkar matuk'in baya so. Kafin daga bisani ya fisgi motar ya k'ara gudu.
Ai kuwa kamar yanda Amina ta fad'a haka dinne, don suna isa kofar gidan suka iske motar a fake, na cikin motar baikai ga fitowa ba saidai kafarsa d'aya da ya fiddo waje. Ta madubin hannun kofar, Ummi ta hangeshi. Kansa a jingine jikin kujera yana amsa waya. Akayi katari suka had'a ido, gani tayi ya yafito ta da hannu. Abin ya bata tsoro, gabanta ya hau dukan tara-tara. Tayi saurin dauke idanunta don bata gaskata hakan ba. Har zasu shige ciki ya danna hon. Wannan ya sanyasu dakatawa.
"Da ku ake." Cewar Maigadi. Amina ta dubi motar, saidai bata hangi ko wanene ba sakamakon duhun gilashin. Suka zagaya suka isa ta mazaunin direba, idanunsa akansu, suka durkusa a ladabce suka gaisheshi. Yaya Faruk ya dago kanshi ya dubesu da idanunsa masu tafiya da dukkan wata diya mace mai lafiya da zata kalleshi. Ya gyad'a kai kafin ya maida dubansa cikin motar, hannu yasa ya janyo leda bak'a babba ya mik'awa Ummi.
"Ki mik'awa Hajiyata." Ta sanya hannunta dake faman rawa don gaba daya wani kwarjini yayi gareta, ta kar6i ledar wanda bisa kuskure hannayensu suka gogi juna har ta gogi tattausan gashin dake kwance a hannunsa, a gigice ta dauke hannunta had'i da kar6ar ledar tana mai amsawa da toh wanda bai fito sarari ba saidai kawai le66anta da ya nuna alamun hakan. Baice uffan ba har suka fice ya bisu da kallo, ya lura yarinyar kamar a tsorace take da shi. Ya dan ta6e baki cike da mamaki, mamakin bai wuce na ganin yara kyawawa haka ba ace wai suna aikatau ba karatu ba, tabbas ya tausayamusu. Ya kuma raina iyayensu wadanda tunaninsa yafi ba shi cewar kwadayin abin duniya ne kawai yasa suke sakin yaransu sakaka suna yawon gidajen mutane don bauta da neman kudi wanda duk yawan abinda zasu samu bazai haura dubu goma ba, aganinsa wannan cutar da rayuwarsu ce kawai. Ya lumshe ido, ya jima a haka kafin ya maida kafafunsa ciki ya rufe kofar gami da yin ribas yabar unguwar.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR