← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 116

Sashe 90

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Saida aka tashi ne suka samu damar ke6ewa. Anan Husna ta yi shiru tana kallon Ummi, ganin haka yasa Ummi soma magana.
  "Wata shawara nake nema agareki."
Husna ta gyada kai cike da k'osawa don sau wajen biyar kenan tana furta hakan amman ta kasa magana. 
"Ina jinki."
  Dakyar ta samu ta labarta mata kadan cikin labarinta wasu abubuwan kuwa ta sakayasu, ta nuna mata kawai dai tana fuskantar matsala yanzu da saurayinnata da aka daura aurensu aka bar biki daga baya. Ta karanto mata matsalar a sakaye sannan ta k'ara da fadin.
  "Husna kin ganni ko? Ban budi ido naga mahaifiyata ba, sannan ban samu wata kulawa daga kishiyarta ba, har zuwa yanzu da aka zo batun aurennan, sannan ni duka-duka ma a Islamiyyar Kano da na ke fadamiki ban jima ina zuwa ba, wani sa'in idan wata fita ta zo shikenan bana zuwa.  Ina cikin tsaka mai wuya Husna, ina 6atawa mijin aurena rai, ki taimakamin da iya abinda ki ka sani, yarda dake ne yasa na sanarmiki abinda ban ta6a fadawa kowa ba a makarantar nan."
Husna wacce ta cika da mamakin wai Hasiya yanzu matar aure ce, ta numfasa bayan kalamanta na karshe wanda yasa ta jin tausayinta.Murmushi ta sakarmata.
"Ki sha kuruminki k'awata, in sha Allah daga gobe zamu soma. Saidai abinda nakeson ki sanyawa ranki, shi fa mijinnan wajibi ne gareki ki bishi sau da k'afa, karki bari damarki ta wuce, idan ance biyayya ciki har da ba shi hakkinsa na aure idan ya nema tunda dai ansan da igiyarsa akanki, wannan zamanin ba'a sakaci Hasiya,  mata da yawa neman mai aurensu su ke yi, wasu kuwa kamar su jawo namijin ya kwanta da su su ke ji, ballantana kuma idan mijinki wani hadadden ne, tuni za ki yi sake. A baya ne za ki ji duk iyayenmu na irin wannan kunya-kunyar, ansan tana da kyau saidai bisa shawara ki rageta, ki rungumi mijinki hannu bibbiyu. Karki damu, yanzu kinga dai anzo daukata, bari zuwa gobe zan taho miki da wani littafi SIRRINMU na wata tsohuwar marubuciya sai kuma wani  Sinadarin Rayuwa shima marubuciyar ta yi kokari matuka wajen koyawa mata salon kula da miji da gida, zan kuma k'ara miki a kai. Duk fa litattafan Antina ne matar Yayana da nake hannunta, zan rufa miki sirrinki Hasiya koda baki nemi hakan ba."
Ummi ta dan ji sanyi, ta yi mata godiya sannan suka zagayo farfajiyar makarantar, anan suka yi kici6us da Fati. 
"Yauwa, anzo daukarki fa tun dazu Anti Hasiya."
Ummi na jin haka ta daure fuska.
"Nikam karki kara kirana Anti banaso wallahi."
Fati ta rike ha6a.
"Ah, ai sai na kiraki da fin haka, kin kai wallahi. Sai ma idan kin hadani da yayannaki."
Dariya Husna ke yi ita kuwa Ummi tsaki ta ja kafin a fusace kuma ta bar wajen. Ganin haka Husna ta sha jinin jikinta, ta biyota da sauri gami da dafe kafadarta.
  "Wai Hasiya kodai shine mijinnaki?"
Ummi ta juya, ganin Fati bata biyosu ba sai ma dagomata hannu da ta yi alamun (bye-bye) ta juyo ga Husna, kai kawai ta gyada mata a sanyaye.
"Innalillahi! Kai Hasiya wallahi ban ta6a ganin irinki ba, kina da kamar wannan me zai hanani zage damtse wajen ba shi kulawa ta musamman? Kodayake..."
Sai kuma ta yi shiru don ta tuna kalaman Hasiyar a dazu ta kuma fahimci cewa ko karatun litattafai ba ta yi, ita kuwa har na yanar gizo yi ta ke yi, tana kuma cin karo da abubuwan karuwa na Matan Aure, wasu kuma idan sunfi karfinta bata karantawa kasancewar yayanta kusan kullum sai ya bincika wayarta yasa ta ke takatsantsan. 
    Ummi babu abinda ta ce saima haushin kanta da ta k'ara ji, lallai kam ta yi babban kuskure a rayuwarta. 
  Suka rabu Ummi ta nufi motar, direban gidansu Haidar ne, Ikram na zaune ciki sai faman cika ta ke yi da batsewa. 
Ummi ta shigo sannan ta gaida Direban, ta kara da fadin.
"Ku yi hakuri don Allah, bansan ya zo ba."
   Tsaki kawai Ikram ta ja sai direban ke amsawa da babu komai.
  Earpiece Ikram ta sanya a kunnenta tana jin wak'a , ita kuwa sai ta maida hankalinta ga kallon hanya cike da tunanin maganganun Husna, kwarai ta yi ganganci, tasan har da hudubar su Anti Abida da Halima ya taimaka wajen k'in sakarwa Faruk. Wanda sam bai cancanci haka ba, sai ta ji tana zuci-zucin gobe ta yi ko don Husna ta damk'a mata litattafan.
Har suka isa ba wanda ya cewa wani uffan, koda suka shiga kai tsaye sama kowannensu ya nufa. Nan suka iske daga Babban Yaya sai ko Faruk da Hajiya sai su Jidda kowanne na kawo raayinsa, lefe Babban Yaya da Hajiya ne zasu hada, na Faruk bai wuce kawai gani ba, kudin ma sunce ya barshi, sai batun dinner party da suke yi da kuma fiddo anko wanda Babban Yaya ya ce su fadi irin wanda zasu yi zai kawo musu su za6a. Duk wannan za su yi shi ne a cikin sati biyu, saboda zuwa Adamawa da zasu yi su kwana uku su dawo don Modibbo ya matsa akan lallai sai an tafi saboda wadanda tsoffinsu basu sani ba. 
    Shigowar su Ikram dinne ya katse su, Faruk idanunsa akan Ummi ya kasa daukesu, haka kawai ya ke jin kewarta ainun, wannan karon fuskarsa a dan sake,  suka gaishesu sannan Ummi ta yi ciki ta bar Ikram anan, itama tana jin batun da akeyi ta mike zuwa nata dakin inda ciki ta riski Intisar kwance saman darduma ta idar da sallah. 
   Wajejan biyar na yamma, Haidar da Ridwan wadanda suka je daukar yara daga makaranta suka shigo ciki, don daman direban suka hutar da sanyashi dauko su Ummi kawai. Nan gidan ya k'are kacamewa, Ummi duk ta takura har saida suka wuce, koda aka kirata cin abinci ta ce ta ci, akan haka har fad'a Hajiya ta yi mata  gami da nunamata kada ta sake irin hakan ta dunga ci tare da su. Daddy yana dawowa daga Kano inda ya je ta'aziyya matasan suka koma wajensa har Hajiya, nan ya ke jin dukkan shirye-shiryensu, ya yi na'am da hakan, ya kuma ji dadin yanda kansu ke a hade har kowanne ya dauki nauyin abinda zai yi. Haidar na buga I.v da rabo ya dauka, shi kuwa Ridwan na dinner party, yayinda Babban Yaya da Hajiya zasu yi lefe, karshe Daddy ya dauki alkawarin yiwa Ummi kayan daki da komai na mata, acewarsa ko don zaman da ta yi da su ta cancanta, bai dace su bar iyayenta da nauyi ba, ta zama tamkar jininsu. Faruk ya ji dadi matuka, bakinsa ya kasa rufuwa, bawai don wani abin ba sai don ganin kowannensu ke nuna kaunarsa da wannan auren, hakazalika hadin kansu ya fi komai faranta ransa, fatansa har mutuwa su kasance tare haka. 
      Washegari sam basu hadu da Ummi ba, sai ta waya ta kirashi, wannan karon bai gwanyata ba don ya amsa, ta gaisheshi ya amsa ba kamar jiya ba, a karshe ta rasa abin cewa kawai ta yi mishi adduar sa'a sannan suka yi sallama. Daga lokacin kullum sai ta gyara mishi daki tas. 
    Koda ta je makaranta Husna ta damk'a mata litattafan, shikenan kuwa ta samu abin karatu, koyaushe cikin karatu ta ke yi har ta soma gano kuskurenta kwarai, har sai gashi tun tana kunyar wanke mishi undies har ta gwada yi na rana daya sai ta kasa shanyawa kawai ta matsar da labulen dake wajen kwamin wanka ta shanyasu a karfensa. 
  Ranar Alhamis ta yi wannan aikin, yana dawowa ya ganewa idanunsa, ido ya fiddo yana kallo da mamaki, sun wanku tas, saidai anya Umminsa ce za ta yi? Ya kasa gaskatawa har ya gama wanka ya shirya cikin doguwar jallabiya fara ya nufo cikin gidan. 
    Hajiya na sashen mijinta, Ikram kuwa wacce ta dawo kenan, tana dakinta tana aikin makaranta. Wannan ya ba shi damar shigewa dakin Ummin. Sallamarsa ce ta sanya ta mikewa zaune da sauri gami da tura littafin kasan filo ta riko wayarta kamar ita take dannawa, ya dubeta sannan ya dubi hannunnata, ta yi kasa da kanta.
'Ya Allah, Ka bani ikon dauriya ga dukkan abinda Yaya Faruk zai zo min da shi.' Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuwa dan zamowa ta yi gami da mishi barka da zuwa, ya amsa sannan ya zauna gefenta, hannu yasa ya kar6i wayarta, ya gama bincikensa har open apps ya duba saidai ba abinda ta bude, ya ajiye wayar saman kafafunta yana dubanta fuskarsa cike da damuwa.
  "Ki yi hakuri Ummina."
Ta dubeshi ido waje.
"Hakurin me?"
Ya lumshe ido ya bude.
"Na 6ata miki rai kwana biyunnan, na yi miki laifi, ki gafarceni."
Ta girgiza kai da sauri.
"Wallahi ni ce mai laifi Yaya Faruk, don Allah ka yi hakuri, in sha Allah na daina yi maki abinda ba ka so..."
Ta karashe a dan kunyace, ya yi murmushi wanda ya jima baiyi gareta ba gami da riko hannunta ya dan murza.
  "Is ok, share wannan, ni yanzu dai ki gayamin, daman an iya wankin undies aka bar Faruk nata wahala?"
Ya fada a shagwa6ance, ji ta yi kamar ta nutse a wajen, ai fa kunyarnan sai a sannu zai saketa gaba daya. Ta hau sussunne kai tana murmushi, ya yi dariya yasa hannu ya karkato fuskarta gareshi, ganin haka ta lumshe idanunta batason su hada ido. Ya yi mata k'uru da nasa idanuwan. Can kuma ya numfasa ya sanyata jikinsa ya matse.
  "Ummina idan addua ki ke min ki rage yinta, don idan Faruk ne kin gama mamaye zuciyarsa, please ki ragwanta kinji? Ina jin kamar zuciyata zata fashe da sonki."
Ta bude idanunta tana numfarfashi, tausayinsa ta ji, ta yi amannar cewa son da Faruk ke yi mata bai kai wanda ta ke mishi ba, kuma ba hakan na nufin ita din bata son nashi bane. Tana ji bata iya hanawa ba, tana gani bata iya ta kwa6a ba, haka sakonnin suka yita shigarta, duk inda ya biyo bata ko tureshi, har abin ya kai ga fin karfin tunaninsu, sai kuma don kansa ya kyaleta yana dubanta. 
  "Za ki tayani kwana yau? Tsoro nake ji." 
Batasan sadda ta dan harareshi ba sannan ta kauda kai gami da dan turo baki, ji ta ke kamar ta nutse saidai batason 6ata ranshi, batason ya k'ara nisantarta. A kwana biyun nan ta wahala da shariyar da ya ke mata. 
   Ya hau gyara mata sutura yana fadin.
"Kinji? Please."
Shiru ta yi, kamar ta ture hannunshi don tasan ba a iya gyaran zai tsaya ba,  ai kuwa ta ji ya sumbaci hannunta.
"Lallen nan naki ya burgeni Ummina, ki dunga yimin please."
Ta gyada kai kawai, sallamar Hajiya yasa ta ja baya da sauri gami da rufe kanta, shi kuwa baya ya ja kadan ya gyara zamansa sannan ya amsa. Hajiya jin muryarsa ta yi mamaki, hakan yasa ta fasa shigowa don kuwa wani hadin ne ta kawowa Ummin na mayuka masu gyara jiki don ance in kana da kyau ka k'ara da wanka. 
   Ganin ta maida kofar ta rufe bata ko shigo ba yasa Faruk duban Ummi yana murmushi mai bayyana hakora.
"Kinji Hajiyata fa?"
A rude ta ke kallonsa. Ta karya wuya.
"Don Allah Yaya Faruk ka tafi kada ta dauka wani..."
Sai kuma ta yi shiru don gudun 6ata ransa, ya dan ja jelar gashinta da ya lek'o.
"Kada ta dauka me? To naji zan fita, amma kirani da wani suna banason wannan."
"To Sadauki." Ta fada da sauri.
Ya yi 'yar dariya.
"Aa, wannan Hajiyata kadai ke fada."
Ta marairaice fuska can kuma ta ce.
"Yalla6ai."
Ya ta6e baki ya girgiza kai.
"Chanja."
Kamar zata yi kuka ta yi shiru can kuma ta dubeshi, ko ajikinsa asalima dariya ya ke mata.
  "Um..um...toh Yaya Umar."
Dariya kawai ya yi ya mike gami da sumbatar le66anta sannan ya ce cikin rada.
"Ina sonki kamar na mutu." Daga haka ya juya ya fita, ta bishi da kallo tana murmushi har ya fice. 
   Daga ranar masoyan suka shirya....!!!
         [truncated by WhatsApp]
Chapter 90 · 0% Book details